chapter four

268 13 2
                                    

*GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)

Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat

                           Page 004


"Soja dai?"

Iya Abu ta sake kifiyar da ke hannunta da take wa Hussaina kitso.

Naseer ya tsaya daga gefe riƙe da form ɗin NDA da ya je ya siyo a Kaduna. Jiya da dare da ya dawo bai samu ya yiwa Iya bayani ba amma da Asuba ya zanta da Baba wanda shima ya nuna damuwarsa kan ra'ayinsa na son zuwa Makarantar Sojoji.

"A'a ba zai yiwu ba Nasiru, bayan ka san kai ne Babban gida"

"Iya na sha faɗa muku Soja nake son zama. Wai menene a aikin Sojan nan ne"

"Ka haƙura da maganan Sojan nan. Ga karatun Likita ko Malamin makaranta duk zaka iya yi. Ɗan gidan Gajiye ba Likita aka ce zai zama ba, yana can yana karatu a Maiduguri"

"Iya gaskiya ki yi haƙuri ra'ayina kenan"

Iya ta juyo ta masa wani kallo sannan ta cigaba da kitson da take.

Naseer yayi shiru yana bin form ɗin hannunsa da kallo.

Kallo ɗaya zaka yiwa Iya ka ga tsantsan kamanninta da Naseer, sai zanen uku-uku da ke gefen goshin Iyan wanda ya fara koɗewa saboda girma kaɗai da Naseer ɗin ba shi da shi.

Iya Abu baƙar bafulatana ce. Tana da tsawo da dogon hanci da ya ƙawata matsakaicin fiskarta. Bata da jiki sam kuma jinyar da ta yi kwanan baya ya sake bushar da ita.
Naseer babu abinda ya bari na kamannin Iya sai ɗan kaurin jiki da ya ɗauko daga wajen Malam. Saɓanin Iya shi Malam yana da tsayi kuma yana da ɗan kaurin jiki. A duk cikin 'ya'yansu Hadiza ce kawai bata da tsayi amma duk sun yi gadon tsawo daga wajen iyayensu.
Shi Malam fari ne amma ba sosai ba shi yasa yaran suka rabu biyu, wasu sun ɗauko hasken fatarsa wasu kuma sun ɗauko baƙin Iya.
Asalinsu Malam ruwa biyu ne, jinin Fulani ne da jinin Bare-Bari. Ance Kakansa daga wajajen Potiskum ya taho  Almajiranci garin Zaki, a nan yai aure ya haɗa dangantakar aure da Fulani. Daga nan kuma 'ya'ya da jikoki duk suka kasance mazauna garin Zaki.

Ita Iya ta ko ina ta haɗa jini da Fulani. Tana jin Fulatanci sosai dan ko lokacin da Malam ya aurota ba ta jin Hausa sosai amma saboda shi Malam ba ya jin Fulatanci da kuma zama cikin Hausawa sai ya zamana itama harshen nata ya juya zuwa Hausa dan idan ka ga tana Fulatanci to tana cikin 'yan'uwanta ne.

"ban amince da karatun Soja ba. Allah ya tsareka da aikin kasada"

"Haba Iya! Haba Iya!"

Iya ta sa hannu a ƙasa ta lalumi kifiya ta cigaba da tsaga kan Hussaina.

Wasa-wasa batun maganar zuwa makarantar Sojoji ta jawo rikici tsakanin Naseer da Iya. Shi ga shi ya je ya karɓo form ya cika amma Iya ta ce sam bata yarda ba. Idan kuma ya takura sai dai yayi gaban kansa.

Shima dai Baba ba wai yana ra'ayin zaɓin ɗan nasa bane musamman yadda ake jin jiki a mulkin Soja da ake ciki. Amma kuma baya so ya tursasa wa ɗan nasa. Tun yana ƙarami yake maimaita cewa shi kam Soja zai zama. Ga shi har yanzu abin na ransa.

"Zainabu" Malam ya kira sunan Iya lokacin da suka kaɗaice a ɗaki.

"Na'am Malam"

"Ba zan miki dole ki canja ra'ayinki ba. Amma maganar Nasiru ki sake dubawa"

"Malam shi kaɗai fa garemu. Aikin Soja akwai kasada a ciki. Mijin Nafisa watansu uku da aure da aka turasu yaƙi ko gawarsa ba a gani ba" idanunta suka cicciko da hawaye.

"Malam ka yi haƙuri mu haɗu mu hana shi wannan aikin"

Malam yayi shiru. Ya san abinda ta ke tsoro.

Shi kam har cikin ransa da Naseer da sauran 'yan'uwansa mata duk ɗaya suke a wajensa.
An sha yi masa maganar ƙarin aure saboda ya samu haihuwar 'ya'ya maza dayawa amma ya ƙi. Duk 'yan'uwansa maza babu mai mace ɗaya sai shi.

GENERAL NASEER  ZAKI (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now