8-10

742 32 0
                                    

_8-10_

*SO*
*GARWASHI*
*NE*

_NA NANA DISO_

http://nanadisoo.blogspot.com

© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Ma Sarautar Fablita Masarauta ce da ta shafi tahiri, sarak'ai da yawa sunyi mulk'i a cik'in ta, Allah ya basu gonak'i. Basu da arzuki sosai kamar Na sauran ma sarauto, Amma k'uma mutanen cik'in ta sun k'asance masu hik'ima da k'uma ilimi, Sark'i suleiman ya gaji sarauta a gurin babansa Na biyu wato sarki kamalu wanda ya dau tsawan shekara yana mulki daga Nan D'ansa ya gajishi wato sarki suleiman..

Lok'acin Da sarki suleiman ya fara mulkin sa yayi gyara sosai a kasarsa da jaharsa har ta k'ai wasu ma sarautar Suna Adawa dashi, Amma saboda jajir cewarsa da kuma rik'o da addinin sa yasamu sauki daga abubuwa, daga 'Yan uwansa har mutan gari suk'anyi masa asari musamman da yasa dok'ar rashin shaye shaye acik'in masarauta, duk wanda aka kama yanada bulala 20 da fasa dutse da k'uma gidan yari Na wata daya, hak'an ya taba faruwa da k'aninsa abdul da kuma ciroma inda yayi musu huk'uncin da ya zarta daga Nan suka dinga zambada masa asiri ak'an kada ya haihu kuma ya mutu ma baki daya, Abunka da mahaddacin kur'Ani kowacce kafa yasani alok'acin da jik'in sa yafara shiga wane yanayi Nan ya bada sanarwar ya tafi kasar waje, yasa matansa suka samo masa ganyen magarya da kuma ruwa da dutse Nan ya karanta ayoyin karya sihiri cikin ikon Allah yasamu lafiya, mahaifiyar sa hajiya inge kullum addua takeyi masa....

Sarki suleiman babban dattijo ne da ya tafi shekara 70 zuwa da uku, matarsa ta farko itace itace maimuna wacce sunyi tsawon shekara 40 tare duk d'an data haifa mutuwa yak'eyi, Matace mai zafi kuma tana mutukar son Mai martaba domin kuwa da'ita da k'annan sa d'uk wace zata shigo sai sun fiddata, Nan Sark'i ya hango k'anwar sarki salim wato maryama awannan lok'acin ne ya Auro fatima...

Maryama babu ruwanta domin macece mai sanyi bata iya tashin hankali ba, Mutanen gidan suk'anji dad'in zama da'ita hak'a ta dinga kishi itada sarauniya maimuna har tak'ai sarauniya maimuna tayi mugun furuci ak'an sarauniya maryama inda tace indai har ta sak'e ta haihu agidan to ta tabbatar mata shine sanadiyar mutuwar ta kokuma sanadiyar kwanciya cutar ta, maganar nan tak'an ta yar mata da hank'ali Amma kuma kullim Allah tak'e sanarwa, bayan ankawo sarauniya fiddausi da kwanaki aikuwa sai ciki ya bayyana tun daga wannan lok'acin sarauniya maimuna ta dinga jifan sarauniya maryama, cikin fargaba sarauniya fiddausi itama ta samu ciki dayak'e ita hatsabibiya ce sai suka dinga asirin tare da sarauniya maimuna...

Wata rana sarauniya maryama tana zaune tana cin dabino jakadiya nayi mata fifita sai kuwa sarauniya maimuna ta shigo tace mata Ai lallai sai ta zubar da cikin...

" Cik'in kalami mai dadi tace haba hajiya maimuna tayaya zan zubar da cikina kuna ganin sarki bai da magaji, kuma in nazubar ai banyi adalci ba...

" Ke gafara can tunda ban haihu ba ai kuwa banga uwar wacce zata gaji sarauta ba, ke bari in gayamiki d'anki ba zai tabayin sarki ba kuma ina kara sanar dak'e ki barar da cik'in Nan...

" Hmm girman ki kuma ya wadi sarauta? Dakata malama indai dana bazaiyi adalci ga mutane ba bana fatan yayi sarauta wallahi, kuma haihuwa da nufin Allah zanyi, d'ana ba shige baniba kuma kada ki manta cewa fa Nema jinin sarautar ce ko k'in manta sarki abdullahi babana ne kuma karki manta sarki salim shine akan mulki, to wacce kwadayin mulki zanyi, Gaba daya kun dameni akan cik'ina haba, Naga kina cikin jahilci ki koma makaranta malama...

" Indai ina rayi kafin gobe k'in mutu..

" Kinji jahila mutuwa haihuwa aure Na Allah ne, kuma bak'i isa ki kasheni ba sai kwana ya k'are...

" Zaki gani..tafice daga dak'inta directly fadar sarki suleiman ta nufa tun daga hanya fadawa suka sanar sarauniyar fiblita sarauniya maimunatu tana tafi zuwa fadar sarki suleiman, Anan kowa ya watse sarki k'am sai da yachanja zama saboda shi k'ansa tsoronta yak'eji...

SO GARWASHE NEWhere stories live. Discover now