CHAPTER ONE

574 30 6
                                    




Note: Wannan labarin kirkirarre neh, idan yazo kusa da labarin ki/ka toh akasi aka samu! I all hope you'll enjoy it!!!!!!!!

Gida neh d'an k'arami ba plaster balle painti sai kace kulki, wata yarinya ce kyakkyawa fara kal tasha kitso kalaba k'anana wanda yasha adon ribbons kala-kala, ak'alla bazata wuce shekaru takwas ba take wani irin kuka tana bubbuga kafanta, ga abinci taliya yasha had'i a zube a k'asa, wata matace fara kal tafito a wani k'aramin d'aki hankalin ta tashe tazo ta d'auke yarinyan tace
"Ayshe!!! Mesa kike kuka?"
Cikin shagwab'a wanda ta kira da Ayshe tace
"Amma Indomie nakeso ba taliya ba"
"Toh me bambancin naga duk taliya taliya neh"
Tura bakin ta tayi tana kuka tace
"Ba d'aya baneh Amma ni Indomie nakeso idan ba haka ba bazan je school d'in ba"
"Yi hak'uri Habibty, bari yanzu zanje na siyo miki indomie d'in nasaka miki a foodflakes but kici taliyan idan yaso sai ki tafi da Indomie d'in makaranta"
Da k'yar Aishe ta yarda Amma ta share wajen ta zuba mata wani taliyan a plate ta shige d'aki, cikin d'akin ni Nana na tsaya kallo, k'asan daga siminti sai siminti koh carpet babu balle akai ga tiles. D'aga katifan ta wanda yaji jiki tayi ta d'au wani rub'emmen naira d'ari wanda sai ka sa ido zaka san d'ari neh. D'auko wani hijabin ta tayi wanda yaji jiki ta saka ta same Aishe wanda tana cin taliyan hankali kwance tace
"Bara naje na siyo Indomie kinji Habibty"
D'aga kai tayi kawai ba tare data amsa ba, fita tayi ta siyo Indomie medium size naira tamanin aka bata canjin ishirin ta dawo gida. Tana zuwa ta kunna mukubur ta dafa mata Indomie ta zuba mata a foodflakes. A lokacin har Aishe ta saka uniform na makarantan ta tayi kyau abunta kamar ka sace ta ka gudu.
"Yawwa Habibty kinyi kyau abun ki"
Murmushi tayi wanda ya k'ara fid da asalin kyaun ta da dimples nata suka fito. Wani mutum neh ya shigo cikin gidan da sallama wanda a shekaru bazai haura arba'in ba, wankan tarwad'a neh amma kallo d'aya zaka masa kasan kyakkyawan namiji neh.
"Abba kud'in makaranta"
Wanda ta kira da Abba yayi murmushi yace
"Haba Mamana kamata yayi ki fara gaishe ni kan kiyi maganan kud'in makaranta"
Turo bakin ta tayi tana kallon sa, zuwa yayi kusa da ita yace
"Ba an zuba miki abinci a kula ba?"
Ta d'aga kanta, yace "Yawwa sai a zuba miki ruwa a gora idan kinci abincin ki kisha ruwa kinji Mamana, dan nima yau na tashi banda kud'i"

Wani kallo Amma ta watsa masa tace
"Haba Mallam! Haba! Wannan wace irin magana ce? Yarinya zataje makaranta amma ace koh sisi bazaka bata ba? Bayan kud'in makarantan ta ni nake biya"
"Wannan ke kika sa kanki, ba nace zan kaita makarantan government ba, kika nace sai private ni kuma gaskia banda kud'in da zan kaita private dan kaf sauran 'ya'yana a government school suke"
Dogon tsaki taja tace "Ka daina had'a 'yata da sauran 'ya'yanka Mallam, kuma ma nawa zaka bata? Ya wuce naira hamsin zuwa d'ari? Kasan nawa nake biya mata kud'in makarantan da take zuwa? Dubu ashirin da biyu koh wani term"
"Wannan ke kika sa kanki bani na saki ba". Yayi shigewar sa d'aki ya barta tsaya. Wani uban tsaki taja tace
"Habibty ga naira ashirin kiyi managi kinji"
Zumbura bakin ta tayi tace
"Amma wannan fa koh chocolate bazai siya mini ba"
"Kiyi hak'uri anjima zanje wajen Kawo Yasir nasan zan samu abu a gunsa"
Haka da k'yar ta lallashe Aishe ta zura hijabin ta takai ta makaranta....

COMING YOUR WAY SOOON

DUNIYA~Ina Zaki Damu!!!!Where stories live. Discover now