3-5

814 33 0
                                    

_3-5_

*SO*
*GARWASHI*
*NE*

_NA NANA DISO_

http://nanadisoo.blogspot.com

© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Ohh Ne sumayya wanne irin Hali ne Da khaleel..

" Shukrah ce tace Allah Anty anty gimbiya batada hankali...

" shukrah sa'arki ce?

" Amma Anty ki duba yadda yarima yak'e wulak'anta ta Amma ko ajikin ta, sai kace wata mayya wallahi, Gata da kyau ilimi gata 'yar sarki Amma ta nanewa makiyin ta, Ni dama mai martaba ya korata masarautar su kowa ma ya huta!..

" Shukrah kenan, ( *So*) Ake gayamik'i, wallahi soyayya gaskiya ce domin Allah kadai ke dorawa bawa, Ku daina jifan najlat da kalamai marasa dadi domin ita kadai tasan yadda tak'e ji, kuma indai ta tsanan ta da Addu'a to soyayyar khaleel ma sai ta rabu da ita gaba daya kinga daga Nan zaku tabbatar *So Garwashi ne* Daga Allah ya yaye mata zai zama kamar toka...

" Hak'ane Anty Ai wallahi tsana batayi ba, kuma Allah yarima baya kyautawa...

" Ke dai babu ruwank'i domin Ak'an Najlat zaku iya batawa da mai martaba...

" Tohm Anty...

♡♡♡♡♡

Gimbiya Najlat tana zaune ak'an gadon asubutin babu abunda tak'eyi sai tunani, da kuma yadda tak'ejin tausayin k'anta kamar daga sama taji anyi sallama anshigo...

" Gimbiya haka kika dawo? Haba najlat?

" Tayaya suk'abar ki kika shigo?

" bakowa a kofar ina tunanin sun tafi sallah, Dan Allah gimbiya menene haka kikeyi dubi yadda kik'a dawo?

" Kuka tafashe da shi tare da fad'in fa'iza wallahi inason ya khaleel, Amma shi bai damu dani ba baya kaunata kwatakwata....

" mtsww wallahi kina ban haushe akan namiji kike wannan abun? To kaddai ki kashe kanki...

" Haba faiza yaya zakici haka? Me isa bazaki tausayamin ba?

" Najlat kin tsausaya min alokacin da babu wanda ya dubeni kinsa an 'yanta ni da mahaifiya ta, faiza ce ta zauna kusa da ita, wannan kukan da kikeyi kamar ni nakeyi, banason b'acin rank'i Amma kuma k'in dakko abunda yafi karfina kuma yafi karfin k'i....

"Najlat ce ta goge hawayen ta Nasani Nasani Amma ki yarda dani Allah shine ya doramin son ya khaleel, faiza taba jikina kiji wannan zafin saboda shine, hawaye na saboda shine, Allah shi yake saka so kauna kuma ta gino ajikin dan adam!...

" hakkane najlat Amma karki manta irin cin zarafin da yake miki kar kuma ki manta mak'iya suna mana dariya...

" Nasani anyi agabana ma, wane sabon hawayen ne yazuba tace yazanyi to ina sonsa ina sonsa wallahi....

"Look husna love is love and kiyayya babu dadi kiyi kokarin rabuwa da yarima kicire shi cikin ranki, nasan hakan bazai yihu lokaci daya ba Amma ki nisance shi, ki koma masarautar mu kibar gidan su...

" Najlat ce ba lallai Na iya ba, Amma karki manta faiza tunda mahaifiya ta ta mutu acikin masarautar mu babu mai kula dani babu mai sona hatta mai martaba ban isa Nayi hira dashi ba, goggo kullum dokana zagi cin mutun ci, wanene yak'e shigowa ya kula dani? Wanene yasan damuwa ta? In inacikin matsala yana kokarin warware min? Wanene yasani a islamiya? Wanene yayi kokarin ganin nayi karatu? Kuka tasaka tace ki gayamin faiza?

" Najlat yarima khaleel ne!

" To me isa zakice Na daina sonsa Me isa? Kinsan duk duniya tun ina karama Nafi shakuwa dashi, shiya koyamin sonsa yasace zuciyata da kyakyawan dabi'arsa, daga karshe Naga ashe ba sona yakeyi ba tausayi na Yak'eji.....

" Fa'iza ce ta saka kuka itama tana tausayin najlat...

" Najlat ce tace k'inga kema kuka kikeyi kina tausayi na faiza banda zabi, Amma zanyi kokari gurin gayawa Allah ya yayemin sonsa, zan kuma koma masarautar mu koda kuwa mutanen ciki zasu kashe ni....

" Fa'iza dai ta k'asa cewa komai, Sanarwa suk'aji cewa mai martaba zai shigo...

" Sannu najlat yajikin?

" Murmushi tayi tace Na warke.

" To zamu iya tafiya?

" Fa'iza ce ta gaida shi..

" eh inason zan koma gida yau ..

" shikansa yaji dadin maganar nan, toh bakomai da daddare sai Akaiki...

Lokacin da suka isa masarauta sai girmama sarki akeyi bangaren sarauniya fatima ta shiga kallon ta kawai najlat tayi sannan tasa ahada mata kayanta!...

" Sarauniya fatima ce tace kinsan nice khaleel ko sai yadda nagaya mai, mahaifiyar sa sama da shekara 20 ba lafiya batada amfani, kuma soyayyar dakike masa sai ki mutu Amma bazaki aure sa ba, Haha karkicimin kwadayin kizama matar sarki nan gaba ko? To gimbiya maryam zai aura wacce bata nacewa maza sai sunci suna sonta...

" kirjin ta taji yafara zafi, cikin hawaye tace amatsayin uwa Na dauke ki da yau sai nagaya miki maganar da har ki mutu bazaki manta ba...

" Mamaki ne yak'amata sarauniya maryam hak'an yasa takira jakadiya....

" Najlat ce tashiga dak'in ta zata dauk'i wayarta faiza tace kinga abunda nake miki gudu ba kinzama abar tsokanar kowa...

" Fa'iza bama wannan ba wai su tunanin su dan nazama matar sarki shine nakeson ya khaleel...

" Hmm mudai tafi..

" Bari Naje gurin inna maryamu ..

" Lok'acin da Najlat tashiga dak'in da kuka tafito ganin halin da babar khaleel take ciki kuma tayi alkawarin duk wanda yayi mata wannan jefan sai yakoma kansa, Ahanya ta samu fadawan dak'e kula da'ita tace zan dinga aiko sako sai ka dinga bata!...

" Tohm inshaa Allahu gimbiya..

" Tana fitowa waje ta tarar da khaleel yana karasowa ya kifa mata mari...

" Rik'i gurin tayi menayi maka?

" kinji kinayi wa hajiya rashin kunya harda sai kin aureni ko?

" Anyi din saime dan kaga inasonka shine zaka dinga daukar kowane yayi kasa Akaina, ta saka kuka to daga yau bazaka kara ganina ba ma, kuma Allah zai yayimin sonka....

" Dana huta kuwa, khalifa abokin sa ne yace Amma yarinyar nan tayi dama ne zataso ni....

" wannan fitsararriyar kaga zo karaka ni zance bari Na shirya...

ASALIN SU...

Urs *Nana diso*

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO

SO GARWASHE NEWhere stories live. Discover now