_83-90_
*SO*
*GARWASHI*
*NE*_NA NANA DISO_
http://nanadisoo.blogspot.com
© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
A firgice jakadiya tace guba?? Ranki yadade duk tsahon shekarun da sarki yayi yana jiran magaji gaskiya ne bana iyawa!!!....
" Fatuwa ce tayi murmushi tace wai ke yaushe zaki waye ne? To Nima bantaba haihuwa ba gwara muzama daya dashi ai....
" Jakadiya tace Amma....
" Amma me? Kinga zanbaki jaka 100 indai kikayi min aikin nan...
" Azabure matar ta miki jaka dare? To zanyi ranki shi dade me za'a zuba mata acikin abincin....
" Fatuwa tayi dariya tace yanzu kikai magana ke kina gidan sarauta ace bakisan mugunta ba? To kinga wannan koren abun shi yabarar wa da queen bilkisu ciki to itama dashi zaayi mata amfani boka tsullu ne yabani shi gashi sai ki kiyaye....
" To Ranki shi dade zanyi yanda kikace sannan tabar dak'in....
" Wata muguwar dariya fatuwa tasaka sannan tayi cikin dak'inta....
Ruma ce yau kusan sati daya fa kenan kina zanbada amai yakamata kiga likita queen najlat...
" likita kuma haba ruma daga amai sai ganin likita bakina ne da babu dadi shine kadai matsalar taron dazaayi afada yau bazanjiba kisanar banjin dadi...
" queen najlat lafiyarki tafi komai ni tunjiya ma zargin ciki nakeyi miki...
" Queen najlat ce tazaro ido a firgice ciki???
" Ruma ce tasa dariya tace to menene abun mamaki bayan da mijinki?
" Ni banda komai karki kara fadamin haka...
" queen najlat kenan Allah kinfi sarki khaleel son haihuwa amma kidinga basarwa ke da kanki yakamata kiyi fatan cikin ne ta bahaushi yace da karan wane yayi farauta gwara naka yayi...
" hmm kinga zan dan kwanta sai anjima..
Sarauniya fiddausi ke zaune acikin fadarta can husaina ce tace hajiyarmu yakikayi shiru?
" Murmushi tayi tace yarima adamu nake tunawa daf da zai mutu sai dayace hajiya ki gyara halinki wallhi khaleel masoyin mu ne, Amma ban saurari sa ba, yau da kaina kinga nagyara halina yadda sarki khaleel yake kula dani abun har kunya yake bani ga matarsa yasamu ta gari...
" husaina ce tace dama gimbiya mero tace dakanki zakiyi sanyi, Yanzu duniyar fa da ka cuce wane gwara acuceka...
" Tabbas shiyasa akace Kada ka yi farin ciki da samun al'amrin da ba zai wuce ka ba...
" Tabbas hajiya..
" Allah yabawa queen najlat 'yaya nagari..
" Ameen hajiyarmu bari naji makaranta nadawo..
Yau Wata 5 kenan Queen najlat tayi kiba ga ciki ya danyi alamar fito, yanayin datake ciki yasa bata fiya shiga mutane ba ummi ma in tazo kusan kullum tana zaune da hijjabi, aman da takeyi ya ragu sai dai yawan kwadiya da hakan yakansa taji haushin kanta, sarki khaleel kuwa wane kara sonta yakeyi kullum yanayin kibar datayi yana mutukar burgesa saboda shi mutum ne mai son kiba....
" Queen bilkisu ke zaune tace yanzu kana nufin bazaka kaine kasar waje adubani ba???
" Sarki khaleel ne yace adubaki akan me??
YOU ARE READING
SO GARWASHE NE
RomanceLittafi ne dake magana akan soyayya da illarta, wulakanta mutane da kuma tozarta tasu , nuna isa da girman kai..da kuma illar tsafi da shaye shaye...Littafine dake nuna cewa shi so gamuwar jini ne, kaunata da soyayya gaskiya ce sai dai bakowa ake zu...