chapter one

963 20 0
                                    

*GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)

Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

                                 ***

                               *2014*

*SOMEWHERE AROUND MADAGALI, ADAMAWA STATE*

Sati biyu kenan da Sojojin da ke ƙarƙashin ikon Colonel Naseer Muhammad Zaki suka kai hari wa sansanin 'yan bindigan Boko Haram.
An ɓadda wuta sosai a karon battar da aka yi, dan kuwa dukkan ɓangarorin biyu sun jigata sosai, daga ƙarshe dai Sojoji suka samu nasaran koran 'yan bindigan.

Sai dai fa tsugunne bata ƙare ba dan yadda 'yan bindigan suka gudu zuwa cikin duhun daji Sojojin na buƙatar a basu umurnin shiga cikin dajin dan su samu damar gamawa da 'yan bindigan gaba ɗaya.
Sai dai jiran wannan umurni da kuma ƙarin makamai da suke buƙata ya sa har yanzu ba su tsunduma cikin dajin ba. Amma a koda yaushe Colonel Zaki ƙoƙari ya ke wajen ganin ya horas da Sojojin da ke ƙarƙashinsa da shirin kota kwana.

"Colonel" wani Soja mai muƙamin Sergeant ya ɗaga hannu ya sarawa Colonel Zaki da ke tsaye yana duba wasu takardu cikin matsakaicin tantinsa.

"Sergeant Umar, ba ka yi bacci ba?" Colonel ya faɗa dan kuwa ya gane Sojan.   Sati biyu da suka wuce da suka yi musayar wuta da 'yan bindiga aka kashe wani abokin Sergeant Umar ɗin wanda ya sa shi yin ƙaramar hauka a sansanin nasu. Da ƙyar aka samu Colonel ya lallaɓa shi har ya dawo dai-dai.
A lokacin ne Colonel Zaki ya ke ce masa idan sun samu fita daga wannan waje lafiya dole ne Sergeant Umar ya je rehabilitation saboda lafiyar ƙwaƙwalwarsa.
Colonel Zaki ba zai taɓa mantawa da abokinsa da ya haukace tuɓuran bayan sun dawo daga wani aiki da aka tura su ba.

"Colonel, ina jin tsoro" Sergeant ɗin ya katse masa tunani.  "Ban yi aure ba. Bani da kowa sai Innata da ƙannena, saboda su na shiga aikin Soja"

"Umar" Colonel ya kira sunansa tare da dafa kafaɗansa. Dole ne ya kwantar masa da hankali dan Sojan da ba shi da ƙwarin gwiwa ba zai iya aiwatar da abinda ake buƙata ba.
Ba a san Soja da tsoro ba. Sai dai, Soja shi ma mutum ne da zai iya shiga wani yanayi na rashin ƙwarin gwiwa. Dan haka hakkinsa ne a matsayinsa na Shugaba ya ƙarfafa masa gwiwa.

Zuwa gobe da safe aka ce za a kawo musu makaman da suka buƙata. Dan haka ba za a jima ba za su shiga cikin daji su far ma 'yan bindiga.

Colonel Zaki ya shiga ba wa Sergeant ɗin baki tareda ƙarfafa masa gwiwa da cewa da sun samu nasara a harin da za su kai za su samu damar komawa gida, wannan zai ba shi damar samun kyakykyawar budurwa ya aura. Sergeant Umar ya buge da murmushi duk da kuwa zuciyarsa ta karaya sosai da aikin na su. Idan ya koma gida ɗin kam zai zauna kusa da Innarsa ne yai aure ya tara mata jikoki, zai ajiye aikin Soja gaba ɗaya.

Basu ankara ba sai suka jiyo ihu daga waje haɗe da ƙaran tashin gurneti.

"Colonel, we're ambushed, we're  ambushed" Suka fara jiyowa daga waje. Wani Soja ya shigo tantin yana haki ya fara yiwa Colonel magana.
Yana ɗaya daga cikin masu gadin sansanin na su.

Kafin Colonel ya iya magana suka jiyo ƙaran bindigogi. Ashe ma 'yan bindigan har sun ƙaraso kusa da su.

Tuni Sergeant Umar ya saki fitsari saboda tsoro yayin da Colonel ya fita saboda a sansanin nasu shine mai bada umurni.

Wannan hari na bazata da 'yan bindigan suka kawowa sansanin Sojin da ke ƙarƙashin ikon Colonel Zaki a dai dai misalin ƙarfe biyun dare ya hargitsa sansanin na su gaba ɗaya.
Harbi da tashin gurneti kawai kake ji ta ko'ina yayinda Colonel ke ƙoƙarin bada umurni da iyaka ƙarfin muryansa. Sai dai kash! 'Yan bindigan sun riga sun cinmusu.

GENERAL NASEER  ZAKI (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now