nine

191 7 0
                                    

*GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)

Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat

                           Page 009



Hussaina ta fito daga banɗaki ɗauke da fitila jikinta na ɓari saboda jinin da ta gani ɗazu da suka dawo daga Islamiyya ya ƙi tsayawa.

"Hussaina kawo fitilan mana, zan raba miya ne"
Hauwa'u da ke tsaye a tsurkukun kitchen ɗinsu ta faɗa. Iya da Fatima sun je barka ita aka bari da abincin dare amma saboda shegen son kallo bata fara girkin ba sai bayan magariba. Wata Amarya aka kawo kusa da gidansu Anty Fauziyya tana da kayan kallo a ɗakinta.
Wani lokaci kafin ta biya wajen ɗinki idan akwai wuta sai ta shiga wajenta ta ɗan yi kallo. Yau ma wani cassette ta saka musu na India shi ya ɗauke mata ido ta manta da girkin da za ta yi. 

Hussaina ta miƙa wa Hau'wa'u fitila ta shige ɗakin Iya tana tunanin wa za ta faɗawa maganar jinin nan. Iya? ko Anty Fatima? ko kuma Hauwa'u?.

"Lafiyanki?" Hassana ta tambaya lokacin da ta shigo kiran Hussainar ta fito su ci tuwo ta sameta duƙunƙune akan gadon Iya.

"Ba komai, ki je ki ci ba yanzu zan ci nawa ba"

"Wallahi idan ba ki fito ba sai na cinye naman ki"

Hassana ta fice a ɗakin tana sa wa a ranta idan Hussaina bata fito ba duka naman cikin miyar za ta tsame ta barta da gayan tuwo. Kwana biyu suna samun nama nasha-nasha a miya. Wata Akuyar Iya ce ta kasa shine aka yanka shekaranjiya, tun daga ranan kuma suke watanda da nama a gidan.

Tana zama kuwa za ta fara cin tuwon ta tsinkayi sallamar Iya da Fatima.

"Iya sannu da dawowa"

Iya ta cire hijabinta ta fara ninkewa ta ce " ina Hussaina?"

"Na kirata ta ce wai in je in fara ci"

Fatima ta shige ɗakinta ta kunce goyonta ta saukar da Al'amin.

"Me ya sameki?" Iya ta tambaya bayan ta shigo ta ga Hussaina kwance akan gado.

"Cikina ke ciwo"

"Shine kika kwanta. Maza tashi Hassana ta raka ki kije kemis a baki magani"

Ta ɗan tashi zaune ta ce "har da jini"

Iya bata tambayeta komai ba ta fita ta ɗauko fitilan da ke gaban Hassana da ke faman tauna ƙashi ta zo ta buɗe akwatinta tana neman zani. Gida biyar ta yanka zanin ta miƙa wa Hussaina tana mata bayanin yadda za ta naɗe ƙunzugun.

Dukkansu akan tabarma ana cin abinci suka ji sallamar yaro daga zaure.

"Wai Iya Abu ta zo"

Gaba ɗaya sai suka sake baki dan abin yayi musu banbaraƙwai.

"Iya Abu ko Hauwa'u?" Hassana ta tambaya dan Hauwa'u ce ke da samari.

"Iya Abu aka ce"

Iya Abu dai bata ce komai ba. Wa zai zo nemanta da dare haka. Babu namijin da ya ke zuwa wajenta sai Basiru ƙanin mijinta wanda shima sai da dalili ya ke zuwa kuma shi babu shamaki da shigarsa gidan, sallama zai yi daga zaure idan aka amsa ya ƙariso cikin gidan.

Hauwa'u ce ta zari gyale ta fita dan ta duba waye ya ke neman Iya.

Cikin hasken farin wata ta gane shi. Malam Dogo mai nama ne.
Suka gaisa sai wani murmushi ya ke yana sosa ƙeya. Ko da ta shiga gida ta faɗawa Iya Malam Dogo ke nemanta sai abin ya sake ɗaurewa Iya kai.

"To Iya ki je ki ji me ya kawo shi mana"

"Ke!"

Hassana ta yi dariya ƙasa-ƙasa

Ko ƙarisa cin tuwon bata yi ba Iya ta ɗauraye hannu ta sa hijabi ta fita.
Mamakin zuwan mutumin da sunansa kawai ta sani bata san kamanninsa ba ta yi.

Sallama ta masa ta haɗa da tambayar ko lafiya?.

Malam Dogo ya wani lanƙwasa kai yana tambayarta ya aka ji da hidimar yara.

Daga yanda suke tsaye ko wajen zama bai samu ba Iya ta katse shi daga dogon hiran da yake shirin ɓarowa.

"Me ya kawo ka, Malam Dogo"

"Dama dai nace" yai shiru yana karantar fiskarta cikin hasken farin wata. Ɗazu da yamma yana rumfarsa ya ga wucewarsu ita da surkuwarta. Ya tambaya ake tabbatar masa matar marigayi Malam Muhammadu ce shine ya wanko ƙafa ko za a dace duk dama dai lokacin da yai auren farko tana da cikin Naseer, an yi aurensa da sati guda aka haifi yaron.
To sai me?.
Ko zata girme shi ma ai ba zai wuce da shekaru uku zuwa biyar ba. Ai Annabi ma ya auri wacce ta girme shi. Dan haka sunna zai ɗabbakar.

"Malama Zainabu" ya cigaba da maganarsa. "Kin san dai dama haka Allah yake lamarinsa, idan wani ya tafi sai wani ya maye gurbin wani. Kuma dama zaman duniya ita kanta cuɗeni-in-cuɗeka ne. Ina so ki bani dama na taya ki riƙe marayun da ke hannun ki"

Iya Abu ta fusata. Wani irin magana ne wannan. Yau shekara uku da rasuwan Malam babu wanda ya taɓa tunkaranta da maganar banza irin wannan sai yau.
Amma dai mutuwar miji tonon asiri ne.
Tsofai tsofai da ita wani aure za ta sake yi yanzu?

"Ka ga Malam Dogo..."

"Sunana Sama'ila"

"Koma dai menene sunan naka ina so in baka shawara, kada ka ƙara zuwa gidan nan da zance irin wannan..."
Tana maganar da iya ƙarfin muryarta.

"To Malama Zainabu idan ba..."

Sallamar Baffa Basiru ya katse shi.

Iya Abu ta juya ta shige ciki ko yaranta bata tsaya biyewa tambayarta da suke me ya faru ba ta shige ɗakinta ta rufo ƙofa ta samu gefen gado ta zauna ta fara hawaye.
Mutuwar Malam ne ya dawo mata sabuwa, wai yau saboda Malam na cikin ƙasa har wani namiji zai iya zuwa wai zance wajenta.

Ko da Baffa ya ce a mata magana ta fito su gaisa ƙin fitowa ta yi.

Abu kamar haɗin baki sai ga shi bayan Malam Dogo kusan mutane biyu sun sake zuwa nemanta ciki har da abokin Malam ƙut da ƙut. Dukkansu babu wanda ta bawa fiska, ta riga ta gama aure a duniya. Yo ma da manya-manyan yaranta wani aure za ta sake yi.

Lokacin da Baffa Basiru ya ga zawarawa sun fara zuwa neman Iya Abu sai shima zuciyarsa ta raya masa ai shi ya fi cancanta ya auri Abu ba wani bare ba.
Daga nan ya fara canja salonsa sai ya siyo cefane ya aiko musu, safe da dare sai ya zo duba su.
Iya Abu ta lura da take-takensa amma ta yi biris kamar bata san me yake nufi ba.
Rashin namiji a gidan ma babu daɗi. Da Nasirunta na gida babu wanda zai iya zuwa ya tunkareta da wani zancen aure.

Sai da aka ɗau wata biyu da zuwan Malam Dogo sannan Baffa Basiru shima ya fito ya faɗawa Iya Abu manufarsa. Ai kuwa ta masa tatas dan har gara ace bare ya nemeta, amma Basiru ƙanin mijinta ai wannan cin amana ne na ƙarshe.

Haka dai zawarawa suka ƙarishi zuwansu suka haƙura babu wanda Iya Abu ta amsa tayinsa.
Shi kuwa Baffa Basiru har Chinade ya je yai wa yayyenta magana amma ta ƙi bashi haɗin kai. Da ya ga fa ba zai yiwu ba sai ya janye ƙafarsa, ɗan alkhairin da ya ke yi musu ya dena.

Cikin yaranta dama babu wanda ya goyi bayan Iya ta sake aure. Hadiza ce ma ta nuna kaman tana ra'ayin Iya ta sake aure saboda kaɗaici. Ai kuwa ranan da ta yiwa Iya maganar tofin Ala-tsine ne kawai bai fito daga bakin Iya ba saboda yadda ta ƙyamaci abin. Tun daga lokacin kuma kowa yayi shiru.

Tafiyar Naseer India da shekara ɗaya da wata uku suka dawo.
Watarana Iya ta yi dambu ana tsakar gida ana ci Indo ta zo daga Kano suka ji hayaniya daga waje.
Ai tun da aka shigo aka ce Naseer ya iso gari yaran suka cire hannu a abinci suka zuga waje har da Indo ma da 'yarta a hannu.

Iya dai na zaune sai hamdala ta ke a ranta. Fatima ta tashi ta shige ɗaki tana ta murmushi.

Wannan karan har kumatu yayi kamar ma dai ba karatu ya tafi ba dan yayi haske ya ɗan yi jiki. Ƙila kuwa ƙasar da ya je ne ta karɓe shi.
Kamar yadda ya faɗa lokacin da ya shigo gidan Iya ya gani zaune akan tabarma sai kuma yaronsa da ke ta ƙoƙarin rarrafe. Ko ba a faɗa ba ya sani wannan yaron ɗansa ne. Balle kuma tun a waje Hassana da Hussaina sun gulmata masa.




GENERAL NASEER  ZAKI (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now