CHAPTER SIX

273 24 0
                                    


    Washegari da asuba tana bacci taji kamar kukan Hashim a mafarki, nan take ta farka ta fita a d'akin. Ganin Ammah tayi rik'e da Hashim sai k'okarin kwara amai yake yi, ga Yaya Kashim, Yaya Faisal da Yaya Ibrahim duk sun saka shi a gaba suna masa sannu. Ganin Jannah da Hashim yayi ya k'ara rik'e cikin sa yana forcing amai na dole, nuna ta da yatsa yayi ya fashe da kukan shagwab'a, duk juyawa sukayi suna kallon Jannah. Ammah ce tace
"Lafiya Hashim meye Jannah ta maka?" Dan yanzu Ammah ba laifi tana d'an shiri da Faysal da Ibrahim banda Kashim da mamar su, cikin kuka yace
"Ammah jiya da daddare Anty Jannah ta shigo da ice cream da kaza gashashshiya ta bani na shigar mata d'akin ta da gudu kar Yaya Kashim ya gani,  daga baya dana rok'e ta taki tabani shineh nace mata zan fad'a wa Yaya Kashim idan bata bani ba, shineh ta bani tace wai da daddare sai ciki nah yayi ciwo na kasa bacci gashi yanzu ciki na yana ciwo"
Faisal da Ibrahim neh suka fashe da dariya, Yaya Kashim kuma kallon ta yake, Jannah kuma tayi soro soro da ido, shafa kan Hashim Ammah tayi tace
"So sorry ka bari zanyi maganin ta ita ba mugunta ba, ai na fita mugunta". Shi kuwa Hashim sai wani lab'ewa yake a jikin Ammah shi a dole bashida lafiya, Jannah kuma juyawa tayi ta shiga toilet dan tasan Hashim zai iya aikata abun da yafi haka ma.....

Bayan ta fito a toilet tayi alwala tayi sallah'n Subh ta k'ara komawa bacci ita bata farka ba sai kusan k'arfe goma sha d'aya.
  Fita tayi a d'akin ta dan tayi wanka ta fita, ganin Yaya Kashim da Mama tayi suna zaune a tsakar gida, kusa da  Mama taje ta zauna ta gaishe ta tace
  "Good morning Momma, kin tashi lafiya?
Murmushi Mama tayi tace
"Lafiya kalau Jannah"
"Mama nikam me kuka dafa neh?"
Wani harara Kashim ya mata yace
"Wato ke bazaki tashi ki dafa ba sai dai a dafa miki koh kina zaman 'ya mace? Maza ki tashi ki bar nan wajen"
Turo bakin ta tayi tace "Shikenan baza'a bar mutum ya huta anan gidan ba kenan"
Mama ce tayi murmushi tace "Habibty dankalin hausawa aka soya maza kiyi wanka kici kinji"
"Toh Mama". Kashim had'a rai yayi yace
"Mama nikam meye sa kuke son b'ata yarinyan nan neh eh? Abun da kuke yi sam bai dace ba"
Kwala wa Jannah kira yayi a lokacin da take k'okarin shiga toilet, ajiye bucket d'in wankan ta tayi tazo tana yak'une fuska tace
"Gani"
B'ata rai yayi yace "Yanzu mesa baki zuwa islamiya?"
  Turo bakin ta tayi tace "Haba Yaya Kashim da girma na da shekaru nah aga ina saka uniform ina zuwa islamiya haba ai wallahi aji down neh"
Ji tayi ya buge bakin ta da k'arfe har sanda jini ya d'an fito, Mama ce ta taso ta rungume Jannah ran ta b'ace ta nuna sa da yatsa tace
"Nan gaba idan zaka mata fad'a kayi but ban yarda ka aza hannun ka a jikin ta ba"
"Haba Mama kiga yarinyan nan kwata kwata shekarun ta nawa yake har zata iya bud'e baki tace tayi girma taje islamiya, bayan ina ganin wanda suka haife ta ma suna zuwa, wallahi Allah ku daina d'aure wa yarinyan nan gindi" Yana gama fad'a yayi ficewar sa. Kuka Jannah ta fashe dashi Mama kuma ta rungume ta tace
"Yi hak'uri Jannah ki daina kuka, idan banda ke Ilimin boko ma ba'a girma masa balle ilimin muhammadiyya, sam haka bai dace ba. Yanzu zan nemo miki Islamiyan da basu saka uniform idan ma uniform d'in neh baki so ki saka kinji"
D'aga kanta tayi alaman "toh"
Ammah ce ta fito a d'akin ta ganin Jannah rungume da Mama tana kuka yasa ta had'a rai tace
"Ke Jannah zo nan"
A sanyaye ta tashi tabi Ammah cikin d'aki, rungume Ammah tayi tana shiga d'akin tace
"Ammah nah I missed you tun jiya da zan fita birthday'n Zee-Zee  sai d'azu kuma da Hashim yake min sharri, Ammah na tunda kika haifo Hashim kin rage so na. na shigo d'akin ki da daddare ma na tarar kina bacci,  Ina kwana Ammah nah"
  Murmushi Ammah tayi tace
"Lafiya kalau Habibty"
"Washh Ammah koh breakfast banci ba bara nayi wanka naci sai nazo"
"A'a tsaya kiji, ni bana hanaki lik'ewa matan nan ba?"
Murmushi Jannah tayi tace "Ammah toh ai ita bata hana yaranta zuwa wajen ki ba, kiga fa kaf yadda kuke da yaranta idan banda Kashim amma sai kice ni kar naje wajen ta?"
"Toh ai yaran sam ba halin ta suka biyo ba sai wannan Kashim d'in nan"
Murmushi Jannah tayi tace
"Shin meye sa baki k'aunar ta Ammah?"
Kamo hannun Jannah tayi tace
"Aishe ai kishiya ba abun so baneh, karki kuskura a rayuwar ki so kishiyar ki, kishiya ba abun yarda bane. Kuma namiji ba d'an goyo baneh, kar kiga wai mijin ki yana sonki kiyi tunanin bazai auro miki wata ba, inaa sam. Karki yarda a rayuwar ki ki d'au namiji uba,  idan kika d'au namiji uba toh zaki mutu marainiya. Karki kuskura kice zaki wa namiji so na hauka, idan har zaki sallama wa namiji zuciyar ki toh tabbas hawan jini shi zaiyi ajalin ki. Namiji ba d'an goyo baneh Jannah,  idan har zaki goye sa toh ki goye sa da kitse idan kitsen ya narke ya fad'a k'asa dammm. Idan zaki aure namiji toh ki aure sa dan dukiyan sa, dan a duniyan yanzu ba'a soyayyar gaskia. Namiji ba wanda zaki masa soyayyar gaskia baneh, uban ki soyayyar gaskia na masa, amma bayan auren mu da wata uku ya k'ara aure, ya rasa wanda zai aura sai 'yar uwar shi kuma aminiyata"
Jannah toshe bakin Ammah tayi da hannun ta tace
"Ammah ni yunwa nake ji kuma fita zanyi please sai na dawo dan nasan surutun ki ba mai k'arewa yanzu baneh"
Rungume Ammah tayi tace "Lemme bath Mother" Ta fice a d'akin.

DUNIYA~Ina Zaki Damu!!!!Where stories live. Discover now