BABI NA GOMA SHA HUƊU

110 5 0
                                    

Page__14.

*FATHIYYA*

Na
*BILLY S FARI*
Da
*UMM ASGHAR*

Sai da ta kira meeting ɗin gaggawa da Executive board na company suka tattauna muhimman abubuwa da zasu kawo cigaba ga harkar kasuwancin su wanda Mahmoud yaƙi halarta duk da ya samu sanarwar meeting ɗin daga bakin sakatariyar shi amma yayi burus da ita yaƙi zuwa saboda takaicin Zinnira dake nuƙurƙusar zuciyarshi har wannan lokacin, ganin da yayi ba yada wasu ayyuka ma sai ya tashi ya bar office ɗin ya koma gida.

Sai ƙarfe biyar da rabi na yamma ta gama da office ɗin ta ɗauki handbag ɗinta da makullan mota ta fice a gajiye, sai da taje wajen motar ma tayi dana sanin rashin tahowa da drivern ta gashi yanzu duk uban gajiyar nan da take ji dole ta tuƙa kanta ta koma gida.

Haka nan taja motar zuwa gida a kasalance, wanda tsaf  kana ganin yanda take riƙon stearing wheel ɗin zaka iya rantsewa kace ƴar koyo ce saboda tsananin gajiya, don in dai don jiki da sanin ciwon jikine to Zinnira zata ɗauki lamba ta ɗaya, don kuwa ba ita ta ƙarasa gidan ba sai daf da magriba saboda yadda take tuƙin kamar bata so, abunka da babban gari kuma marece yayi akwai yawaitar motoci don ma'aikata duk sun tashi daga office suna kan hanyar komawa gida.

Koda ta shiga gidan babu kowa a parlourn ƙasan ko 'yan aikin dake kai da kawo babu duk sun gama abun6da suke yi sun koma wajajen da aka tanadar musu na zama, sama ta haye tana mamakin rashin ganin Mahmoud a ƙasan don sau tari idan har yana gidan to zaka same shi a ƙasa ne bai cika zama a sama ba sai da dalili.

Tura ƙofa tayi ta shiga ɗakin baccin nasu ba tare da tayi sallama ba don bata ɗauki hakan dole ba, kuma a wayewar ta yin hakan ƙauyanci ne da kuma takurawa rayuwa, kwance ta isko shi saman makeken royal bed ɗin su ƙirar ƙasar Turkiyya ya kife Laptop computer ɗinshi a saman gadon ya sata a gaba yana wani ɗan aiki da bai samu ƙarasawa ba sai daya zo gida ya tuno dashi shine ya ɗauko yake ƙarasawa, yana jin shigowarta yayi banza da ita, dama ba tayi sallama ba balle taci albarkacinta ya amsa mata.

Ajiye jakarta tayi akan gado ta zare ɗan yalolon mayafin data rufe kanta da shi ta ajiye, ɗan kallon shi tayi a kaikaice ta gefen ido ta taɓe baki kafin tace "sannu da gida, yau ka rigani dawowa".

Nan ma banza yayi da ita yaci gaba da aikinshi don ya ɗau alwashin sai ya ganar da ita kuskurenta matuƙar bata cire Implant ɗin ba, duk da taji haushin share tan da yayi hakan bai sa ta haƙura ba, musamman idan ta tuno da maganganun Mommyn tata, sai taji ta samu courage ɗin da zata shanye duk wani wulaƙancin da zaiyi mata don su cimma burinsu, kan gadon ta hawo tare da haye bayanshi daga kwancen da yake kasancewar rub da ciki yayi tace "ka kuwa ci abinci?.

"Banda case da hakan".

"Haba Mahmoud! don me zaka ce haka?" Oya taso muje kaci". mamaki ne ya kama shi cikin ran shi jin kalaman dake fitowa daga bakinta na kulawa, anya Nira ɗin sa ce kuwa? Ya tambayi kanshi tare da mirginowa yana kallonta, wanda hakan ya sata faɗa wa zaune a gefenshi, itama kallon nashi take yi.

"Meye kake kallona, abinci fa nace ka tashi muje kaci" bai tankata ba kuma bai ɗauke idanuwan nasa akanta ba hakan yasa tasa hannu ta rufe laptop ɗin tare da ɓata rai ta ce "Haba Mahmoud da kai fa nake magana, wai duk meye na wannan fushin, Implant ce kace na cire kuma naje na cire, to meye kuma yayi saura? Ko sai na gwada maka inda aka tsaga hannun aka cirota tukuna zaka yarda?" Ta ƙare tana ƙoƙarin zame hannun rigarta.

"No ba sai kinyi hakan ba". Ya faɗa tare da tashi zaune ya janyo laptop ɗinshi zai sauka kan gadon, rungumeshi tayi ta baya ta kwantar da kanta saman bayanshu haɗe da runtse idanunta saboda ji take yi tamkar ta rungumi garwashi, cikin dauriyar aron waɗannan ɗabi'u daba nata ba tace

"Pls am sorry Mahmoud, wallahi na cire don ALLAH kayi haƙuri tunda ka faɗi abinda kake so  kuma nayi to dogon fushin na menene, um?" Ta ƙarashe maganar kamar zata yi kuka, runtse idonshi yayi tare da juyo da fuskarshi yana kallonta, da idanuwa ta sake tabbatar masa da tabbas ta cire Implant ɗin, bai san lokacin da ya sakar mata wani irin murmushi ba tare da janyota ya rungume, kwarai ta saka shi cikin farin ciki don bai tsammaci zata cire Implant ɗin haka da wurwuri ba sanin halinta na kafiya da tsayawa akan ra'ayin ta,.

FATHIYYAWhere stories live. Discover now