nineteen

209 8 0
                                    

*GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)

Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat

*MMG'S*
_Chilli powder_
   Tasty Yaji... *kin kuwa san sirrin haɗa yaji da garin ɗanwake mai kyau ko kuma dai a bar maganar kar ayi tone-tone?. To! matso Hajiyata ba sai kin wahalar da kanki ba, MMG's Tasty Yaji sun zo muku da sauƙi, ba ruwanki da jan hanci ko tari wajen dakan yaji. Kawai order za ki yi a kawo miki yaji mai kyau har gida. Ga kuma garin ɗanwake mai danƙo suɓul-suɓul Malamata . Domin  gwada yajin mu da garin danwaken zaku iya tuntubar mu ta wannan lambar. 08094816690 ko ta wannan number 08157709148.*  Sayan na gari mai da kudi gida, sai an gwada akan san na kwarai, sayan daya-daya ko sari akan furashi me rahusa.

                           Page 019

***

*2014, KADUNA*

Wayoyi guda biyu ne a gabanta ga ɗaya da ta riƙe tanata dannawa.
Yanayin yadda ta nitsu tana bin hirar da ake a tashar BBC Hausa zai tabbatar maka hiran na da mahimmanci a gareta. Jiya aka sake hirar kuma daga jiyan zuwa yau a ƙalla sama da mutane dubu hamsin sun kalli hirar.
Maimaita kallon take saboda ta tabbatar babu inda ta yi kwaɓa ko kuma ta manta da mahimmin abu da bata faɗa ba.
Komai ya mata a kwalliyarta amma ta ɗan lura kamar wacce ta mata zanen gira ta yi ɗaya ya fi ɗaya girma. Bata da gashin gira sai 'yan tsilli-tsillin gashi da ba su fi a irga ba, wannan yasa in dai za ta fita koda ba zata yi kwalliya ba to dole ne ta zana giranta. Sau da dama idan ta tashi a barci ta kalli fiskarta a madubi giranta take fara dubawa. Ba kalar mayukan ƙara gashi da bata shafa a giran ba amma gashin ya ƙi tohowa, kuma kaman shafe-shafen mai da ta yi a baya ya sake soye giran nata.

Hajiya Munira Bawa kenan wacce duniya ta fi saninta da Hajiya MoBaby. Babbar Producer ce kuma Director a masana'antar Kannywood. Sannan mata a wajen Colonel Naseer Muhammad Zaki.

Duk da shekaru bakwai kenan da ta dena fitowa a fina-finai har yanzu tauraronta bai dena haskawa ba dan duk inda za a kira Producers na Kannywood guda biyar to dole a tsinci sunan kamfaninta a ciki.
MoBaby ta zamo ɗaya daga cikin iyayen Kannywood. Su ne ke juya masana'antar. Sune masu faɗa aji.
Tana da jarumai dayawa da ta shigo da su cikin masana'antar ta koya musu aiki har ta yaye su.
Bata shiga film amma tana aikin bayan fage. Tana da ɗimbin mabiya a shafukan Instagram da Facebook.
Bayan harkar film tana da business ɗinta na skincare products. Inda take da mayuka da kayan kwalliya da ta fitar duka ƙarƙashin kamfanin MoBaby Cosmetics.

A shekaru bakwai da aure Allah ya albarkaceta da 'ya'ya biyu. Babban Ibrahim Khalil yanzu shekaransa shida sai ƙaramar 'yar shekara biyu, Zainab da suke kira da Zee ko Baby saboda sunan Iya da ta ci.
Akwai yaron mijinta Al'amin da ta riƙe amma yanzu yana boarding school inda yake JSS 2.

Zahra ƙanwar Al'amin har yanzu tana hannun Iya ita kam ko a hutu bata son zuwa Kaduna dan bata shiri da Munira. Tsakaninta da Babanta sai dai idan ya zo duba su a Azare ko kuma dukka gidan sun zo hutu Azare. Tana gaban Iya tana shan gata, ba wanda ya isa ya taɓa Zahra idan ka ce zaka taɓa Zahra yanzu zaku ɓata da Iya.

Shigowar Mukhtar ya sa Munira ta kashe video'n da ta ke kallo ta fuskance shi.

"ƙaramin Soja" ta faɗa tana dariya. Duk cikin 'yan'uwan mijinta babu wanda tasu ta zo ɗaya irin Mukhtar ɗan gidan Indo. Shekarar da ta wuce ya fara karatu a NDA Kaduna. Shima ɗin sahun Kawunsa yake son bi.
Kafin ya tafi makarantar ma sai da yayi zaman watanni a gidansu bayan ya gama Sakandare. Yaron bashi da girman kai haka zai zage yayi ta mata aikace-aikace irinsu wanke mota da kuma kai ɗanta Khalil makaranta.
Yaranta ma gaba ɗaya sun saba da shi, da ya zo zaka ga suna ta ihun Uncle Mukhtar. Hatta Baby Zee tun ba a yayeta ba ta ke maƙale masa. Yanzu ma da ta ganshi zata fara Uncle babu me. Wato ya goyeta.

GENERAL NASEER  ZAKI (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now