Page__9.
*FATHIYYA*
Na
*BILLY S FARI*
Da
*UMM ASGHAR*A ɓangaren Mahmoud kuwa gaba ɗaya yau ya hanawa Zinnira zama sakat, duk yadda bata so haka ta haƙura a wunin ranar suna naniƙe da juna don dama shi hakanne muradin shi, tun tana ƙoƙarin ganin bata bari fuskarta ta bayyanar da abinda take ɓoyewa cikin zuciyarta ba har ta gaza ta nuna mishi halin takurar da yake sakata, shi kuma ganin yau ya samu dama irin wacce ta daɗe bata bashi ba yasa ya kasa haƙurin sarara mata, a rayuwa babu mutumin da Mahmoud yake so da ƙauna sama da Zinnira ita kuma ta kasa ganin wannan ɗumbin soyayyar, shagwaɓe mata fuska yayi yana jero mata kalaman daya tabbata zasu bayyanar mata da tsantsar yanayin da yake tsintar kan shi a ciki idan yana tare da ita amma sai ta kauda kanta gefe tana ji tamkar ta saka kuka, ita fa har ga ALLAH waɗannan abubuwan da yake yi mata tana kallon su a matsayin takurawa, a yadda take ganin tsarinta da kuma zubinta akwai naƙasu sosai ace kamar Mahmoud wanda yake nema a ƙarƙashin mahaifinta shi ne mijinta, mutumin da baya da wani gata na uwa ko uba bare dangi in ba nata ba, taya za'a yi ma har tayi kuskuren son shi ko kuma ta ƙaunace shi, sam bai dace da ita ba kuma bai cancanci amsa sunan abokin rayuwarta ba, shi yasa duk waɗannan abubuwan da yake yi don ya burgeta bata gani, asalima haushin shi take ji don gani take koma me zai zama ko zai samu a rayuwa nan gaba duka a dukiyar ubanta ne tunda da bazar su yake taka rawa balle ya iya zamowa mijin shiga tsara ko nunawa a wajen mutane.
Ɗan tsaki ta ja tana juyar da kai gefe jin abubuwan da ya keyi mata tare da rufe idanuwa tamkar mai bacci don ba jin daɗin kalaman nasshu take yi ba, ƙoƙarin tashi tayi daga kwancen da take tayi matashi da cinyar shi anan falo da suke zaune suna kallo ya yi saurin dakatar da ita tare da sakin murmushi yana yi mata tafiyar tsutsa a cikin gashinta yace "ina kuma zaki je, ki tsaya a hakan ina jin daɗi sosai kin ji ko?"
Dole ta sake gyara kwantar da kan nata a saman cinyar shi tana lumshe idanuwanta, ji take yi tamkar ta fashe da kuka shi kuma hakan sai ya bashi damar yin gyaran murya haɗe da cewa "Nira ya kamata ki fahimci irin muhimmancin da kike dashi a cikin rayuwata kuma ki ƙara mini matsayi a cikin zuciyarki da zai saka ni jin cewa tabbas ni ɗin mijinki ne ke kuma mallakina ce ta hanyar karɓar girkin gidan nan koda na yau kaɗai ne, ni dai ina so ki riƙa dafa mini abinci da kanki musamman a ranakun da muke gida, kinga sai na riƙa tayaki tunda babu inda zamu je, ina so na riƙa cin girkin matata data sarrafa mini da hannunta domin na tabbata zaifi gamsar dani tare da bani nutsuwa fiye da wannan da kike sa masu aiki na girka mun".
A hankali ta buɗe idanuwanta haɗe da zubasu akan kyakkyawar fuskar shi kafin ta ɗan taɓe baki tana maida kallonta ƙasa ganin yadda shima ya kafeta da idanuwa, cikin muryar dake nuni da ranta ya ɗan ɓaci da zancen nashi tace "kada ka soma janyo abinda zai haɗa mu faɗa Mahmoud bana so, bazan iya ba gaskiya saboda gajiyar da nake fama da ita a jiki, ga taka ga kuma ta office, duk ya kake so nayi dasu? Ko har ka manta da baƙar wahalar daka tara mini tsakanin jiya da yau da har zaka ce naje na wani ɗora maka girki, gaskiya bazan iya ba, don haka ma kadena wannan zancen tunda dai idan sun yi abincin nan zaka iya ci, nima ai shi ɗin nake ci kuma ban ji wata matsala a tattare dashi ba ko ka manta hakan?"
"Amma Nira..."
"Ya isa haka Mahmoud, wai kai me yasa baka ƙaunar kaga ina hutawa fisabilillahi?" Ta ƙare maganar tana sakin ɗan tsaki haɗe da kauda kai gefe, cikin ranta kuwa faɗa take yi ba don tana da buƙata a wurin shi ba data rantse ba zata zauna yana wani naniƙarta haka a jikin shi ba balle har yaga damar da zata sa yace wai tayi mishi girki, wannan ai mafarkine don bazai taɓa faruwa ba'.
Kanta ta soma janyewa daga saman cinyar shi cike da ɓacin rai tana neman barin wajen da sauri ya riƙo hannunta yana faɗin "Please Nira yi haƙuri, meye na ɓacin rai kuma a cikin wannan maganar? Me yayi zafi a cikin cewa da zaki ɗora girkin da kanki.."
STAI LEGGENDO
FATHIYYA
Storie d'amoreFathiyya! Labari akan wasu abokai kuma aminai guda biyu wato FAROUQ da MAHMOUD, inda ƙaddara tayi wa rayuwarsu ƙullin goro akan mace ɗaya mai suna FATHIYYA. FAROUQ shine masoyinta kuma mijinta da take jin cewa mutuwa ce kaɗai zata iya rabasu, kwats...