105-110

945 31 0
                                    

_105-110_

*SO*
*GARWASHI*
*NE*

_NA NANA DISO_

http://deejarhberver.wordpress.com

© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Hank'alin kowa yatashi hatta su ummi sun kasa zama sai sintiri sukeyi..

Bayan Awa uku likitoci suka fito dak'in duk cikinsu babu wanda yayi magana sai da babban likita yafito, A han zarci sarki khalil ya tashi likita...

" baby girl aka miko masa cikin murna ya karba tare dayi mata addu'oi cikin sanyin murya yace zan'iya ganin mamanta....

" Dariya likita yayi sannan yace tana cikin koshin lafiya, kuma anyi aiki lafiya ku dan bata awa daya tukunna...

" su ummi ne suka dinga barka barka Allah yakara lafiya wanga yarinya da uwata take kama....

" Murmushi sarki khalil yayi sannan yayi sujjada domin godiya da Allah sannan ya huce zuwa masallaci...


Queen bilkisu ce dauke zaune akan gadon ta takaicin duniya ya'isheta cikin zuciyar ta tace mai yasa sarki khalil yafi son najlat? Dubu yadda ya gigice yafita hankalin sa akanta! Wane guntum hawaye ne ya fito a cikin idonta sannan tace tabbas najlat tafine iya soyayya da kuma kissa nima zan kokarta gurin daukar irin dabiun ta masu kyau, bata nufi ko ina ba sai fadar fatuwa nan ta sanar dasu cewa queen najlata ta haihu 'yamace murna suka hau yi sannan aka dauke hanya sai asubuti....

" Yadda asubutin ya cika da 'yan uwa yasa sarki khalil kunyar shigewa amma haka fadawa suka shige masa gaba har ya shiga dak'in da aka kwantar da queen najlat yana tura kofa yaganta a k'wance sai kayi tunanin ta mutu cikin sauri ya tsugun na agabatan yace masoyi yata bude idonki ko naji dadi...

Alamar motse tayi da hannun ta sannan ta bude duk tayi wane iri, cikin tausayawa yace sannu ubangiji Allah shi kadai zai iya biyanku, kuma inshaaAllah ke 'yar aljanna ce, Allah ubangiji yayi miki Albarka...

" A hankali ya rike hannun ta alokacin ta kalle idonsa tace Ameen..

Najlat gimbiyar mata,soyayya mai dadi baza tafi tamu ba,wallahi najlat kina burgeni,a duniya kice farin cikina, inna rasa ki wazata bani gata? Idan nazauna ni ke nake tunani a zuciyata ina sonki, Nifa sonki biyayya kadai nake miki Ni banda burin da inbaki komai nawa,duk d'ana na halak bazaici amana ba...

" murmushi tayi tace Na godiwa Allah da yasa naga wannan rana kuma nagodewa Allah daya bani namiji tamkar uwa da uba, kuma na godewa da yabani nagari mai kula dani ko da so ko babu, Allah yasaka maka da Alheri...

" Kin canci hakane Queen mekikeso kici yanzu likita yace zaki iya cin komai yanzu...

" cikina da zafi fa har yanzu cewar najlat...

" sarki khalil ne yace zai daina ahankali sannu bari naje na dakko miki kayanki...

" Daga k'anta tayi sosai har ya kai kofa fadawa suna biye dashi nurse ce tace DanAllah yallabai ko zan iya magana dakai??

" fadawa ne zasu daka mata tsawa sai cewa yayi ku dakata inajinki...

" Wallahi kacika mutumin kirki gaka sarki Amma kana kula da matarka babu girman kai babu tak'ama...

" Murmushi yayu yace su Amana ne Agaremu kuma Allah zai tambayi mu kamar yadda zai tambayi mu abisa milkin da mukeyi, Duk d'a Na halak ba zaici Amana ba, Duk mai gulma ba zai huce jin kunya ba, Mai nazari aikinsa bazai kwabe ba...

" Murmushi tayi tace tabbas hakane nagode Allah yaja kwana...

" Fita yayi fadawa suna tafi dashi har cikin mota...

SO GARWASHE NEWhere stories live. Discover now