CHAPTER TEN

97 8 0
                                    




   Wani sanyi taji a lokacin da ta fad'a cikin motar, wata yarinya ce a driver seat wanda ak'alla zata kai shekaru ashirin da biyu ta juya sukayi four eyes da Jannah. Murmushi ta sakar wa Jannah haka zalika itama Jannah d'in, Zee ce tace
"Umm Yawwa Ayshe ga friend na sunan ta Amina" ta d'an juya wajen k'awar ta da ta kira da Amina tace
"Amina ga k'awata sunan ta Ayshe"
Hannu Amina ta mik'a mata tace "Nice to meet you Ayshe"
Jannah murmushi tayi tare da mik'a hannun ta itama suka gaisa tace
"Nice to meet you too"
Zee tace "Umm yanzu Ayshe sai ina kuma?"
Ajiyan zuciya ta sauk'e tace
"Wallahi kinga ba abunda nayi, koh admission letter ban amsa ba"
Amina tace "Wani department neh suka baki"
"Medicine and Surgery" Jannah ta bata amsa a takaice
Amina tace "Gaskia Medicine and Surgery is either suna amsan admission letter nasu a nan cikin faculty'n wato college koh a UMTH"
"Yanzu ya zanyi? Koh zaku kaini faculty d'in na tambaya neh?"
Wani d'an k'ara Amina tayi yace
"Yes!!!! Kinyi sa'a, akwai wata cousin sis na itama ta samu MBBS, let me call her to confirm koh ta shigo sai na had'a ku"
"Okay thanks" Jannah ta fad'a tana mai jin dad'in za had'a ta da 'yar department nasu.
Nan take Amina ta d'au wayar ta cikin jaka ta latsa number'n cousin sis nata, bayan sun d'anyi magana ta katse wayan.
Tace "You're lucky itama kamar ke sai yau zata fara abubuwan ta. Yanzu haka tana gate two muje mu same ta"
"Okay" both Jannah da Zee suka had'a baki.....

A bakin gate2 na Unimaid suka samu yarinyan, cikin motan ta take wanda glass na motan tint
Amina tace "Buuu sakat! Taya akayi Amat ta shigo da mota tint cikin makarantan nan, despite the securities da suke bakin gate"
Zee tayi dariya tace "Kinsan mutumiyar ki ba wasa baneh"
"Kuma kiji 'yar iska ni take so na fita a cikin mota na same ta, mtsw"
D'aukan wayar ta tayi ta latsa number'n yarinyan, tana picking tace
" 'Yar iska ni sa'ar kice? Wato ni kike so na fita a cikin mota ta na same ki?" Ta katse wayan.
Cikin sec goma sai ga yarinyan da Amina ta kira da Amat ta fito a cikin motar ta Picanto new model. Yarinya ce doguwa chocolate colour, fuskan ta oval shape, tana da idanuwa wanda basu da girma sosai amma masu kyau, sai hancin ta daidai da bakin ta wanda ya dace da tsarin fuskan ta. Tana da kyau daidai gwargado, tafiya take kamar wanda iska zai kad'a yayi tafiya da ita har ta k'araso wajen motan. Tana zuwa ta bud'e k'ofan baya ta shige Jannah ta d'an matsa mata, Amina ta juya tana kallon ta tace
"Wato 'yar iska ni kike so na fita na same ki koh?"
Dariya tayi tace "Wallahi Ya Amina kibari kawai banjin dad'i menstrual pain na damu na shiyasa"
D'an guntun tsaki Amina taja tace
"Na samu miki coursemate"
D'an murmushi Amat tayi ta juya wajen Jannah tace
"Kece koh?"
Murmushi itama Jannah tayi had'e da mik'a mata hannu tace
"My names are Ayshe Kashim Abdulqadir, but you can call me Jannah"
Amat d'an dariya tayi tace "Amatullah Mustapha Mongono, nice to meet you"
"Nice to meet you too"
Bayan sun gaisa Amat tace "Ya zee ina kwana"
Dariya Zee tayi tace "Sai yanzu kika ganni? Ni fad'a mun taya aka barki kika shigo da mota tint cikin makarantan nan?'
Dariya sosai Amat tayi tace "Zee-Zee kema kinsan ni ba wasa bace, wani babban soja na samu ya mun tint permit kuma yazo ya had'a ni da ogan soldiers da suke bakin gate na makarantan nan"
Zee-Zee ta kad'a kai had'e da murmushi tace
"Amat kin wuce tunanin mu"
Dariya Amat tayi tace "A'a ku manya na neh"
Bayan sun d'anyi hira sai Amat tace wa Jannah "Mu tafi koh?"
"Okay toh"
Bayan sun fita a motan Amat ta juya tana kallon Jannah tace
"Nikam sojojin nan basu barki kin shigo da motan ki baneh?"
D'an murmushi Jannah tayi tace
"Umm actually I don't have a ride"
Take Amat ta juya ta k'ara kallon Jannah tace "What the fuck! How comes?"
"My parent ain't rich soooo"
Dariya sosai Amat tayi wanda ya bayyanar da hak'orin makkan ta tace "My parents ain't rich too, baki da koh da irin samari masu kud'i koh sugar dadies that can take care of your needs?"
Girgiza kanta Jannah tayi tace "I don't have any"
Sosai Amat take kallon ta, sai can ta bud'e mata mota ta shiga. Bayan sun d'anyi nesa a tafiya tace
"Nayi mamaki da kamar ki baki da samari masu kud'i, Ayshe kina da kyau Mashaa Allah, wanda basu kaiki kyau ba ma suna da manya manyan masu kud'i, taya kika yi sakaci haka?"
Murmushi Jannah tayi tace "Do those guys give you everything for free? The money, the cars, the phones and everything?"
Dariya Amat tayi tace "Ayshe nothing is free in now days era, you have to give what you have to get what you want. Baki sha'awan lukury life? Don't you want to live your life the way you plan it? Abubuwan duniya da kyalkyalan ta basu baki sha'awa?"
Nauyayyan ajiyan zuciya Jannah ta sauk'e tace
"Amat idan na ce miki basu ban sha'awa nayi miki mugun k'arya, but the problem is that I love someone so very much, I will hate to give myself to anybody idan ba shi ba"
Take Amat taja wani wawan biriki, ta fashe da wani irin dariya "Toh you're saving yourself for someone? Ummm good... How freaking rich is he? Yaron wanene a k'asar nan"
"So neh Amat, so ba ruwan shi da kud'i koh kyau. I love him for who he is, baban shi commissioner ba"
"Ummm commissioner's son ahn! Not bad. Ya sunan sa?"
Gyara zaman ta Jannah tayi tace
"Why are you asking? Any problem?"
Girgiza kanta Amat tayi tace "Not at all, I just wanna know you a lil more"
"Zayd Abdullahi Banki"
"Huhuhu, Yaron Abdullahi Bankiii..... Tohm na fita da shi kanshi Abdullahi Banki, nazo na rabu dashi naga bashida wani abun kirkin da zai tsinana mini, balle wani d'an sa.. mtsw" Take ta ja motan suka cigaba da tafiya, basu sake wani hiran da ya shafe rayuwar su ba sai na makarantan har suka kammala karb'an admission letter da clearance

Sai yamma lik'is suka gama da clearance, dan ma akwai mota zuwa TH da school d'in baya basu wahala. Bayan sun gama Amat ta kalla Jannah tace
"Ummm I am so exhausted wallahi, dan ma Allah ya so mu department namu ba yawa just mu goma sha biyar suka d'auke mu da mun ji jiki wajen layi"
Lumshe idanuwan ta Jannah tayi tace
"Wallahi kuwa, but kinsan za had'a mu da 'yan BDS ai"
"Yeah haka neh fa, but suma basu fa yawa naga they are just eleven, har mun fi su"
"Yeah hakane"
Gyara seat na motan ta Amat tayi tace
"Muje gida please, ina neh arean ku ida zan iya dropping nake toh idan bazan iya ba na rage miki hanya"
"Ina nan cikin gwange"
"Oshhh! Wallahi bazan iya ajiye ki a arean ku ba sabida gidan mu yana Hausari, but zan ajiye ki a junction naku idan yaso sai ki nema tricycle ya shigar dake"
"Don't worry ba komai, i really appreciate... Thank you"
"Haba dai ba komai, what are friends for?"

A dai-dan layin su na gwange tayi dropping nata, daga nan Jannah ta nema tricycle ya kawo ta har k'ofan gidan su.... Tana sauk'a taga wata mota a gefen gidan su anyi parking, ita duk a tunanin ta koh wani abokin Yaya Kashim neh, zata bud'e k'ofan gidan su ta shiga taji an damk'e mata gyale, juyawan da zatayi taga ZAYD............

Vote

Comment

DUNIYA~Ina Zaki Damu!!!!Where stories live. Discover now