chapter seven

231 7 0
                                    

*GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)

Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat

                           Page 007

*1999*

* Gulak, Madagali, Adamawa State*

Tun da safe John-Yahaya ke sintiri a tsakar gida saboda matarsa da ke labour. An kira Matron Mary ta zo ta duba ta ce lokacin haihuwa bai yi ba.
Kuma tun da Asubahi ta fara labour. Ba zai iya tuna haihuwar Sɗang ba saboda shekaru goma kenan da haihuwar sai dai kamar Tabitha ba ta juma irin haka ba.
Lokacin haihuwar Paul da dare ne kusan ƙarfe bakwai aka kira Matron ta zo ta karɓi haihuwar. Kafin ƙarfe goma na dare har ta tafi.
Haihuwarta na biyu kuwa da safe ya tafi gona da ya dawo da yamma ya samu an haifi Sɗang.
To daga haihuwar Sɗang sai da aka shekara goma kafin Tabitha ta samu wani cikin. Har sun cire rai da sake samun haihuwa sai ga ciki da rana tsaka.

John Yahaya Medugu mutumin ƙauyen Gulak ne da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Madagali a jahar Adamawa.
Mahaifinsa da kowa ke kira Kaka Medugu asalin ɗan ƙabilar Marghi ne ciki da bai.  Kaka Medugu tsohon mafarauci ne da ya yi tashe a zamaninsa. Sai dai yadda iyayensa basu karɓi addinin Kiristanci daga hannun 'yan missionary ba haka shima Kaka Medugu ya taso a mabiyin addinin gargajiya. Sai dai fa 'ya'yansa uku da Allah ya bashi duka mabiya addinin Yesu ne. Hakan ya faru saboda matar da ya aura ta karɓi addinin a farko farkon aurensu, sai dai duk yadda ta yi da Kaka Medugu bai karɓi addininta ba, amma kuma duk wani hidima na coci yana bada gudummawarsa. Hakanan idan matarsa na bikin Kirsimeti shima yana tayata murnan haihuwar Yesu Almasihu.

Gulak ƙauye ne da ya haɗa mabiya addinai uku, akwai Kiristoci waɗanda su suka fi yawa, sai kuma Musulmai waɗanda basu kai yawan kiristocin ba. Yawanci cuɗeɗeniyar Fulani ne ya shigo da musulunci ƙauyen. Akwai kuma mabiya addinin gargajiya wanda har yanzu suke riƙe da abubuwan da Kaka da Kakanninsu suka gada musu.
Sai dai shigowar Kiristanci da Musulunci yasa mabiya addinin ƙarfajiyan suka yi ƙaranci, yara da jikoki masu tasowa watsar da wannan addinin suke suna rungumar sabon addini da ya zamo silar haske a gare su.

Kaka Medugu yana ɗaya daga cikin tsoffin da ke ƙauyen wanda aka shaida cewa tasirin Kiristanci Ko Musulunci a ƙauyen bai sauya ra'ayinsu daga tubalin da suka taso ba.
Shi mutum ne mai daraja a idon mutane saboda matarsa ɗaya kaman auren zobe, duk da kuwa mabiya addinin gargajiya suna tara mata a gida. Shi matarsa ɗaya ce har ta mutu shekaru shabiyar da suka wuce, kuma bayanta bai sake wani auren ba.

Har yanzu yana taɓa farauta amma saboda jinyar da ke ƙafarsa ba kasafai ya ke fita ba, kusan yanzu noma ne ya ke son ƙwace sana'ar farauta da ya ke yi tun zamanin samartakansa.

Yaran Kaka Medugu biyu mata ne, sai ɗaya namiji wanda matarsa ta saka masa suna John amma sunansa na yare Adarju ne kuma har gobe Adarju Kaka Medugu ke kiran John.

John Malamin Primary school ne kuma manomi. Yayarsa Martha tana aure a Sukur ita kuma ƙanwarsa Dorcas tana aure a Maɗagali.

John mutum ne mai sauƙin kai da girmama mutane. Akwai shi da riƙo da addini sosai. Duk inda ya shiga a ƙauyen da kekensa sai dai ka ji ana ta Teacher John, Teacher John.

Shekara shahuɗu da suka wuce ya auri matarsa Tabitha. Haihuwar farko ta haifa masa ɗa namiji aka saka masa suna Paul. Amma ko rarrafe bai fara ba ya rasu. A wannan lokacin ne kuma zuwansa Yola wani aikin sa kai ya dawo ƙauyensu da sha'awar musulunci.
A hanyar tafiyarsu Yola aka musu fashi aka ƙwace musu komai. Wani da suka haɗu a motar ya taimaka masa bayan sun sauka ya kai shi shagonsa ya bashi kuɗi ya ce yai kuɗin motar komawa. Wannan abu ya daki ran John. Bayan sun gama abinda za su yi a Yola sai ya koma wajen mutumin nan Alhaji Abubakar dan ya masa godiya da ya je sai ya tarar Alhajin yana kulle shago zai je sallah.
Tun daga nan da ya koma Gulak ya ke bibiyar musulman ƙauyensu yana musu tambayoyi akan musulunci. Sai da aka kai kusan wata huɗu da dawowarsa daga Yola kafin ya karɓi kalmar shahada a wajen Alhaji Abubakar a can Yola.

Bayan matarsa ta sake haihuwa sai ya saka wa ɗansa suna Abubakar suna kiransa da Sɗang.
Daga lokacin da John ya musulunta ya ke amfani da John-Yahaya Medugu a matsayin official sunansa.

Matarsa bata musulunta ba, kuma hakan bai hana zaman lafiya tsakaninsu ba. Shi kam mahaifinsa Kaka Medugu da suke zaune tare da musulunci da kiristanci duk ɗaya ne a wajensa, dukka addinan biyu sun samo asali ne daga turawa da larabawa, basu da haɗi da abubuwan da iyaye da kakanninsu suka gada musu...

Tabitha bata samu haihuwa a gida ba. Tana labour tun safe har rana duk ta galabaita amma haihuwar ya ƙi zuwa, wannan ya sa John Yahaya ya je ya nemo motar a-kori-kura aka wuce da Tabitha Asibiti a can Madagali.
Haihuwa har tsakar dare kafin Tabitha ta haihu da ƙyar dan har ana maganar aiki za a mata washegari. Sai da aka riƙe su a Asibitin kwana biyu kafin aka sallamesu. Suka dawo gida da kyakykyawar jaririyarsu mai manyan idanu kamar na Kaka Medugu.

"Kyauta. Kyauta ce daga Allah" John Yahaya ya faɗa yana shafa kumatun yarinyar.
Ranan suna kuwa aka saka mata suna *KYAUTA-NGWATAM* (Ngwatam- gimbiya/Princess).

Kamar yadda Kaka Medugu ya saba idan aka yi haihuwa zai yi 'yan surkullensa dan ya san irin rayuwar da yaron da aka haifa zai yi. Wannan haihuwar ma sai da yayi abinsa.

Watarana Sɗang yana wasa da Kyauta a tsakar gida kusa da ƙofar Kaka Medugu ya kallesu ya ce "ka yi wasa da ita sosai kafin ku rabu"

John Yahaya da ke gefe yana wanke kekensa ya ce "Baba ka dena wannan magana"

Kaka Medugu ya kurɓi giyarsa dake cikin ƙwarya ya ce " Adarju na gaya maka Kyauta za ta yi nisa da gida"

John Yahaya yai shiru ya tsurawa 'yarsa idanu, can kuma ya girgiza kai ya cigaba da wankinsa.
Duk da dai addininsa ya hana shi yarda da canfe-canfe da duba, amma wasu lokutan Kaka Medugu ya kan faɗi wasu abubuwan kuma ka ga abin ya zo ya faru. Wannan yasa masa shakku a ransa.

Lokacin da Kaka Medugu ya faɗa masa sakamakon bincikensa cewa yai wai 'yarsa Kyauta za ta yi nisa da gida, sannan ita da yayanta Sɗang za su jima basu ga juna ba hankalinsa ya ɗan tashi. Ko Tabitha bai gayawa ba dan kar hankalinta ya tashi. Kullum dai yana addu'ar Allah ya tsare masa Kyauta, ya kula masa da ita har girmanta...

***

Top-Notch season 3 wannan karan sun zo muku da daɗaɗan labarai guda uku.

NAZNEEN...exquisitely beautiful (Mai Dambu).
BINTUN BATUL (Shatuu).
GENERAL NASEER ZAKI (Azizat)

Za ku samu labarai ukun ta whatsapp a farashin 1300
Ɗaya #500
Biyu #900

Ku tuntuɓe ni ta whatsapp 08137311900.

*Account Details*

0008219237
Jaiz Bank
Azizat Hamza
08137311900

Ko kuma ku bibiyesu a manhajar Arewabooks.

@ Azizat
@Shatuuu095
@maidambu41












GENERAL NASEER  ZAKI (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now