sixteen

181 12 0
                                    

*GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)

Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat

                           Page 016

Hausawa suka ce wani hanin ga Allah Baiwa.
Tafiyar Zarah Beauty Egypt kamar gobarar Titi ne a Jos dan ko wata huɗu ba ai da tafiyar ta ba sai ga labari ya karaɗe kafafen rediyo akan cewa tsohuwar Jarumar Kannywood Zarah Haroon Barde da aka fi sani da Zarah Beauty za ta auri wani hamshaƙin maikuɗi Balaraben Egypt kuma ambassada a ƙasar Turkey.
Cikin sati biyu aka riƙa yawo da hotunan engagement ɗinsu.
Ƙarshen wata kuwa sai gashi ana hasko ɗaurin auren kai tsaye daga manyan gidajen jaridu.
Aure ne da aka kashe maƙudan kuɗi haka nan manya-manyan masu kuɗin duniya sun halarci taron bikin.

Wannan cigaban da Zarah Beauty ta samu ya haukata MoBaby ba kaɗan.
Ta so ace yarinyar ta walaƙanta, sai ga shi an ma manta da maganar shaye-shayenta. Suma 'yan industry da suka cireta sai ya zamana sun koma cizon yatsa dan kuwa a duk hidimar bikin mutum ɗaya Zarah ta gayyata daga industry wacce ta tsaya mata lokacin da ake ta hayaniyar video'n ta da aka yayaɗa.

A dai dai gaɓar kuwa Captain Zaki ya nemi Munira ta ba shi amsar tayin soyayyarsa. Kwana uku ya bata ko ta amince da shi ko kuma ta manta da shi.

MoBaby irin matan nan ne da ba sa rabuwa da saurayi gaba ɗaya, ko basa son mutum ba za su haƙura da shi gaba ɗaya ba.
Tun da ta watse da Alhajinta ta ke bibiyar Captain Zaki. Yana ranta amma sharaɗinsa shine ya mata tsauri.
Ta ajiye film gaba ɗaya, anya za ta iya kuwa?
Sai dai kuma auren gata da Zarah Beauty ta yi ya tashi kanta. Ta ji itama ɗin tana buƙatar auren a wannan gaɓar. Duk cikin samarinta ta sani babu wanda ya kai Captain Zaki nagarta.
Shine za ta aura ta zama abun kwatance.

A rana ta uku ta kira shi ta sanar da shi ta amince da buƙatarsa sai dai itama tana da sharaɗinta. Za ta ajiye shiga film amma kuma ba za ta ajiye aikinta na producer ba.
A taƙaice ya turo mata reply da "ba matsala"
Wannan taƙaitacciyar amsa ita ta ƙulla alaƙar da ta kai su ga aure.

*

" 'yar dirama za ka aura. Haba Nasiru. Haba Nasiru"
Amsar Iya kenan lokacin da Naseer ya bayyana mata matar da zai aura.

Tun lokacin da maganar ta fito kafin ma ya zo da kansa yai mata bayani su Hassana suka sakawa Iya wani film ɗin da Munira MoBaby ta yi suna nuna mata cewa ita ce wacce su Anty Aminatu suka ce Yaya Naseer zai aura.

Iya ta tsura ido tana kallon TV baki buɗe, ba a jima ba kuwa aka fara waƙa a film ɗin iya ta fara salati lokacin da aka hasko MoBaby tana tiƙar rawa tana wani yar-yar da kitson attachment da ke kanta.

"Matar da ta gama barikin za ka aura Muhammadu Nasiru. Duk matan duniya ka rasa wacce zaka aura sai 'yar dirama. Ka kyautawa 'ya'yanka kuwa?"

"Ki yi haƙuri da zaɓi na" Ya faɗa a taƙaice.

Duk yadda Iya ta nuna rashin amincewarta babu yadda ta iya. Har mutanen Zaki sai da ta kira tana neman su haɗu su hana Naseer auren da yake shiri amma bata samu goyon baya ba.
Kowa ce mata ya ke Naseer NAMIJI NE.

Shi kenan dan namiji ne sai a bar shi yayi duk abinda ya ke so.
Yayyensa da ƙannensa kaf ɗinsu babu wacce ta aibata zaɓin Naseer wannan ya sa aka bar Iya ita kaɗai da kumfar baki.
Har ɗakinta Baffa Basiru ya shigo ya ke faɗa mata suna so su je tambayar auren Munira amma saboda ta ƙi Naseer ya ce a jira tukunna.

"Zainabu, kwanaki kina ta kukan Nasiru ya ƙi aure, yanzu kuma ya kawo wacce ya ke so kin hana shi. Kina tunanin idan yaya yana nan zai bari ki hana Nasiru samun farin cikinsa ne"

Ba ta ce masa ƙala ba har ya gama maganarsa ya tafi. Ta sani ɗan abin arziƙin da yake samu a jikin Naseer ɗinne ya sa shi wannan tsayin dakan da ya ke akan maganar.

Lokacin da Naseer ɗin ya bugo bayan ya koma bakin aikinsa ce masa ta yi.
"Ba zan hanaka abinda kake so ba. Allah ya bada zaman lafiya".

Abin ya mata ɗaci. Ta fi so Naseer ya auri ta gida wacce za ta kula masa da marayun 'ya'yansa tsakani da Allah.
Amma yana shirin auro wacce duka duniya an santa, anya kuwa za ta iya riƙe 'ya'yan marigayiya?.

Lokacin da aka fara shirye-shiryen biki haka Iya ta zuba ido tana kallonsu.
Da ke ga ta da arziƙin 'ya'ya mata kuma Naseer shi kaɗai cikin mata sai ya zamana dukkansu sun haɗe kai suna ta shirye-shirye babu kama hannun yaro.
Su har wani jin daɗi suke ɗan'uwansu zai auri babbar jaruma kamar Munira MoBaby.

Lokacin da biki ya fara ƙaratowa sai abin ya fara bawa Iya tsoro. Abubuwa ne na bidi'a da kashe kuɗi ake shirin yi wanda take ganin almabazzaranci ne tsantsa. Tun tana kukan abubuwan da ake shirin yi har ta haƙura ta zuba musu ido dan babu mai sauraronta.

A Kano aka yi dukkan shagali sai guda ɗaya da aka yi a Azare.

Biki ne na Captain ɗin sojoji da kuma fitacciyar jarumar Kannywood MoBaby.
Tun daga Dinner, Luncheon, cocktail party da buɗar kai babu wanda ba a kashe maƙudan kuɗi ba.
Captain Zaki ya zuba kuɗi haka itama MoBaby ta zuba kuɗi a bikin nata. Sannan ga uwa uba 'yan Kannywood da suka mata kara.
Shima kansa Naseer ɗin abokanansa da suka yi NDA wanda waɗansun su sun zama manyan sojoji wasu kuma sun zama manyan 'yan siyasa da 'yan kasuwa duk sun shiga bikin dumu-dumu.

Tun daga farkon watan September 2008 har zuwa Ƙarshenta babu bikin da ake maganarta irin bikin *Captain Naseer Muhammad Zaki da Munira Bawa (MoBaby)*

A gidansa da ke Azare ya fara ajiyeta bayan sun sha Amarci sai ya koma bakin aikinsa a can Maiduguri.

Inda suka fara samun matsala da Iya kenan lokacin da Munira ta koma Kano saboda aikinta yayinda mijinta ya ke can Maiduguri.

A waya ta ke tambayar Naseer ko da saninsa Munira ta tafi ya ce mata shi ya bata izinin tafiya.
Bayan sun gama wayar Iya ta ajiye wayar a kan kujera ta sauke ajiyar zuciya. Abinda dai take tsoro ne yake shirin faruwa.
Fargabanta a kullum kada Nasiru ya auro wacce za ta saka shi ya juya musu baya. Gashi tun ba a je ko'ina ba alamu sun nuna hakan zai iya faruwa...

***

*Gulak, Madagali, Adamawa state*

Jikin Kaka Medugu yayi tsanani sosai gashi ya ƙi yarda a kaishi Asibiti.
Kyauta ke dafa masa saiwowin magani da ganyayyaki. Duk magungunansa ta sani dan tun tana yarinya Kaka Medugu ke koya mata ilimin saiwowi da ganye. Ko idonta a rufe idan ta shafa saiwa ta shinshina za ta iya faɗin saiwar wata bishiya ce.

"Kaka me yasa ba za ka musulunta ba" tambayar da Kyauta ke yiwa Kaka Medugu a mafiya yawan lokuta kenan.

Wani lokacin sai yayi shiru, wani lokaci kuma sai ya ce mata " na yi rayuwa mai kyau. Ban zalunci kowa ba, ban bi matan kowa ba. Wannan ya ishe ni"

"Amma Kaka ai kana shan giya"

Kaka Medugu ya ɗan yi tari sannan ya fara dariya.
Addinin Bature dana Larabawa shi ya hana shan giya. Idan namiji bai sha giya ba mi zai sha.

"Męnagkur" ya kira sunanta.

"Na'am Kaka"

Ya riƙo hannunta duka biyu ya ce "kowanni irin addini kika zaɓa ki tabbatar kin yi rayuwa mai kyau. Kada ki cuci kowa, ki taimaka wa duk wanda za ki iya, kin ji?"

"To Kaka" ta amsa tana murmushinta mai sanyi.

"Ngwatam" ta jiyo muryan Babanta daga tsakar gida. Da gudu ta miƙe ta bar ɗakin Kaka ta fita waje

"Baba gani"

John Yahaya ya karkace hularsa yace "zan je masallaci mi zan siyo idan ina dawowa"

"Manja ya ƙare"

"Sai me kuma?"

"Ummmm! Barin duba kitchen"
Ta yi maza ta shige ɗan tsurkukun ɗakin da aka yi da langa-langa inda suke dafa abinci.
Ta fito tace " babu gishiri da maggi"

"To zan siyo. Na tafi"

Ya fice daga gidan hannunsa ɗauke da carbi yana ja.

GENERAL NASEER  ZAKI (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now