_100-105_
*SO*
*GARWASHI*
*NE*_NA NANA DISO_
http://deejarhberver.wordpress.com
© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
Masarautar fablita kullum sai cigaba takeyi yadda garin gaba daya ya sauya ga makarantu da sarki khalil ya giggina, cikin huk'uncin Allah kowanne matasa sunada aikin yi ga albarka cin gona, rayuwar sarki khallil sai kara baya takeyi kullum bashi da addua sama da godiya da Allah yauma yayi tafiya zuwa wata masarauta basu dadi dadawo wa ba.....
" Queen najlat ke fama da dawainiyar cik'inta duk da dai queen bilkisu ita ta karbe prince imran amma nauyin jikinta takeji yau tashirya kayan ta tsaf domin zuwa masarautar bimjim tana kokarin saka riga sai ga sarki khalil...
" Tun dazu nake jiranki acikin fadata shiru baki zoba?
" cikin yanayi irin na cuta tace to ni mai zan maka??
" Kinfi kowa sanin abunda nake bukata ai...ina prince imran din?
" Ai kasan inda yake! Daman inason tambayar ka zanje gida nayi kwana biyu....
" wai najlat meke damunki kwana biyu sai wata rigima kikeyi fa!...
"Rigima kuma daga na tambayi ka zanje naga mahaifina shine zakaci nafiye rigima aa kamanta jaririya ce ni....
" Badai sokikeyi kije ba to babu inda zakije babu kuma mai kaiki....
" cillar da wayar hannunta tayi sannan ta kwanta abakin gadonta can kuma ta dan rik'i ciki....
" Har cikin zuciyarsa sai dayaji badadi amma bazai iya barinta taje ba saboda cikinta ya tsufa..Yadda yaga take zubda hawaye yasa yace kiyi hakuri in kika haihu sai muji tare kafin nan ma prince ya kara girma....
" Wayasan gobe??? Ai sai Allah, ni yau nakeson zuwa inkuma ka kafi akan bazanjiba nagode sai ka fitarmin a daki...
" Murmushi yayi yabar mata gurin acikin ransa yace dan kinbata min yanzu najlat bazanje komai ba don kin faranta min yafi a kirga...
" queen bilkisu ce ke bawa prince imran abinci yanata dariya...sarki khalik yana zuwa yafara daga hannu...
" sarki khalil ne ya zauna kusa dasu sannan yace mum imran abinci kike basa??
Eh naga yanason kunnun ne shine nake basa da kaina....
" Kina kula dashi bilkisu banda bakin yimiki godiya kin daukeshi kamar ke kika haifeshi dubi yadda kuke cikin raha ku shirya anjima zamu dan zaga...
" Murmushi tayi ta rungume imran tace aini Allah kadai yasan irin soyayya da nakeyiwa sarkin mu nagama jira nakeyi queen najlat tace ta barmin shi.....
" Ai an barmiki gashi yau yafi 3mouth hannun ki...
" Bataci komai ba ta dauke imran ta canja masa kayan jikinsa cikin shagwaba tace kagayawa najlat zaa fita kaga takara jindadin jikinta....
" A'a bansanar da'ita ba Amma ku shirya bari naje nasanar da'ita....
Ruma ke faman lallashin najlat tace Abinci Amma taki...
" Ruma kifita adak'in nan babu abincin da zanci naga cikina ne me ruwanki....
" haba ranke shi dade kodan lafiyar abunda ke cikinki ai kyaci....
" wane dogon tsaki ta buga tace kyatayi...
" Sarki khalil ne yace fita ruma bari naganta...
" To ranka ya dade Allah yakara tsahon rai...
YOU ARE READING
SO GARWASHE NE
RomanceLittafi ne dake magana akan soyayya da illarta, wulakanta mutane da kuma tozarta tasu , nuna isa da girman kai..da kuma illar tsafi da shaye shaye...Littafine dake nuna cewa shi so gamuwar jini ne, kaunata da soyayya gaskiya ce sai dai bakowa ake zu...