eighteen

174 6 0
                                    

*GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)

Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat

*MMG'S*
_Chilli powder_
Tasty Yaji... *kin kuwa san sirrin haɗa yaji da garin ɗanwake mai kyau ko kuma dai a bar maganar kar ayi tone-tone?. To! matso Hajiyata ba sai kin wahalar da kanki ba, MMG's Tasty Yaji sun zo muku da sauƙi, ba ruwanki da jan hanci ko tari wajen dakan yaji. Kawai order za ki yi a kawo miki yaji mai kyau har gida. Ga kuma garin ɗanwake mai danƙo suɓul-suɓul Malamata . Domin gwada yajin mu da garin danwaken zaku iya tuntubar mu ta wannan lambar. 08094816690 ko ta wannan number 08157709148.* Sayan na gari mai da kudi gida, sai an gwada akan san na kwarai, sayan daya-daya ko sari akan furashi me rahusa.



Page 018

*2014, Gulak, Madagali"

Ƙarfe uku na rana Kyauta ta shigo cikin gidansu da sallama. Uniform ɗin makaranta ne a jikinta, tun daga tsakar gida ta cire ɗan ƙaramin hijabin da ta sa ta lanƙaya shi a wayar shanyar da ke bakin ɗakinta.

"Ngwatam"

"Na'am Baba"

Bata shiga ɗakinta ba sai ta juya ta shiga ɗakin Babanta. Sati ɗaya kenan yana kwance baya fita ko'ina.
Da zazzaɓi ya fara abin kuma ya zo ya zame masa babban ciwo har baya iya tashi.

"Baba gani" ta tsugunna gaban gadonsa.

"Gobe zan je Mubi, Sɗang zai raka ni Asibiti"

"Baba zaka iya zuwa kai kaɗai? Zan raka ka"

Murmushi ne ya suɓuce masa. 'Yar tasa akwai ƙarfin zuciya.
Wani lokaci ya kan tambayi kansa anya yayi adalci da ya zauna babu mace a gidan.
A shekarun baya yayi yunƙurin sake wani auren amma abubuwa basu tafi yadda yake so ba, sai ya zo ya haƙura.

"Kar ki damu, zan iya tafiya ni kaɗai. Sɗang yana jarrabawa ba zan iya cewa ya zo gida ba"

"Baba, Allah nima zan iya raka ka. Ina da ƙarfi sosai"

"Na san kina da ƙarfi. Ki tsaya ki kula da Kaka kin ji"

"Kaka fa ya warke. Jiya ma shi da Kaka Lazarus haka suka zauna suka yi ta shan giya. Ba abinda yake sai shan giya yanzu" ta yi maganar tana ɓata rai.

"Kyauta"

"Ni kam ka bari na bika" ta faɗa da shagwaɓa.

"Kar ki damu ba zan jima ba zan dawo"

Washegari Kyauta da wani yaron maƙocinsu Joseph suka raka Baba tashar mota ya wuce Mubi.
Sɗang yana karatu a nan Federal Polytechnic Mubi. Yana ma ajin ƙarshe ne, HND II.

Da uniform ɗinsu dama suka fita. Sai da motar su Baba ta tashi kafin suka juya suka wuce Makaranta.

"Kyauta kin yi assignment ɗin Maths?"

"Wallahi ba zan baka ka kwafa ba Joseph"

"Haba mana"

"Jiya ai da aka tashi kana ji Mirabel na kirana da mai ƙwala-ƙwalan ido baka ce komai ba"

"Kyauta ba haka bane"

"Ai dama Mirabel budurwarka ce sai ka je ta baka assignment ɗin ka kwafa" ta tura baki ta yi gaba ta bar shi.

Joseph ya bi bayanta yana bata haƙuri.
A haka dai suka isa Makarantar. Suna zuwa kuwa suka samu ana dukan makara.
Joseph ya bada hannunsa aka masa bulala. Ita kuwa Kyauta da aka zo kanta tsalle-tsalle ta fara tana ihu. Ƙarshe bulala biyu aka mata aka barta ta wuce maimakon bulala biyar.
Dama duk makarantar an san Kyauta Ngwatam Yahaya wajen tsoron bulala.

GENERAL NASEER  ZAKI (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now