57-60

957 30 4
                                    

_57-60_

*SO*
*GARWASHI*
*NE*

_NA NANA DISO_

http://nanadisoo.blogspot.com

© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Haba ummi wannan maganar bata dace dake ba yadda kikeson najlat?

" Kaga kasan mai sonka, duk wanda bayason d'anka ai ba masoyin ka baniba...

" Amma ummi ai bakisan yadda take sona acikin ranta ba..

" Kaga mai martaba ba dolene kafadi abunda kasani ba Amma yanada kyau kasan me kake fada...

" Shiru yayi baice mata komai ba har ta fita....

Queen najlat dake faman kuka duk hankalinta ya tashi umminta ce yau tayi mata haka?

" Ruma ce tashigo tace me yafaru ranki shi dade?

" jiyowa tayi tagyara mayafin dake jikinta sannan tace abunda ummi tayimin bantaba tunanin sa ba wallahi na dauketa amatsayin mahaifiyata wacce zata sharemin hawaye na Amma ki dubi abunda tayimin...

" Hakuri zakiyi ranki yadade kuma kima sai kin gyara babu uwar da zataso a tsane d'anta...

" Toh Allah yakaramin hakurin rashin uwata wato ako dayaushe takan cemin Karamin yabon da mutane za su yi maka, ya fi yawan yabon da ka yi wa kanka....Ada nayi hakuri da tozarcin da danta yayimin ya wulakanta ne yanuna baya sona Amma ki duba yanzu nice matarsa kuma ace Bazanyi zuciya ba? Ko kare ya cinye tawane??? Gwara arabu da ahargitsa zumunci...

" Batasan sarki khaleel yana bayanta ba tuntuni yayiwa ruma alamar tafita...

" gyaran muryar da yayi shiyasa ta jiyo fuskarta dake wanke da hawaye....Najlat nasan ummi bata kyauta miki ba Amma yakamata kiyi hakuri nasan bakyasona Amma kulawarki gari ne zai rufe sirrin zuciyarki...

" kana tunanin zama da wanda bakyaso zai iya kwarar ka?...

" Queen najlat abunda bazai taba yihuwa ba shine rabuwar mu, Nasani samu shine farin cikin mai nema.....

" Ai kai bakada matsala tunda Ne kakeso Kuma kana tare dani...

"Shi gani sai dai ido,karkisa natako garwashi, ina kaunarki inakuma son zama dake tarin dayayi shiyasa ya zauna abakin gadon ta...

" Shiru tayi sannab tafita daga dak'in....


Haba jakadiya wannan impossible ne tayaya zaace wannan jakar yarinyar tazo har tana kokarin shiga zuciyar sarki, naje ina yimasa sannu da zuwa amma kawai ambaton sunan najlat yake...ai wannan iskance ne wallahu ita wacece wai??

" Jakadiya ce tace ranki yadade yana dakyau kiyi hakuri..kuma ita wannan sarauniyar wato queen najlat dakanki zaki fidda ita tunda daman auren dole akayi mata....

" what kina da tabbacin abunda kike fada??

" kwarai kuwa queen najlat ta aure sarki ne abisa umarnin mahaifin ta kuma batason sarki koda da kwayar zarrah.....

" queen bilkisu ce tace really? Wannan labarin yayimin dadi sosai da sosai kuma sarki mutum ne mai mutukar son kulawa kuma bata bashi hahaha zatasan cewa queen bilkisu ba saar wasanta bace ba.....

" haka yakamata kiyi sarauniyata ki kuntata mata da muggan kalamai kada ki raga mata...

" Mekiwa tayi ta huce zuwa fadar sarki nan ta tarar babu kowa aciki sai ta huce dakinsa najlat na zaune kan wata kujera tana danna waya, queen bilkisu ce tace sannu fa...

SO GARWASHE NEWhere stories live. Discover now