63-70

740 30 4
                                    

_63-70_

*SO*
*GARWASHI*
*NE*

_NA NANA DISO_

http://nanadisoo.blogspot.com

© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Sarki Khaleel da rabin hankalin sa ya tashi kokarin gigicewa yayi tayi saurin daukar rigar ta bar dak'in da sauri ta shiga fadar ta itama gaba daya ta birkice....

" Sarki khaleel ne yasamu guri gefen gadon sa ya zauna cikin k'asalalliyar murya yace tabbas mutane kala uku ne..wasu kamar guba suke, gudunsu akeyi..wasu kuma kamar magani suke, akai akai ake bukatar su..wasu kuma kamar abinci ne, a kullum ake neman su saboda amfanin su, tabbas najlat tana cikin wacce kullum ya kamata a nemeta domin amfani da yawa, mace tagari ita ke gyara mijinta....

" Ruma ce tace ranki shi dade yana ga sai murmushi Kuma Sai kisha kunu lafiya? Ince lafiya?

" Ruma mamakin munafukan mutane nakeyi wallahi sai su nuna suna sonki nan sune manyan mak'inya..mutum kurum mugu ne....

" ruma ce tace kada ki damu da masu kulla miki sharri duk iya kokarinsu basu wuce zartar da kaddarar akan ka ba...

" Wannan gaskiya ne ruma kuma nagode wa Allah danasan abubuwa uku suk'an kau da bala'i;- sadaka addua da zumunci.... yau zamuyi sadaka ko ta kayace, Addua daman inayi kuma zan cigaba dayi..kuma inshaa Allahu zan tambayi sarki domin zuwa gaida mahaifina...


" Wanna maganganun naki gaskiya ne ubangiji ya yafemana ne bari naji nayi sallah ki huta lafiya....

" Alamar godiya tayi mata sannan ta huce fadar ummi inda ta tarar da da queen bilkisu acan sai hira sukeyi....

Yarima farouk k'e murmushi yayin da najlat ta shigo cikin zolaya yace queen bilkisu ta kwace miki ummin ki kullum suna tare...

" Murmushi queen najlat tayi tace ai ummi ta kowa ce ko ummi???

" Queen bilkisu ce ta taba bak'i tace wasu dai sunfi matsayi agurinta...

" Wane kallo najlat tayi mata sannan ta zauna ummi please nazo ne neman Alfarma....

" Alfarmar me 'yata??

" Ina son zuwa masarautar mu ina bukatar ganin mahaifina...

" Amma queen najlat kisan halin mutanen gidanku kada suyi miki wani abun...

" Amma ummi yakamata naji na sada zumunci da 'Yan uwa na...

" Queen bilkisu ce tace dama ne ai duk wata sai naje Amma ke sani cewa kekinyi gaba sarauniya kike agurin mutane kuma kinada arzuki dan haka ba sa'an ninki ba niba...

" Queen najlat ce tace komai dai Allah ke bayarwa ba mutum ba kuma yakan karbe Alokacin da yaso...kuma banda abinki queen ai A kan pillow Sarki yake kwana, Haka shi ma talaka, Amma babu wanda zai ji dadin bacci sai wanda yake da kwanciyar hankali....

" Tabbas gaskiya kika fada queen najlat zan kokarta yimasa magana...

" Queen najlat ce ta durkusa tayi mata godiya sannan ta huce bangaren ta...


Fatuwa ke faman sintiri tana tsaki jakadiya meke shirin faruwa ne naga sarki baisa kayan ba kuma kinsan boka yayi mana kashedi....

" Ko dai wane ya labe lokacin da muke sa maganin...

" Da abin kunya gwara mutuwa dole ne matansa su rabu dashi domin banaso kwata kwata ya haihu dasu....

" mutsaya mugani tukunna in baisa ba a sabo sabon shiri....

SO GARWASHE NEWhere stories live. Discover now