BABI NA HUƊU

78 8 0
                                    

Page__4.

*FATHIYYA*

Na
*BILLY S FARI*
Da
*UMM ASGHAR*

________________________________
Shiru Mahmoud ya yi mata tamkar bai ji me take faɗa ba yana cigaba da dannar system ɗin dake gabanshi, cikin ɓacin rai Zinnira ta daki Table ɗin haɗe da cewa "da kai nake fa Mahmoud zaka wani yi banza dani, i can't tolerate this anymore, har sau nawa na kira ka a waya amma kaƙi ka ɗaga, meye hujjarka na yin hakan ko ka manta cewa halartarka wajen meeting ɗin nada muhimmancii?"

A hankali ya ɗago kyawawan idanuwanshi haɗe da zuba mata su yana kallonta jin abinda take faɗa, tsuke fuska ta sake yi tare da tsareshi da idanuwa tana jira ya amsa mata tambayar data jefo mishi duk kuwa da kaifin idanun shi ya rage ƙarfin tsiwar data zo mishi da ita sai dai ta yi matuƙar ƙoƙarin saita kanta bata bari hakan ya nuna ba ko a fuskarta kuwa, murmushi ya saki cike da takaici yana jingina a jikin kujerar da yake zaune tare da riƙe haɓar bakinshi yana kallonta cikin idanuwa shima, dama tasan zuwan nashi zai yi amfani amma shine ta kasa tsayawa ta bashi cikakkiyar kulawar da zai samu natsuwar isa wajen? Lallai Nira tama gama raina mishi wayo, ya faɗi hakan cikin zuciyarshi yana ɗan jujjuya kujerar da yake zaune akai a hankali har lokacin bai tankata ba.

Hakan ya sake ƙufular da ita tare da ɓata mata rai ta ja iska ta bakinta ta furzar tana juyar da kanta gefe, sun fi mintuna uku a haka kafin ta juyo haɗe da sake kallonshi tace "Very good Mahmoud, na fahimci ko me kake nufi yanzu, sanin da kayi cewa ba kada matsala acikin faɗuwar M&N GROUP OF COMPANIES shiyasa ka janyo mana asarar rasa wannan kwangilar ta miliyoyin kuɗi ko, to shikenan, sai ka tanadi amsoshin da zaka bawa Abba idan ya buƙaci ganinka".

Tana gama faɗar hakan ta ja handbag ɗinta ta nufi ƙofar ficewa daga office ɗin ranta a ɓace, har ta riƙe handle ɗin ƙofar zata buɗe ta fita ƙarar yatsun hannayenshi guda biyu daya murza ta dakatar da ita, runtse idanuwa tayi kafin ta juyo tana shirin jin abinda zai faɗa.

"Nira kenan! Wai a tunaninki zan rasa abinda zan faɗawa Abba ne idan ya kirani ko kuma zan ji zafin maganar da kika faɗa mini ne? Hmm! Ko ɗaya ban damu ba Nira saboda nasan gaskiya kika faɗa, sai dai ina so ki sani, ni nake da tarin hujjojin faɗa a gaban Abba akan rashin halartata wannan taron, saboda haka go ahead and tell him, kije ki kai ƙarar tawa wajenshi, na rantse miki da ALLAH babu abunda zan ɓoye mishi akan waɗannan mugayen halayen naki da kika ƙirƙiro mini". Ya ƙare maganar yana mai nuna ta da yatsa ranshi a matuƙar ɓace shima.

"Haka kace?"

"Eh haka ɗin nace".

"Shikenan mu zuba mu gani ni dakai". Ta buɗe ƙofar a hasale ta fice tana rufo mishi ita da ƙarfi har sai daya runtse idanuwan shi saboda yadda tayi ƙara.

Dafe kanshi yayi da dukkanin hannayenshi yana jin gaba ɗaya duniyar ta yi mishi ƙunci, ya zama dole ya fara tunanin samawa kanshi mafita kafin Nira ta saka mishi ciwon zuciya da tarin waɗannan matsalolin nata, sai dai ta ina zai fara shine bai sani ba.

A ɓangaren Zinnira kuwa tana fita ta ciro wayarta ta kira mahaifiyarta Hajiya Maryam, tana ɗagawa ta ce "Mom we lost the contract, mun rasa wannan kwangilar gaba ɗaya saboda Mahmoud bai tafi wajen taron ba".

"Tirƙashi! Amma wannan yaro ɗan baƙin ciki ne, to yanzu ya kenan?"

"Zuwa gobe zan dawo na karɓi waɗannan takardun dana kawo miki, dama target ɗina idan muka samu wannan kwangilar zamu yi replacing ɗinsu da kuɗaɗen da aka samu a zuwan sayarwa aka yi, gashi ya lalata mana komai don sun ƙi amincewa su saka hannu saboda basu gan shi ba, kuma ya yi hakan ne saboda naƙi na bashi haɗin kai".

Ta ƙare zancen tana buɗe motarta ta shiga jikinta a sanyaye, tsaki Momy ta yi haɗe da cewa "ai kinji matsalarki Zinnira, don me zaki hana shi kanki bayan kinsan da wannan maganar ajiye? Ai ko kwana zai yi yana yi ya kamata ace kin daure don mu samu mu cimma burin mu, ai yanzu na fahimci cewa ba Mahmoud ne ya janyo mana asara ba, kece da kanki kika janyo mana ita".

FATHIYYATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang