Twenty

178 8 0
                                    

*GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)

Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat

                           Page 020

*2014*

*SOMEWHERE AROUND GULAK, MADAGALI, ADAMAWA STATE*



Sanyin Asubahi ne ya fargar da Colonel Naseer Zaki daga dogon suman da ya yi.
Hannunsa ya fara motsawa sannan ya buɗe idanunsa, tsilli-tsillin ciyayi da yake gani dishi-dishi shi ya tabbatar masa da cewa ba mutuwa yayi ba. Yunƙurin miƙewa yayi amma hakan ya gagare shi. Rufe idanunsa yayi a karo na biyu yana ƙoƙarin tattaro ƙarfinsa.
Bayan tsawon lokaci ya sake buɗe ido, wannan karan yunƙurawa yayi da duk iya ƙarfinsa ya motsa daga inda yake kwance ya mirgina gefe.
Jan jiki ya fara yana ƙoƙarin kaiwa gindin wata ƙatuwar bishiyar da yake hangowa ko zai samu ya dafa bishiyar ya miƙe.
Yana jan jiki yana hutawa har ya kai jikin ƙatuwar bishiyan kuka.
Ya yunƙura ya tashi zaune ya jingina bayansa da bishiyar.
Tari ne ya kufce masa wanda ya sa shi bezar da jini ta bakinsa.
Idan bai samu taimako ba babu yadda za a yi ya iya tsira da rayuwarsa.
Gari ya ɗan fara haske amma bai ga alamar akwai mutane a kusa da inda yake ba.
Nishi yake, yayinda duk lokacin da ya yi yunƙurin miƙewa sai ya kasa. Ƙarfinsa ya ƙare.
Ya rufe ido yana kiran sunan Allah...

***

"Kyauta, ki fito mu wuce fa"

Abubakar Sɗang ne a tsakar gidansu yana ɗauke da fartanya da kuma wata jaka da ya goya a baya.

Tun bayan rasuwan Babansu da rikicin Boko Haram ya ɓarke suke rayuwan taka-tsantsan.
An rufe makarantu dan haka ko result ɗinsa na gama HND bai samu ya karɓo ba. Makarantun Sakandare kam ba a san yaushe za a buɗe su ba. Kyauta har ta sallama da yiwuwar komawa makaranta nan kusa.
Babu abinda suke sai aikin gona dan ruwan bana ya zo da wuri, ana shiga watan August kuma ruwan ya fara yawa.
Kaka Medugu dai tun mutuwar ɗansa hankalinsa ya gushe.  Wani lokaci mantawa yake cewa ɗansa ya mutu sai ya kira Kyauta ya fara tambayarta "Adarju bai dawo bane?" Ko kuma yace "Babanku na gida kuwa?, na ga bai shigo ya gaishe ni ba"
Idan yana irin haka Kyauta kuka take sakawa saboda tuno mata da babban rashin da tayi ya ke. Wani lokaci kuma sai ta biye masa da cewa Babanta ya kusa dawowa.

Fitowar Kyauta daga ɗaki sai Sɗang ya sakawa tsohuwar machine ɗin Baba ƙirar Jincheng key ya fara burgata, sai da ya burga sau uku kafin ta tashi.

"Kaka mun tafi gona" Kyauta ta faɗa duk da ta san ba lallai ya tashi daga bacci ba.

A ƙofar gida ta tadda Sɗang yana jiranta. Ta hau machine suka wuce gona.

Tsoron hare-haren Boko Haram yasa mutane da dama basa iya fita gonakinsu dake wajen gari.
Duk da dai har yanzu babu wani hari da aka kawo kusa da su, amma suna da labarin nesa da su ana ta kai musu hare-hare.

Sai da suka sha aiki rana ta fito sannan suka ɗan tsaya dan su huta.
Cikin Kyauta ne ya juya ta miƙe da sauri tace wa Sɗang za ta ɗan kewaya.

"Ngwatam kar ki yi nisa, it's not safe"

Gyaɗa kai ta yi ta ɗau goran ruwa ta fara tafiya.
Duk inda ta duba sai data ga bai mata ba sai da ta hango wata ƙatuwar bishiyar kuka, ta ƙarisa wajen da sauri ta tsugunna lokaci guda kuma ta sake zawo. Idan ya saura kwana ɗaya ko biyu ta fara al'ada to a lokacin take fara ciwon ciki, wani lokaci har da gudawa.

Tana tsugunne ta rufe idonta tana ɗan fitar da nishi a hankali, sai kuma ta ji wani gurnani a bayanta. Tsoro ne ya shigeta ta haɗiye yawu da ƙyar ta kasa kunne tana jin kamar gurnanin a kusa da ita ne.  Hannu na rawa ta jawo goran ruwa ta yi tsarki a gaggauce ta miƙe.

GENERAL NASEER  ZAKI (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now