Page__12.
*FATHIYYA*
Na
*BILLY S FARI*
Da
*UMM ASGHAR*Ga Fathiyya kuwa tun yamma data dawo daga office take zuba idon ganin dawowar Farouq duk daya fita cikin fushi, cikin ƙarfafa kanta da zuciyarta ta shirya mishi duk wani abu da tasan yana so kuma yana buƙata da zai sanya shi farin ciki ba tare data damu da gajiyar data kwaso a Office ba, tana gamawa ta sha wankanta cikin kaya marasa nauyi ta feshe jikinta da turarukka masu sanyi da daɗin ƙamshi, ganin har anyi sallar magrib bai dawo ba yasa bata sauko ba sai da tayi Sallah tayi azkar tare da karatun Alqur'ani lokacin anyi sallah Isha ta tsaya tayi sannan ta sauko ƙasa, kallo ta kunna tana yi amma rabin hankalinta duka yana a wajen harabar gidan, bini-bini ta ɗaga curtain ɗin tagar ko zata hango shigowar motar shi amma tsit, duk data saba da irin wannan halin da yake yi mata idan suna faɗa baya dawowa gida da wuri bai taɓa kai wannan lokacin ba, wannan dalilin ne yasa ta danne duk abinda take ji a ranta ta janyo wayarta ta shiga kiranshi har kusan sau uku bai ɗaga ba, hankalinta ne ya soma tashi ta sake kiran na shi a karo na huɗu, a lokacin ne taga yayi rejecting call ɗin nata wanda hakan ne ya tabbatar mata da yana lafiya, wayar tabi da kallo tana hasaso abubuwa da dama a cikin zuciyarta wanda nan take taji hawaye sun cika mata idanuwa don ta tabbata dole ne ɗaya daga cikin zatonta ya zamo gaskiya.
Ganin har goma tayi sha ɗaya na neman rufewa bai dawo ba yasa ta kasa jurewa saƙe-saƙen da zuciyarta keyi mata ta fashe da kuka, ta jima tana kukan kafin ta kashe kayan kallon ta fara ƙoƙarin hayewa sama, ba taji tsayawar motar shi ba har zuwa lokacin daya kasheta, shigowar shi kaɗai taji a hankali ta juyo tana kallon shi maƙale da waya a kunnen shi yana dariya, suna haɗa idanuwa da ita ya ɗaure fuska ganin irin kallon da take yi mishi tare da ƙoƙarin raɓawa ta gefenta zai wuce.
"Sannu da dawowa". Ta faɗa tana danne wani abu dake taso mata a zuciya haɗe da miƙa hannu zata karɓi ledar dake hannunshi.
Da ƙarfi ya janye ledar yana watsa mata wani mugun kallo mai cike da gargaɗi akan sake shiga sabgar shi sannan ya haye sama abun shi, jin ƙafafuwanta sun mata wani irin nauyi tayi ta bishi da kallo har ya karasa hayewa ta sauke ajiyar zuciya a hankali haɗe da furta "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allahu Allahu rabbi laa ushrik bihi shai'an" cikin ranta, tafi mintuna biyar a tsaye kafin tabi bayanshi, jin alamun yana bathroom data tura ƙofar yasa itama ta wuce ɗakinta ta sauya kayan jikinta izuwa na bacci sannan ta koma ɗakin shi, fitowar shi kenan ɗauke da towel a ƙugu da wani ƙarami a hannu yana goge sumar kan shi, ɗago kai yayi ya kalleta ya cigaba da abinda yake yi, a hankali ta tako ta miƙa hannu zata karɓi towel ɗin hannun nashi don ta taimaka mishi da goge jikin taga ya ajiye towel ɗin a bakin gado.
"Sweetheart" Ta faɗa cikin sanyin murya tare da karyewar zuciya, bai tankata ba ya cigaba da shirin shi, ba tare da gajiyawa ba ta sake cewa "Abinci fa..?" Bata ƙarasa rufe baki ba taga ya janyo ledar da Sameera ta haɗo mishi snacks a ciki ya buɗe ya zauna a bakin gado ya soma ci.
"Amma sweetheart...".
"Get out of my room.". Ya faɗa cikin ɓacin rai tun kafin ta ƙarasa faɗar abinda zata faɗa, da gudu ta fice daga ɗakin tare da fashewa da kukan baƙin ciki ganin irin zallar wulaƙancin da mijinta da take bugun gaban shine asusun sirrin farin cikinta yake yi mata don dai kawai zai ƙara aure.
Shi kuwa da wani mugun kallo ya rakata yana hurar hanta kafin ya maida hankalinsa ga snacks ɗinsa da yake ci yana wani lumshe idanuwa tamkar bai saba cin irinsa ba, yana jin tashin sautin ƙarar kukan nata amma yayi biris ko a jikinsa tamkar ba Fathiyyarsa da yake nunawa tsananin so da ƙauna ba, wanda da za ace masa zai aikata mata haka a lokacin daya musanta zancen ko kuma yace sai dai idan asiri aka yi masa zai iya yi mata hakan, sai gashi cikin hankalinsa da tunaninsa da kansa yana shuka mata tsiyataku da wulaƙanci kala kala.
KAMU SEDANG MEMBACA
FATHIYYA
RomansaFathiyya! Labari akan wasu abokai kuma aminai guda biyu wato FAROUQ da MAHMOUD, inda ƙaddara tayi wa rayuwarsu ƙullin goro akan mace ɗaya mai suna FATHIYYA. FAROUQ shine masoyinta kuma mijinta da take jin cewa mutuwa ce kaɗai zata iya rabasu, kwats...