CHAPTER TWELVE

117 8 0
                                    



Washegari da safe Jannah tun asuba da ta koma bacci bata farka ba sai k'arfe goma sha d'aya. Da wani irin matsanancin ciwon kai ta tashi, d'an guntun tsaki taja ta d'au toothpaste da toothbrush nata ta fita a d'akin. Brush tayi bayan nan ta shiga d'akin Ammah, Ammah zaune take a gaban laptop tana kallon dad'in kowa wanda tana jinsu jiya ita da Ibrahim akan ya tura mata na satin nan, dan shima yana bin series d'in yana zuwa a tura masa. Dan  basu da satellite daga tv sai tv, d'an guntun tsaki taja tace
"Ni Ammah wai dad'in kowan nan har wani dad'i yake dashi koh wani sati sai an tura miki?"
Dariya Ammah tayi tace "Toh koh ba dad'i akan zama shuru gwara nagani"
"Umm nidai idan school ya zama serious zan karb'a laptop na"
Bud'e baki Ammah tayi tace "Na zata ai kin bar min"
"Tab, wani dalili zan bar miki? Ni kuma sai nayi amfani da meye?"
"Toh shi Zayd meye amfanin sa ba sai kisa ya sake siyo miki wata ba"
"Haba Ammah, kinsan kud'in lapton d'in nan kuwa? Zai kai d'ari da hamsin fa?"
Zare idanuwan ta tayi tace "Kina nufin dubu d'ari da hamsin?"
D'aga mata kai tayi, d'an guntun tsaki taja tace
  "Sai mei?, Nan gidan Baana 'yar ta saurayin ta yana mata kyautan dubu d'ari biyar, yarinyan da ba kyau ta fiki ba ba komai ba. Ni dan Allah ki rabu da matsiyacin yaron nan"
"Ammah kin fara koh?"
A tsawace Ammah tace "Eh d'in, ke gaki so ya rufa miki ido. Nan nace miki Baana zata rakani wajen Malamin da ta kai 'yarta dan kema kina samun manya manyan masu kud'i amma kin ki. Kwata kwata bakiso ana fad'an aibun Zayd, ko magani ya miki sai Allah"
Jannah bata san lokacin da ta fita a d'akin ba tana mai jin zafin maganganun Ammah, a wani dalili zata kaini wajen Malami sabida masu kud'i su so ni? Duk kyawu na, a yau idan naga daman fita da attajirai zan fita dasu ba har sai an kaini wajen Malami ba. Duk wannan maganan da take a zuci take yi, shiga kitchen tayi dan ta samu ma cikin ta abun da zata ci, bud'e wata kod'ad'iyar foodflask tayi take taja wani dogon tsaki ganin d'an wake. A rayuwar ta bata k'aunar d'an wake koh kad'an. Shiga d'akin ta tayi ta dau gyalen ta ta fita wajen mai shayin dake gefen gidan su. Kwai ta siya da indomie ta dawo gida ta dafa. Bayan ta zuba a plate ta shiga d'aki Wayan ta dake kan drawer'n ta ta d'auka, kunna wayan tayi daidai lokacin ta fara cin abincin ta. Messages ta gani kusan guda goma sha uku, farko na Zayd ta bud'e wanda yake kamar haka "Good Morning The LOML, i miss you so much. Please do call me when you see this"
D'an gutun tsaki taja taje kan message na Amat wanda yake kamar haka "Jannah I've been calling yoh but your line is off, wanted to know yaushe zamuyi registration namu?". Nan take Jannah ta latsa wa number'n ta kira, bugu d'aya Amat ta d'auka tace
" 'Yar air kinsan tun k'arfe nawa nake trying number ki? Why did you even switch off your phone?"
Ajiyan zuciya ta sauke tace "Amat wallahi zanyi bacci jiya na kashe sabida bana so a dameni, yau kuma i woke up late"
Guntun tsaki Amat taja tace "Yanzu kina ina? Ki shirya mushiga muyi registration"
"Hmm wallahi Amat Dad bai bani kud'i tukun na ba, bashida shi yace sai ya samu"
"Allah sarki... Toh meye amfanin Zayd ki kirasa mana ba sai koh shi ya taimaka ba"
"Amat I can't ask him wallahi, tunda nake dashi ban tab'a tambayan sa wani abu ba, sai dai idan shi ya bani toh ina karb'a"
Dogon tsaki Amat taja tace "Toh meye sa bakya tambaya?"
"Wallahi ina jin nauyin sa"
A tsawace Amat tace "Bakida hankali Jannah, ni da nake miki kallon big girl?"
Dariya Jannah tayi tace "Ina iya tambayan sauran samari na sabida bana son su and bana jin kunyan su,  amma kinga Zayd ina son sa, ina kunyan sa kuma inajin nauyin sa"
"Banza, wawiya kee sai anjima kin ma bani haushi wallahi" Amat ta katse wayan.
  D'an dariya tayi nan take taga call na Zayd wanda tun wayan su da Amat take ganin yana kiran ta, take tayi receiving, yana jin tana cewa Hello ya fara masifa a waya "Ke da waye kike waya tun d'azu call waiting d'in? Kinga message d'ina amma baza ki iya kirana ba?"
A tsawace tace "Ka gani koh? Matsala ta da kai Zargi, idan ina waya sai ka d'auka da wani gardi nake waya, idan kuma ban d'auka ba sai ka d'auka ina tare da wani". Ganin ranta ya b'aci yace "Soory SoulMate, kinsan ina bala'in son ki, dole nayi mugun kishin ki"
D'an guntun tsaki taja tace "A hakan sai kace kishi na yayi yawa, sau nawa nake kiran ka call waiting amma ban tab'a zargin ka ba? Sau nawa?

   *Ramadhan Mubarak In Advance*

See you all after sallah

*Dan Allah kusani cikin addu'an ku, ina cikin wani yanayi*😭😭😭😭

Nana Faad

DUNIYA~Ina Zaki Damu!!!!Where stories live. Discover now