95-100

616 23 2
                                    

._95-100_

*SO*
*GARWASHI*
*NE*

_NA NANA DISO_

http://deejarhberver.wordpress.com

© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Cikin sanyin murya tace kayimun uwa kayimin uba...yaune a so na hau dokin muk'amai... cikin hawaye tace Allahu ina gode maka da Nufinka abun ya tabbato kabani miji mai kaunata, ga arzikin d'a kamini, Allah nagode maka..Mijina Allah yasaka maka da Alheri....

" Sarki khalil ne ya bude idonsa tare da yin murmushi sannan ya zauna kusa da'ita yace tabbas Allah shine abun godiya domin ya Azurtani da namiji kuma kima ina godiya agareki da kike gyaramin wasu halayen nawa kike kuma yimun addua gashi yanzu kin kin haifamin wane sabon farin cikina...

" Hawaye ne ya wanke fuskarta tace duk abunda nayi maka abaya kayafemin ....

" kada ki damu najlat komai ya huce nidai fata mucigaba da zaman lpya fiye da baya...

" Hannunsa ta rike alokacin queen bilkisu zata shigo sai ta tsaya dataga sarki khalil yana goge mata hawayenta...

" queen najlat ce tayi murmushi tace mijina kaunar ka na tsumani babu kamarka afadin duniyar nan, sannan ta mike zaune tace karka juyamin baya afadin duniyar nan ina fata alkawarina yana nan?? Da kai kadaini mijina na yarda na tabbata kaima zaka shida kasan inason ka,sannan tasa k'anta aka fadarsa tace tsoro nake kada arabamu ni nafiso mutuwa ta rabamu... sannan ta shafa fuskarsa tace kaunarka ta mamayi ruhina...

" matata ki daina kuka ina tare da ke..kuma mai hakuri shiyake nasara har yadafa dutse yasha ruwansa, Nima banda kamarki duk duniya...Nayi dacen matata tana sani dariya mai kunya akwai ladabi da biyayya, matata kinada kyau amma bakida girman kai, babban farin cikina kin zama matata,nayi naam da hankalin ki nutsuwar ki da nazarinki, kisa aranki ni sarki khalil nakine, bazan barki ba har abada kina gidana, Wanda yasamu kulawa A so kamar yarda kikaye min to lallai soyayya tayi masa rana...

" Rungumesa tayi sannan tace ina boy dina akawomin nagansa...

" A lokacin queen bilkisu tayi maza tafita idonta cike da hawaye sannan ta samu guri ta zauna sarki khalil yana zuwa ya tadda ita tanata kuka hakan yasa yaji babu dadi zama yayi kusa da'ita sannan yace my queen meke damunki???

" cikin sanyin murya tace kaine damuwa kaine matsalata anya kasan yadda nakesonka kuwa Amma....sai kuma tayi shiru...

" sarki khalil ne yace bantaba samun matsala dake gurin soyayya ba kuma kinfi kowa sanin son danake yimiki queen bilkisu kinsan....

" Nasan ban haihuwa ba bazaka soni kamar najlat ba, to ga 'danta kaimata Nima watarana zansamu ai...

" haba my queen kidaina irin zancen nan mana haihuwa ai nufin Allah ce....

" Goge hawayenta tayi sannan tace ni natafi ga ga yaronta...

" Karba yayi yana kallonta tashiga mota...

" Su ummi da momy amal nusaiba duk suncika dak'in jaririn ya basu sannan yabi bayanta zuwa masarauta....

Queen najlat tana fitowa daga bandaki mumy tace lallai su najlat anzama babba...

" ummi ce tace aine nasamu suriki...

" Amal tace ina ai duk bayayi daku ko kawoshi ma tabashi yasha...

" queen najlat dai murmushi tayi sannan ta karbeshi batasan lokacin datace Allah nagode maka ba!

"Sadiya ce tace dole ki godewa Allah wannan santalilin d'a mashaa Allah...

SO GARWASHE NEWhere stories live. Discover now