chapter five

240 9 0
                                    

*GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)

Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat

                           Page 005

***

Suna isa bakin hostel ɗin suka tarar wasu seniors ɗinsu na tsaye da bulala duk wanda zai shiga sai an masa bulala uku a baya wai WELCOME TEA kenan.
Faruƙ Lawanti kaman ya kurma ihu wato ma dai gidan wahala Babansa ya turo shi. Mahaifinsa Kwamishinan lafiya ne a Kaduna. Ba ya son zuwa NDA mahaifinsa ne ya takura masa akan makarantar da zai yi kenan.

Nasir kam ko a jikinsa. Ya sani wannan somin-taɓi ne ma akan abinda za su tarar gaba. Kuma ko kaɗan bai yi dana sanin zaɓinsa na son zama soja ba.

Ko ɗar bai yi ba lokacin da aka zuba masa bulala a baya. Yayin da Faruƙ ke ta rawar jiki.

Suna shiga ciki aka nuna wa kowa gadonsa sannan aka gwada musu yadda ake gyara gado. Ba yadda Amarya ke gyara gado ba, yadda sojoji ke gyara gado. Aka ce kullum gadon su ya zamto irin haka ko kuma dukkansu su sha punishment. Ko zama ba su yi ba bayan sun canja cikin uniform da aka basu aka buga ƙararrawar fita cin abinci.

Ba su suka dawo ɗakin ba kuwa sai can dare kusan ƙarfe shaɗaya, dan kuwa daga cin abinci suka yi sallah aka sa su gudu. Bayan nan kuma aka kira su camp fire drill inda kowannensu sai da ya tsallake wuta. Suka dinga rawa suna zagaye wutan jikinsu na ƙuna saboda zafin wutan.

"Naseer ni fa zan gudu, ba zan iya wannan wahalar ba"

Naseer ya juyo gefen Faruƙ ɗin wanda tun da ya hau gado ya ke ta nishi gaba ɗaya jikinsa yayi tsami.

"Haba kai kuwa, tun daga ranan farko. Ka yi haƙuri dai har zuwa lokacin da zamu saba"

"Ni fa ba zan iya sabawa da wannan wahalar ba"

"Za ka saba"

Ƙarfe huɗu da rabi sai ga shi an buga ƙararrawar tashi. Faruƙ ji yayi kamar ma baccin da yayi bai kai awa ɗaya ba aka tashe su.
Tuni Naseer har ya miƙe ya gyara gadonsa kamar yadda aka koya musu jiya.  Yana ƙoƙarin cewa Faruƙ zai gyara masa nasa aka shigo duba su dukkansu sai suka ƙame. Faruk da wasu uku gadonsu ba a gyare yake ba  sai wasu guda huɗu da suka gyara gadon amma bai yi neat irin yadda aka koya musu ba.
Dukka ɗakin kuwa sai da suka sha punishment, da wanda yayi laifi da wanda bai yi ba.

A ranan aka fara koya musu deep water swimming da yadda za su iya tsayawa cikin ƙasan ruwa na mintuna.
Lokacin da aka gama gaba ɗaya sun galabaita.  Naseer ma ya ji jiki dan rabonsa da shiga ruwa tun suna yara da suke zuwa wanka a rafi.
Daga baya aka kai su aka fara koya musu yadda za su yi amfani da wuƙa su far wa abokan gaba.

Idan aka ce ana cin kwakwa a NDA to kuwa ba a yi ƙarya ba dan kuwa zuwa 'yan kwanaki da zuwan su Naseer NDA wasu da suka gaji da training da ake musu suka hau katanga suka gudu gida. Wasu kuwa cewa suka yi ba za su iya ba suka nemi a barsu su tafi. Ba dan Naseer da ya hana Faruƙ guduwa ba da tuni ya gudu dan ya riga ya gaji da wahalar makarantan.

***

Iya Abu na zaune a ɗaki tana ninke kayan wanki ta jiyo sallamar Malam a tsakar gida. Ya sako kai cikin ɗakin tana ƙoƙarin fitowa.
"Ina tare da baƙo daga Chinade, a kawo masa ruwa da abinci"

"Malam waye?"

"Amadu ne, ƙanin mijin Halima"

"Lafiya dai ko?"

"To, lafiyar dai muke fata"

A zaure suka zauna inda Malam ke tambayarsa mutanen gida. Bayan an kawo masa ruwan randa mai sanyi ya sha tukunna ya faɗi abinda ya kawo shi. Allah ya yiwa Halima matar yayarsa wacce ta ke ƙanwa wajen Iya Abu rasuwa, har anyi sadakan uku ma.

Lokacin da Malam ya faɗa wa Iya Abu sai da ta yi kuka. Halima ƙanwarta ta uku kenan, uwarsu ɗaya ubansu ɗaya.

Yadda Allah ya jarrabceta da haihuwar 'ya'ya mata ita kuma jarrabawarta tunda ta haifi Fatima yau shekara goma shahuɗu bata sake haihuwa ba. 'Ya ɗaya kamar mayya, gorin da kishiyoyinta ke mata kenan.

Da yamma bayan Amadu ya tafi Iya ta nemi izini Malam ya bar ta ta je Chinade dan ta yiwa 'yan'uwanta ta'aziya. Bayan kwana ɗaya Iya ta shirya ta tafi garinsu.

Ko da ta je gidan rasuwa yadda ta samu 'yar marigayiyar bai mata ba. Ga shi dai ta rasa mahaifiyarta amma babu wanda ya ke kula da ita. Halima ce mata ta biyu a gidan, saboda tsananin haƙurinta ya sa tsangwamar kishiyoyi bai hanata zaman aure ba. Ko shi Mijinsu Umaru yana jinjina mutuwarta dan ta fi sauran matan haƙuri da yi masa biyayya.

Iya Abu ta zanta da Umaru akan tana so ta riƙe Fatima a wajenta. Umaru ya ce shi bai yarda a je a saka 'yarsa a boko ba idan ba rasuwar da aka yi bama yana so kafin kaka'a ya aurar da ita. Daga jin haka Iya tace idan ya amince tana so ta haɗa zumunci ɗanta Nasiru zai auri Fatima. Da wannan batu Umaru ya amince ta tafi da Fatima.

Da zata dawo gida ta taho da Fatima. Malam yayi na'am da zaman Fatima tareda su amma maganar aure tsakanin Nasiru da Fatiman sai ya nuna kaman Iya ta yi gaggawa kar a zo Naseer ya dawo ya ce bai yarda ba.
Iya ta ce ai kuwa bai isa ba.

Ranan da aka kawo musu wasiƙar da Naseer ya turo tareda kuɗi sun yi farin ciki sosai. Hadiza ce ta karanta musu wasiƙar Iya ta riƙe wasiƙar tana shafawa tana jin daɗi a ranta wai wannan daga hannun Nasirunta ya fito.
Kuɗin da ya turo ya zo musu a lokacin da abubuwa suka ɗan ja baya.

"Dama ana biyansu kuɗi ne? Hadiza ba a Makaranta ya ke ba. Ko dai yaƙi aka tura su?" hankalinta ya ɗan tashi kada fa yaƙi aka tura su ake biyansu kuɗin aikin da suka je yi.

"Kai Iya, ya ce fa ana biyansu alawus na ɗalibai duk wata"

"Ayyo"...

***

Top-Notch season 3 wannan karan sun zo muku da daɗaɗan labarai guda uku.

NAZNEEN...exquisitely beautiful (Mai Dambu).
BINTUN BATUL (Shatuu).
GENERAL NASEER ZAKI (Azizat)

Za ku samu labarai ukun ta whatsapp a farashin 1300
Ɗaya #500
Biyu #900

Ku tuntuɓe ni ta whatsapp 08137311900.

*Account Details*

0008219237
Jaiz Bank
Azizat Hamza
08137311900

Ko kuma ku bibiyesu a manhajar Arewabooks.

@ Azizat
@Shatuuu095
@maidambu41









GENERAL NASEER  ZAKI (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now