80-83

799 26 0
                                    

_80-83_

*SO*
*GARWASHI*
*NE*

_NA NANA DISO_

http://nanadisoo.blogspot.com

© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Yanayin da queen najlat ta Nunawa sark'i khaleel game da maganar da yayi Mata baiji dadi ba hak'an yasa yayi shiru har suk'a karasa masarauta....

" Fadawa ke faman kirari da marok'a har suka karasa cikin harabar fadar sarki Nan driver yafita queen najlat ta yunk'ura zata fita sarki khalel ya rik'o hannuta...

" Cikin wane irin kallo da saida jikinsa ya mutu yace nabaki izinin fita??

" Komawa tayi k'an kujera sannan tace ina jiran izini to....

" Ina dai fata queen lafiyarki kalou..

" Daga masa kai kawai tayi sannan yace yak'amata ki fuskanci ne kikuma san Agogo yana zagayawa ne akan kowace sa'a,haka rayuwa take zagayawa da mu a kan yanayi daban daban Yi hakuri idan yanayinka a yau bai yi dadi ba, watakila gobe ne za ka yi dariya...

" Wane irin murmushi tayi da baikai zuciba tace Kibiya sai an ja ta baya sannan ake harba ta,Kai ma Dan Adam wani lokaci kana bukatar ka ja da baya don cim ma bukatarka....sannan tafita daga motar anata yimata kirare....

" A hankali sarki khaleel yafito cikin fara'arsa wacce ke kunshi da damuwa fadawa suka zagayeshi...Nan aka dinga kwasar gaisuwa har ya karasa cikin fadarsa...

" Sarkin fablita sarki khaleel ya iso cikin fadarsa...

" Zama yayi Nan mutane suka dinga kawo masa korafi kalakala harda wata mata datazo tace tabarmasa 'Yarta halimatu....

" Shiru yayi sannan yace sai yayi shawara bata bar fadar nan ba sai da godiya dakuma tumin abun arzuki....

" Waziri ne yace Allah yakara maka lafiya maganar bokayen da kace akamo mun kamosu...

" Sarki khaleel ne yace su Nawa kuka kamo?

" Su 50 dana cikin kauye dana cikin birni...

" To babu damuwa zuwa gobe zamu zauna dasu...

" Daganan su kace jaaaarakin ka ya mike tsayi bai tsaya ko'ina ba sai fadar ummi Nan suka gaisa...

" Ina fatan tare kuka dawo da queen najlat?

" eh tare muka dawo...

" Ina neman afuwanku komai nayishi ne abisa rashin fahimta...

" Murmushi yayi tare dajin dadin maganganun mahaifiyar tasa yace babu komai ummi ai ya huce....

" Inaso ka rarrashi queen bilkisu domin tana cikin damuwa sosai?

" damuwa kuma kamar tame???

" Rashin 'ya'ya wacce ako da yaushe yake burkita mata lissafi...

" Amma kullum ina sanar da'ita hakuri shi yakamaci ta...

" Kasan mace ita lallabawa take bukata wannan fadan zai kara harzukata ne!

" Shiru yayi sannan yace badamuwa...

Fatuwa ki zageyi acikin fadarta wannan bani bala'ine jakadiya an kama bokan mu fa???

To ranki yadade yakikeso nayi? Ko prison din ba'a shiga ballantana musan abunyi....

" Dole kisamo mafita domin sarki yace ratayesu zaayi in yatona asiri kinsan korata zaayi acikin masarautar nan...

SO GARWASHE NETempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang