chapter three

293 9 0
                                    

*GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)

Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat

                           Page 003

Lokacin da aka zo aka sanar Indo ta haihu Iya Abu na zaune a ƙofar ɗakinta tana ƙullin Omo. Malam da kansa ya shigo ya faɗa mata dan zai shigo gida bayan ya dawo daga sallar La'asar Halilu mijin Indo ya tare shi yake gaya masa haihuwar.

"Namiji aka samu" Malam ya faɗa yana ƙoƙarin zama akan tabarmar da Iya Abu ke zaune. Ciwon kai da yake fama da shi ya sa tun Azahar ya baro kasuwa.

"Allah ya raya" Iya Abu ta faɗa ƙasa-ƙasa cike da kunyar wai 'yar tata har ta riga ta haihuwa.

"Ɗazu a kasuwa Malam Umari ke faɗa mini jibi ɗansa zai dawo, kin kuwa san shima yaron na sa a can Toro yake karatu. Ina ga shima Nasirun jibi yana hanya"

"Alhamdulillahi" Iya Abu ta faɗa tana washe baki.

"Allah ya dawo da shi lafiya"

Ga Makaranta nan nan a Azare amma haka Nasiru ya tsallake ya tafi Toro. Ita dai ko kaɗan ba ta son Nasiru yayi nisa da gida. Shine fa magajin gidan gaba ɗaya. Sauran matan da ke gabanta yanzu da an kwana biyu da ɗauki ɗai-ɗai za a aurar da su su tafi gidan mazajensu. Amma Nasiru shine Babban gida.

Iya Abu ta miƙe tana goge sauran burbuɗin Omo a jikin zaninta ta ɗauki fantekar kayanta ta shiga da shi ɗaki.

Yaran suna dawowa daga Makarantar Allo da Iya ta faɗa musu Indo ta haihu suka wanke ƙafa suka tafi duba jariri. Haihuwar Indo na biyu kenan, ta farkon da ta haifeta shekara uku da suka wuce bata zo da rai ba sai kuma ɓari da ta yi sannan wannan.

Kamar baki washegari da Asubahi Iya Abu ta tashi da naƙuda. Ta daure ta cigaba da ɗan ayyukanta kafin haihuwar ta zo. Dukkan haihuwanta a gida ta yi. Ungozomar anguwarsu ake kira mata ta karɓi haihuwar. A haihuwar 'yanbiyunta da ta ɗan wahala ne ma aka kira mata wata sabuwar Amarya midwife da ke ƙasan layinsu da suke kira da Sister Fati Ita ta ƙarfi haihuwar dik da kuwa ta so Iya Abu ta yarda su je Asibiti amma ta ƙi ta dage ita ba inda za ta je.

Wasa wasa Iya Abu na tunanin haihuwa kafin hantsi sai ga shi har Azahar shiru. Zuwa la'asar da Kande Ungozoma ta zo gaba ɗaya ta galabaita.  Shiru haihuwa har Magariba. An je neman Sister Fati a gida wai tana Asibiti.
Iya Abu ta galabaita ƙwarai. Da Malam ya dawo daga sallar Magariba aka ce har yanzu shiru ya ce su tafi Asibiti kawai.
Iya Abu ta ƙi fau fau. Wai 'yarta Indo ta haihu a Asibiti sannan itama ta je ta haihu a Asibiti, wannan abin kunya ne.

Sai kusan ƙarfe goma na dare da Sister Fati ta zo gidan sannan Iya Abu ta haihu. Lokacin ta gama yin laushi kusan ƙarfinta ya ƙare.
Bayan ta haihun Sister Fati ta ce ya kamata gobe da safe su je Asibiti a ƙara dubata.

Tunda aka ce mace ta haifa Iya Abu ta ji jikinta ya yi sanyi. Ta riga ta gama saka rai da haihuwar namiji sai ga shi macen ta sake haihowa.

Washegari Iya Abu ta tashi da yunƙurin fara aikace-aikacen da ta saba duk da kuwa jikinta babu wani ƙarfi.
Ta saba idan ta haihu da ƙarfinta take tashi ta cigaba da harkokinta kamar ba ita ta haihu ba.
Lokacin da ta ciko bokiti da ruwan zafi za ta shiga banɗaki sai ta yanki jiki ta faɗi...

***

*GOVERNMENT COLLEGE, TORO*

Kusan kowanni ɗalibi cikin ɗaliban da suka kammala jarrabawar ƙarshe a makarantar Government College da ke Toro murna haɗe da kewa ne cunkushe a zukatansu.
Daga an rabu yau ba a san yaushe za a sake haɗuwa ba.
Ɗalibai da dama za su yi kewar Senior Zaki saboda mutuncinsa. Ba ya ƙuntatawa juniors, amma fa idan junior yayi laifi zai sha punishment mai shiga jiki. Amma wai irin cin zali na haka kawai da seniors ke wa juniors ɗinsu senior Zaki ba ya wannan, kuma ko ya ga ana yi zai sa baki ya hana.

Tuni sun haɗa kayansu. Lokacin da aka fara kiran 'yan Azare senior Zaki ya shiga bankwana na ƙarshe da sauran abokansa da juniors ɗinsa da suka ɗauko masa kaya.
Wasu har da hawaye saboda senior Zaki daban ne a cikin dukkan seniors ɗin da suka gama. Yana da zafi sannan yana da sauƙin kai. In dai ba ka laifi to babu abinda zai haɗa ka da senior Zaki.

Senior Zaki ya shiga motar yana kewar gida, yau dai babu cin tuwon hostel sai tuwon Iyansa.
Lokacin da ɗalibai 'yan Azare suka gama shiga motar sai Direba ya hau hanya.
Ana tafiya ana taɗi. Wasu kuma na sake taya senior Zaki murnar kyaututtukan da aka ba shi. Har da masu cewa sai sun bi shi gida sun buɗe kyaututtukan kafin su wuce na su gidan.
Shi kan sai murmushi ya ke yana ayyanawa a ransa babu mai buɗe kyaututtukan da aka bashi sai Iya.

Motar ta su ta yi gudu sosai dan ana kiran sallar la'asar suka shigo Azare.

Tun daga bakin titi da Naseer ya sauka akan mashin yara suka yanyame shi suna masa oyoyo. Wasu suka ɗauki akwatinsa na ƙarfe wasu kuma suka ɗau jakar Ghana-must-go suka bi shi har cikin gida.
Yadda tsakar gidan ya ke a hargitse ya fara sanar da shi ba lafiya a gidan. Iya Abu bata barin waje da datti.

Ya juyo ya tambayi ƙaninsa Nura ɗan Baffansu da ya riƙe masa ledar tsarabar da ya siyawa su Iya a tasha.
"Ina mutanen gidan?"

"Sun tafi Asibiti"

"Waye ba lafiya?"

"Iya Abu"
Ai bai jira ƙarshen ba ya fita. Sashen Baffansa ya shiga inda Amaryar Baffansa da suke kira Umma Talatu ta sanar da shi Asibitin da aka kai Iya Abun.

Lokacin da ya isa Asibitin ya tarar ana buƙatar jini. Jinin Baba A+ ne ita kuma Iya Abu O+ ne. Wai an aika Chinade ƙannenta su taho.

Ran Naseer a ɓace ya fara yiwa Baffansa magana.
"Fisabilillahi Baffa tun safe a ce wai ana jiran sai mutanen Chinade sun zo sannan a sa mata jini"

Baffansa na ƙoƙarin bashi amsa ya share shi ya bi bayan wata  Nurse yana tambayarta ina zai je a ɗauki jinin. Ya riga ya san kalar jininsa O+ ne tun a Makaranta da aka  taɓa masa gwajin.

Sai da aka ɗau jinin ya fito ya samu Baba ma ya dawo. Dama zuwa yai neman kuɗi. Buhun hatsi ya kai kasuwa ya siyar a farashi mai rahusa duk dai dan ya samu kuɗin Asibiti.
Jini leda uku ake buƙata da safe da ƙyar aka samu aka sayi leda ɗaya aka saka mata shi yasa ma suka aika Chinade ɗin saboda 'yan'uwanta su zo.

"Baba" Naseer ya ƙarisa wajen yana dafa kansa saboda hajijiya da yake ji. Nurse ɗin ta ce ya tsaya ya huta amma ko minti biyar bai yi ba da aka ɗau jinin ya fito.

Baba ya riƙe shi ya zaunar da shi kan kujera.
"Sannu ko. Allah ya maka Albarka"

Zuwa Maghriba mutanen Chinade suka iso. Amma saboda an riga an saka wa Iya leda biyu sai washegari za a saka leda na ukun.
Aka haɗu ana yiwa juna sannu.
Sai a lokacin Naseer ya san cewa Iya haihuwa ta yi. Taɓ! Yai ta mamaki dan hutun ƙarshe da ya zo gida har ya tafi bai san Iya na da ciki ba.

Wasa-wasa Iya Abu sai da ta yi kwana goma a Asibiti kafin aka sallameta. Zuwa lokacin 'yar da ta haifa ta rasu ana kwana huɗu da haihuwarta. Malam ya sa wa 'yar suna Jamila.

Mutuwar jaririyar yai wa Iya ciwo. Ko da ta dawo gida sai da aka ɗau lokaci kafin ta fara dawo da walwalarta.

********


Top-Notch season 3 wannan karan sun zo muku da daɗaɗan labarai guda uku.

NAZNEEN...exquisitely beautiful (Mai Dambu).
BINTUN BATUL (Shatuu).
GENERAL NASEER ZAKI (Azizat)

Za ku samu labarai ukun ta whatsapp a farashin 1300
Ɗaya #500
Biyu #900

Ku tuntuɓe ni ta whatsapp 08137311900.

*Account Details*

0008219237
Jaiz Bank
Azizat Hamza
08137311900

Ko kuma ku bibiyesu a manhajar Arewabooks.

@ Azizat
@Shatuuu095
@maidambu41






GENERAL NASEER  ZAKI (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now