70-75

610 22 16
                                    

_70-75_

*SO*
*GARWASHI*
*NE*

_NA NANA DISO_

http://nanadisoo.blogspot.com

© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Yadda queen Najlat ta wadi yayi masifar tsoratar da kowa fadawa ne sukayi k'an sarki khalil dauk'ar sa su kayi suka tafi dashi dak'in da likita yake dubasa cikin sauri irin nasu na ma aik'ata tuni ko'ina aka sanar bashida lafiya cikin mintuna ciroma yakirawo likitoci...

" Najlat kuwa wasu bayine suk'ayi cikin dak'i da'ita wanda ruma ta bukaci atafi asubuti da'ita Amma aka hana hankalin ruma bai tashi ba sai da taga babu wanda ya lura da halin da gimbiyar tak'e ciki Nan ta dauk'i waya cikin kuka tace mumy mumy queen najlat zata mutu...

" What wrong kuma? In cutar ce ta tashi ki duba zakiga allurar ta kiyi mata...

" Cik'in k'idime wa tayi mata nan kuma taji tayi shiru, Cikin yanayi nadamuwa ta nufi fadar sarki mutane suka cika daga can gefe ta hango ummi tare da queen bilkisu sai kuka takeyi karasawa tayi ta tsugunna tace ranki shi dade queen najlat tana cikin matsala fa??

" Ummi ce ta k'ifa mata mari ta kara kifa mata mari cikin bala'i tace bataga matsala ba saima sarki bai tashi ba tsinanniyar yarinya tasamin d'a agaba tana kokarin kashe shi nan tak'e ummi tasaka kuka...

" Ummi wallahi que...

" fatuwa ce tace zak'i fita ko saina sa an koreki a aiki?

" Sauri tayi tabar gurin idanuwan ta dauke da hawaye....

" Fatuwa tacewa ummi tabbas najlat ta nuna miki karshen kiyayya domin ta k'yamaci danki ina baki shawara adauki hukunci mai girma ak'anta...

" cikin kissa queen bilkisu tace inason mijina danAllah kada ta kashemin shi ummi please...

" Yi hakuri 'yar kirki nasan hukuncin abunda zan dauk'a..

Ruma dake faman kallon queen najlat Har ta Bude idonta da ya canja kala cikin muryar tausayi tace ina sarki khalil?

" Ita Dai ruma tausayinta ne ya kamata batace komai ba tace yajikin?

" Ruma sarki khalil ta fashe da kuka ta mik'i zata fita..

" kada kifita queen akwai matsala! Maganar queen najlat taji Kamar daga Sama ta dawo jingina tayi k'an kujerar ta tana fidda hawaye cikin sautin kuka tace Allah kajikan mahaifiyata sannan takara saka kuka...

" Ruma da tausayin queen najlat ya cikata itama sai kuka, dataga queen najlat kukan takeyi sosai sai cewa tayi ki daina kukan nan queen Allah Yana tare dake...

" Ruma karnayi kuka??? To inbanyi kuka ba ya kikeso zuciyata ta kasance?

" Hakuri zak'i Yi komai zai huce tabbas tsantsar kaunarki tananan atare da sarki khalil idan bakiso mijinki ba wazaki so queen??

" abokin kuka shi ake gayawa mutuwa kinsan irin rayuwar danayi abaya kinsan Kuwa ya khalil da bakinsa yace ya tsanine to ina amfanin tuwo ba miya?? Sannan ta saka matsanan cin kuka yagayamin maganganu a idon mutane wannan cutar danaki Fama dashi shine sila!!! Kuma ni har me nayi masa takara saka kuka....

" Goge hawayenta taYi tace queen kitsaya ki nutsu kikuma tuna ita rayuwa Bata tafiya dole sai da jarabawa fa,mata nawa ke son mijin aure?? Mata nawa ke hakuri da mazajen su? Mata nawa ke cikin KUNCIN RAYUWA? Tabbas so garwashi ne Amma kuma baya kona masoyan farko wane abun kanayi ne Dan makiyan ka wane kuma kanayi ne Dan amfanar k'anka idan baki gyara ba igiyar aurenki tana rawa...

" A tsorace ta dago manyan idanunta tace what?

" Tabbas ummi tace sai ya rabu dake su futuwa sunata angazata dan haka yarage ga naki!!!

SO GARWASHE NEWhere stories live. Discover now