chapter six

230 12 0
                                    

*GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)

Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat

                           Page 006

***

Lokacin da Naseer ya taho hutu gida bayan watanni kar ka ga murna a wajen iyaye da ƙannensa. Haka aka dinga zuwa gaishe shi har yayyensa da suka yi aure sun zo gida. Indo ce dai da take Kano yanzu bata samu zuwa ba, wata ɗaya kafin zuwansa gida mijinta ya koma Kano dan ya samu aikin kamfani a can.

Naseer ya rame ya yi baƙi amma kuma jikinsa ya mummurɗe saboda training da suke yawan yi.

Sai da ya ɗan kwana biyu tukunna Iya ta same shi da maganar Fatima da kuma alƙawarin da ta yiwa mahaifinta. Naseer ya ce bai yarda ba shi ba zai yi aure ba sai ya gama makaranta. Ita kuma Fatima makaranta ya kamata a sata ba aure ba. Iya ta bar zancen a haka amma idan ya gama makarantar ba shi da mata sai Fatima.

Kafin ya koma makaranta sai da ya saka Fatima a makarantar je ka- ka dawo. JSS one aka saka ta dan tunda ta gama Primary bata cigaba ba.

Zuwa lokaci kaɗan ta sake jiki tana karatu abinta dama Babanta ne ya hanata cigaba da karatu amma Mamanta na son ta yi karatu.

Wani hutu da Naseer ya sake zuwa lokacin yana shekaransa na biyu a NDA ya tarar ana rikici da Hadiza. Ta gama Sakandare ta ce karatu zata cigaba Iya kuma ta ce bata yarda ba. Shi Malam dai ya ce ba zai yiwa 'yarsa auren dole ba duk da manemin nata kaman ɗa yake a wajensa.

"Yaya ni fa karatu zan yi. Baba da ya ke cewa idan na yi aure sai na cigaba shi fa Salisun cewa ya yi ba zai barni na yi karatu ba. A barni na yi karatuna a gida"

"Ka gaya mata karatu dai ba a gidan nan ba. Kina mace wanda kika yi bai ishe ki ba. Uban me za ki yi da bokon?"

Iya ta faɗa tana ɓantarar goro. Ita da Hadiza sun zamo kamar mage da ɓera a gidan kowa ba ya sarara wa kowa.

Naseer ya tsaya ya rasa ma ta ina zai fara yiwa Iya bayani. A wannan zamani karatu shine gatan mace.
Ya san me zai yi. Idan ya samu Malam ya masa bayani har ya fahimci mahimmanci cigaba da karatun 'ya mace shi zai iya canja ra'ayin Iya.

Malam dama akwai sauƙin kai. Kuma shi dake yana fita ya san yadda duniyar ke caccanjawa, yanzu yara mata har karatun gaba da Sakandare suke. Sai dai da ya ke anfi danganta hakan da 'ya'yan masu wadata shi yasa yake ganin kamar gara Hadiza ta yi auren idan ya so idan da rabon yin karatun sai ta yi a ɗakinta.

Kafin Naseer ya koma makaranta sai da ya tabbatar ya shawo kan iyayensa.
Iya dai taron dangi aka mata, uba da ɗa sun tsaya mata a wuya, ga itama Hadizar shegen naci kamar yayanta Naseer.
A layinsu kaf sa'annin Hadizan daga wanda suka yi aure sai wanda aka saka musu rana amma wai Nasiru ya dage da wannan bokon. Nasiru namiji ne idan ya yi boko mai zurfi babu matsala amma ita ɗiya mace ai rufin asirinta shine ta kasance a ɗakin mijinta.
Ga shi ana cewa matan da suka yi karatu mai zurfi basa yiwa miji biyayya.

Shekara biyu Naseer ya roƙawa Hadiza ko ta gama karatu ko bata gama ba bayan shekara biyu za ta yi aure.
Kafin ya koma Kaduna kuwa sai da ya tabbatar ya sama mata gurbin karatu a College of Education, Azare inda za ta karanci English.
Farin ciki a gun Hadiza ba zai misaltu ba. Tun daga lokacin ta sake jin ƙaunar ɗan'uwanta tana kuma ganin girmansa.

Iya dai har Hadiza ta tare a Hostel bata saki jiki da ita ba. Amma fa a hakan da za ta tafi sai da ta ƙulla mata kayan yaji da ƙanzo da bushashshen zogale da garin kunu.

Hadiza da ta tare a hostel ta buɗe bagco bag da Iya ta bata sai ta sa dariya. Iya dai akwai fushi, amma hakan baya hanata nuna soyayyarta ga 'ya'yanta.
Insha Allahu kuwa ba zata zubarwa iyayenta da mutunci ba. Abin da suke gudun ba zai taɓa faruwa ba. Karatu ta zo yi, karatu za ta yi tsakani da Allah. Ba za ta taɓa watsar da karatun da aka musu da tarbiyyar gidansu ba...

***

*1998, Azare*

"Malam ba za ka sha kunun ba?"

Malam ya girgiza kai yana sauke numfashi a hankali. Daga zazzaɓi da ya ɗan ji sauƙi ya fita kasuwa sai ya yanki jiki ya faɗi. Kwana biyar kenan baya fita, sun je Asibiti an kwantar da shi kwana biyu suka sallamo shi.
An ce wai jininsa ne ya hau.

"Zainabu"

"Na'am Malam"

Hannunta ɗaya ya kamo yace " ba abinda zan ce miki sai dai Allah ya haɗa mu a Aljannah"

"Malam..."

"Nagode Zainabu. Nagode da kulawarki gareni"

"Malam tsakaninmu ai babu godiya"

Ya ɗan yi murmushi.

"Idan Allah yayi ba zan ga Nasiru ba ki ce masa na yafe masa duniya da lahira sannan ina masa wasiyya da ya kula da mahaifiyarsa da ƙannensa"

"Malam ka dena irin wannan maganar, babu abinda zai same ka. Nasiru zai zo ya sameka da lafiyarka"...

Duk da an aikawa Naseer wasiƙa ya zo gida mahaifinsa ba lafiya bai samu zuwan ba saboda an kusa hutu. Wannan ya fi komai baƙantawa Iya rai akan irin makarantar da yake.
Naseer bai zo gida ba sai bayan kwana goma shashida da rasuwan Malam.

Tun daga hanya da aka fara masa ya haƙuri jikinsa yai sanyi. Ya shigo gida gwiwa a sace. Iya na nan kamar kullum tana zaune a ƙofar ɗakinta da rediyonta a hannu tana sauraron labaran yammaci. Tana ganinsa ta tashi ta shige ɗaki.

Naseer ya shigo ɗakin ya tsugunna gabanta.

"Iya, Baba..."  muryarsa ta yi nauyi. Yana so yayi kukan amma babu hawayen kuma babu halin kukan. An riga an musu horon da hawayensu ba ya kusa.

"ɗan gidan Jiji bai aika maka da wasiƙa ba?"

"Iya...na samu wasiƙar kwana goma da suka wuce, na nemi damar tahowa gida ba a barni ba"

Ta tura fiskarta gefe ta ce " ka dai san yanzu kai ne Babban gidan"

"Allah ya jiƙan Baba ya masa rahama" ya faɗa da raunatacciyar murya

Iya ta amsa da Amin.

Sai da ya shiga ɗaki ya fara naushin gini yana ƙoƙarin rage raɗaɗin da zuciyarsa ke masa. Yau dai ɗaya ya ji a ransa ina ma shi ba soja bane ya yi kuka son ransa. Ga shi hutun ƙarshe da zai koma makaranta bai samu yayi sallama da Malam ba saboda ya tafi gaisuwar ta'aziya a can wani ƙauye Dunkurmi ta wajajen Misau.

Kafin ya koma makaranta Iya ta sake kawo masa maganar auren Fatima wacce a yanzu take cika shekara goma shabakwai, kuma ta kammala aji uku na sakandare.

Ga kuma maganar Hadiza itama. Duk dama dai yanzu wani Likita ke nemanta maganarta da ɗan'uwanta ya banje. Tun kafin Malam ya rasu Dr Anas ya zo neman izinin hira da Hadiza wacce suka haɗu lokacin da ya raka ƙanwarsa makarantarsu Hadizan. Da ke dai Hadiza ta nuna tana ra'ayinsa sai Malam ya ce a bari idan Naseer ya dawo sai ya turo.

Shima Naseer ɗin ya ji daɗin zaɓin Hadiza. Duk da dai Dr Anas ɗin yana da mata da yara biyu amma kasancewar ya yarda zai bari ta kammala karatunta sai hakan yai wa Naseer daɗi, ko ba komai dai ta samu mijin da ya ke da burin inganta rayuwarta.

Kafin ya tafin kuwa aka zo neman aurenta. Baffa ƙanin Malam ya bada ita aka saka lokacin biki farkon shekarar 1999.

Auren Naseer da Fatima ma dai babu fashi dan Iya ta nuna iya abinda zai mata kenan ya wanke fushin da take masa na ƙin zuwansa gida lokacin jinyar Malam. Tuni su Baffa suka je can Chinade suka nemawa Naseer auren Fatima a wajen mahaifinta. Lokacin da aka je tambayar Naseer ya riga ya koma makaranta amma da yardarsa aka je tambayar. Shi ma ɗin an saka bikinsa dai dai dana Hadiza...

***

Top-Notch season 3 wannan karan sun zo muku da daɗaɗan labarai guda uku.

NAZNEEN...exquisitely beautiful (Mai Dambu).
BINTUN BATUL (Shatuu).
GENERAL NASEER ZAKI (Azizat)

Za ku samu labarai ukun ta whatsapp a farashin 1300
Ɗaya #500
Biyu #900

Ku tuntuɓe ni ta whatsapp 08137311900.

*Account Details*

0008219237
Jaiz Bank
Azizat Hamza
08137311900

Ko kuma ku bibiyesu a manhajar Arewabooks.

@ Azizat
@Shatuuu095
@maidambu41











GENERAL NASEER  ZAKI (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now