fourteen

185 9 0
                                    

*GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)

Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat

                           Page 014

*2007, Azare Bauchi state*

"Yanzu haka zaka cigaba da zama babu aure. Nasiru ka yiwa kanka adalci kuwa?"

Naseer ya ɗaga ido ya kalli Iya sai dai bai iya ce mata komai ba. Shekaru biyu kenan da rasuwan Fatima. Kuma ko yaushe ya samu damar zuwa gida sai Iya ta saka shi a gaba da maganar aure.

Ba wai baya son auren bane. Sai dai har yanzu ya kasa samun nitsuwar da zai tsaya ya nemi wata mace. Zaɓa masa Fatima aka yi kuma ya riƙeta da hannu bibbiyu, bai taɓa nadamar haka ba saboda Fatima mace ce ta gari. Duk da ba auren soyayya suka yi ba, a zaman aurensu akwai zaman lafiya da farin ciki.

Wannan karan yana so ya zaɓo matar da zai aura da kansa ne, sai dai har yanzu bai ga wacce ta dace da shi ba.
Iya ta masa tayin 'yanmata kusan uku yana ƙi, yayyensa mata ma ba a barsu a baya ba, kowa da wacce take biɗar ya aura.
Akwai wata cousin ɗin abokinsa Faruƙ Lawanti da ta nace masa ita ma, amma bai tunanin zai iya aurenta dan bata kwanta masa ba.

Yana buƙatar mace a tare da shi. Yana buƙatar 'ya'yansa Al'amin da Zahra su koma hannunsa da zama.
Akwai kaɗaici idan ya dawo daga office ya shiga gida ya ji wayam babu ɗuriyar mutum a cikin gidansa.
Yana da niyyar shekaran nan ba zai ƙare ba zai yi aure.
Ko ina matarsa take zai samota ba sai an nemo masa ita ba.

Kamar yadda ya saba zuwa ya yi kwana biyu a Azare wannan karan ma kwana biyun yayi ya shirya komawa bakin aikinsa a Maiduguri amma kafin nan zai halarci bikin wani abokinsu a Abuja. Tare da Lawanti za su wuce dan dukkansu a NDA Kaduna suka haɗu.
Kaduna zai fara wucewa ya haɗu da Lawanti su wuce Abuja.

"Maganar Aminatu baka ce komai ba"

Iya ta masa maganar lokacin da ya shigo ɗakinta sallama.

Sun yi magana da Aminatu. Itama tana son auren amma abun ne ya gagara, duk masu zuwa sai su dinga ja baya da tsoron wai tunda aikin Asibiti take ba zata samu daman zaman gida ba, masu aikin Asibiti basa hutu safe har dare kullum suna aiki.
Ya kan faɗa mata cewa za ta samu mijin da zai sota ya kuma aminta ɗari bisa ɗari da irin aikin da take. Kar ta ɗaga hankalinta.
Ita kuma Iya kullum ƙorafinta Aminatu ta doshi shekaru talatin babu aure.
Da ke a lissafinta na dikake gani take shekarun Aminatun da yawa tunda ba wai ta kama ainihin shekarar haihuwarta bane (date of birth).
Sai dai Naseer da ya san lissafin shekarun ya san shi kansa yanzu ne ya shiga shekara talatin ɗin, amma a lissafin Iya ganin ya kai arba'in ta ke. Ta manta cewa auren wuri yayi.

"Aure lokaci ne" ya bata amsa "Kamar yadda Allah ya baiwa sauran 'yan'uwanta mazajen aure itama Allah zai bata nata mijin. Ki dena ɗaga mata hankali, ki cigaba da yi mata addu'a kuma ki sa mata albarka a aikin da take. Wannan kawai shine iya abinda za ki iya yi mata"

Yana alfahari da ƙanwarsa Aminatu. Ita ce ta ciri tuta ta yi karatu mai tsayi bayan shi. Da ke Allah ma ya taimaketa dukkan karatun da ta yi cikin sa'a ta yi, babu wani tangarɗa ko kaɗan.
Akwai Alfanun karatun 'ya mace. Ita kanta Hadiza ma da ta yi NCE farkon shekara da ya zo gida take ce masa ta samu admission a ATBU da ke Bauchi za ta jona degree kuma mijin ya barta ta cigaba da karatunta.

"To ga nan Musan gidan Inna Ladi yana so ya aureta ta ƙi shi. Ka ga auren ne bata so"

"Amina ba za ta auri Musa ba" Naseer ya faɗa da wani izza wanda ke nuna maganarsa ta tsaya kenan.
Iya ta hangame baki. Dama so take ta lallaɓa shi ko zai yiwa Aminatu magana ta yarda da Musan kawai a sha biki ta huta da maganar mutane.
Wani lokaci idan Naseer yai magana sai ta ga kamar Malam ne ke maganar.

GENERAL NASEER  ZAKI (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now