Page__11.
*FATHIYYA*
Na
*BILLY S FARI*
Da
*UMM ASGHAR*Shi kuwa Mahmoud kai tsaye gida ya nufa a ran shi yana jin da Zinnira tayi halin mahaifiyarta da tabbas yaji daɗin zama da ita kuma bai fuskanci tarin matsaloli da ita haka ba, saboda ba wani munanan halayenta ya sani ba don ko sau ɗaya bata taɓa nuna mishi irin tsana da haushinsa da take ji ba, idan ma tayi mishi wani abun na ɓacin rai to ya kan kalle shi ne a matsayin ajizanci na ɗan adam ba wai don bata son shiba, Daddy kuma bai bata damar da zata dinga nuna halinta kai tsaye ba tunda bata ga fuska ba, mutum ne da baya ɗaukar raini kuma baya son wasa a lamurransa shi yasa bata iya fidda ƙiyayyarta fili akan Mahmoud ba sai dai ta ƙarƙashin ƙasa.
Da irin wannan tunanin ya isa gida, wani ɓaci rai ne ya ji ya ziyarci zuciyar shi lokacin daya tunkari ƙofar gidan tunawa da yadda suka yi da Zinnira kafin ya fita, hakan yasa shi jin ko ganin ta baya son yi don ya gama gano babu wani girman shi da take gani ko kuma girmama al'amuran shi, yana son su zauna lafiya cikin aminci da ƙaunar juna, soyayya kulawa da kuma tarairaya kamar dai farkon auren su amma hakan ta faskara.
Koda yayi parking motar shi a ma'adanar adana motoci ta gidan ya ɗebi kusan mintuna da yawa bai iya ya fito daga cikin motar ba don yasan babu wani abu na farin ciki da zai iske ko ya shiga, redion motar ya kunna karatun ƙur'ani a ciki na ƙira'ar Manshawi da yake yi tare da wani ɗan yaro yana maimaita mishi, baya yayi ya kwantar da kan shi a jikin kujerar da yake zaune tare da rufe idanuwan shi shima yana bin karatun nasu a hankali, sai daya ji ya samu nutsuwa sosai sannan ya kashe ya fito cikin motar ya rufe ya nufi cikin gidan yana karanta addu'o'in shiga gida.
A main parlour dake ƙasan gidan ya iske Zinnira zaune tayi kwalliya cikin ƙananun kaya bum short da crop top tana kallonta hankali kwance ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya irin ba abinda ya dameta ɗin nan.
Kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai haɗe da gimtse fuska ya haye saman abun shi ba tare daya ce da ita uffan ba, da wani irin kallo ta bishi tana taɓe baki kamar wacce taga wani abun ƙyama, sai da ya ƙule wa ganinta sannan ta maida dubanta ga kallon program ɗin da ake yi a akwatin talabijin wanda dama shi take kallo kafin shigowar shi.
Direct ɗakin baccin su ya nufa, kallon shimfiɗar gadon yayi da yau ko arziƙin gyara bata samu ba, dama Zinnira bata ɗauki wannan a cikin aikinta ba tunda akwai masu yi, da kuma suka zo yi lokacin tana waya tayi masu nuni da su tafi su barshi, a mai makon data ƙare wayar ta gyara sai bata yi hakan ba ta shiga wasu sabgogin nata da take ganin sunfi muhimmanci a wajenta, wata irin kasalalliyar ajiyar zuciya ya sauke yana girgiza kai, kayan jikin shi ya rage sannan ya shiga fara tattare kayayyakin dake barbaje har akan gado wankakku data watse ya watsa cikin laundry basket sannan ya karkaɗe gadon ya gyara don shi mutum ne mai tsafta sosai, sai daya ga ɗakin yayi mishi tsab yadda yake so sannan ya shiga bathroom yayi wanka, kasancewar shirin kwanciya bacci yake yi yasa ya shirya cikin cream colored silk pyjamas ya feshe jikin shi da turaren Versace (Eros) kafin ya haye gadon ya zauna tare da jingina bayan shi da allon gadon ya harɗe kafafun shi ɗaya kan ɗaya, wayar shi ya janyo yana duba messages ɗin shi na whatsapp da duk yau bai samu ya duba ba, a lokacin Zinnira ta turo ƙofa ta shigo don an gama program ɗin da take kalla.
Sau ɗaya ya ɗago kai ya kalleta ya mayar ga wayar shi yana jin tamkar ya tashi ya bar mata ɗakin, itan ma duba ɗaya tayi mishi ta wuce zuwa bathroom, amma ba zai iya ba saboda baya son ɗabi'ar ko ɗaya kar yazo ya fara tayi mishi yaji babu daɗi, har tafito ta gyara cikin kayan baccinta bai koma kallon koda gefen da take ba, da gangan ta tashi ta kashe fitilar ɗakin don ya tankata ko ta samu ta sauke mishi kwandon masifar dake cinta don bai jima da shigowa ba tayi waya da mahaifiyarta take ce mata ya je gidan, a tsammaninta ƙararta ya kai don tace taje ta cire implant ɗin da ta saka saboda wani hasashe da tayi, saɓanin ɗazu da kai tsaye ce mata tayi kada ta kuskura ta cire tunda ba zama zata yi dashi ba, idan kuwa tayi tazo ta samu ciki ta haihu tofa zai iya zame musu cikas ɗin dako tana so ta bar gidan hakan zai masu wahala, sai gashi kuma ta kira tana sake bata umurnin taje ta cire Implant ɗin, hakan ya matuƙar ɓata mata rai sosai don bata buƙatar haihuwa ne ita kwatakwata a wannan lokacin, to don me zai sa a tursasata yin abinda bata da ra'ayin yi.
YOU ARE READING
FATHIYYA
RomanceFathiyya! Labari akan wasu abokai kuma aminai guda biyu wato FAROUQ da MAHMOUD, inda ƙaddara tayi wa rayuwarsu ƙullin goro akan mace ɗaya mai suna FATHIYYA. FAROUQ shine masoyinta kuma mijinta da take jin cewa mutuwa ce kaɗai zata iya rabasu, kwats...