5-8

854 31 0
                                    

_5-8_

*SO*
*GARWASHI*
*NE*

_NA NANA DISO_

http://nanadisoo.blogspot.com

© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Ma sarautar binjim babba ma sarauta ce data shafi shekaru masu dimbin tahiri, ma sarauta ce mai tsattsauran ra'ayi ta banbanta da ma sarautu da dama, ako da yaushe wannan masarauta su sukeyin Nasara agurin yak'i, ta hada masu ilimi hikima da kuma arzuki sun kasance masu kishin kasar su gomno nin garin da shugaban ni suna bada tasu gudun mawa sosai.

Sarki Abdallah shine mahaifi Ga sarki salim wanda awannan zamani shi yak'e k'an mulkin. Sarki Abdallah babban mutum ne da yagaje sarauta agurin k'akan ninsa, Alok'aci mulkin sa ya gudanar da zalunci kalakala amma kuma mutum ne mai kishin alummar sa, tun daga zamanin sa anyi asiri da kuma jefan mutane, wanda ya nuna hak'an bakomai bani, ayayin da yasha cuta mai tsanani hak'an yasa har ajalin sa yazo, awannan lokaci da ya mutu babban dansa shine salim daga nan kuma yafara Nashi mulkin..

Sarki Salim mutum ne mai aqida daban tunda ya hau k'an kujerar mulki shikenan abubuwa da dama suk'a chanja hak'an ya haifar da gyara acikin masarautar dama kasar baki daya, ya gudanar da yak'i kala kala hakan yasa wane sa'in suyi nasara wani sa'in kuma acinye su, yanada shekara 40 akwai kanwar sa dak'e gurin sa kuma ita d'aya suke iyaye daya, Akwai wata shekara da sarki suleiman yazo da yak'i A lok'acin Shikuma yanason k'anwar tasa maryama to sai akace ayi gasa indai sarki suleiman yace mulki to za'a aura masa maryama kanwar sarki salim indai kuma sarki salim yaci wannan yak'in to sarki suleiman zai bashi bayi guda 100, daga karshe dai sarki suleiman yayi nasara aka aura masa maryama tatafi masarautar fablita.

Sarki salim Yana da Mata guda 3 sai kwarkwarori, gidan sarautar ne da'akeji da mulki da kuma kudi, matarsa ta farko itace Sarauniya hafsa itace mai fada aji acikin masarautar shekarar ta 43, masifaffiya ce duk wane harkar asiri tasani, duk wasu amare da zasu shigo gidan sarautar kadan ne basa mutuwa saboda asirin ta,tanada yara biyu kadai, babban d'anta shine auwal shine wanda ake kira yarima yarone dan shekara 27 amma yalallace gurin neman mata, sai Na biyu yahya wanda yake da shekara 20 harkar shayi shaye ci agaban sa, sai autar ta sadiya shekarar ta 15 amma girman kai da wulakanta mutane sune agabanta..

Matar sarki salim ta biyu itace sarauniya Atika macece mai mutunci kirki da kuma gaskiya asalin mahaifin ta dan boko ne ita k'anta phd ne da'ita, tunda ta shigo gidan nan abubuwa dayawa suka chanja hatta ma'amalar sarki, sarki salim yana mutuk'ar sonta domin duk tafiyar da zaiyi to da'itace, daga wannan lok'acin suk'a fara artabu da sarauniya hafsa, farkon asirin datayi Mata shine ak'an ta haukaci aranar sarauniya hafsa da k'anta ta barbada mata magani akofar dak'inta, batasan awannan lokacin ma karatun kur'ani take tayi kuma lok'acin fitarta da bismillah tafita kuma da karatun qur'ani a bak'inta, hak'an yasa sarauniya hafsa acik'in wane hali...

Tun daga lokacin tafara yimata sharri kala kala tun sarki baya dauka har wata rana ya shigo mata dak'i rai abace sanadiyar wai sarauniya atika ta zuba masa guba a abinci, lokacin da yak'eyi mata fad'a bataci komai ba sai lok'acin da yagama tace ko bana sonka bazan kashe ka ba ballantana kaine rayuwa ta kaine kuma farin ciki na kai ba azzalumi bani ba kuma kanason talaka wanka kaga idan nakashe ka ribar me zanci? Cikin fada yace wato wannan tugun hafsa ne? Murmushi tayi addua zakayi musu da'ita da yaranta Allahu ya shiryasu Amma ni bantaba shirka ba kuma bazanyi ba rungumeshi tayi tace kaine farin cikina, Allah ya karama ka lafiya, sai kuma tasa kuka alok'acin ya gigice goge mata hawayen ta yayi sannan yace lallai nasan akan haihuwa kike kuka kuma Allah zai baki, " Murmushi tayi tace inaso inga nima mai yimin addua idan namutu, inson yarinya mai halina mai kuma kawaicin babanta, " kada kidamu zaki haifi ta inshaa Allahu bari Natafi fada, " mik'ewa tayi ta bude frige dinta ta dakko madara, cikin shagwaba tace bana sonk'a da yunwa bana sonka da damuwa mijina kasha kowannan ne, " Dariya yayi yace kina faranta min Atika Allah kema yayi miki ina kuma sonki da kaunarki..

SO GARWASHE NEWhere stories live. Discover now