Bayan sun gama lecture Amat tayi dropping nata a gida, tayi mata godiya. A zaure ta had'u da k'awar ta Ruky, nan take Jannah tayi hugging nata tace
"Besty nah i missed you sooo much"
Tureta Ruky tayi tace "Dallah can, bawani nan. Tunda kika samu admission medicine kika share ni sabida ni na samu course na yakubayi"
Dariya sosai Jannah tayi ta rungume ta a k'aro na biyu tace "Kiyi hak'uri wallahi ba haka baneh, and ai Microbiology is a very nice course wallahi"
Hararan ta Ruky tayi tace "Ai dole ki fad'a haka, dan ke kin samu abunda ranki yake so"
Murmushi Jannah tayi had'e da rik'o hannun ta tace "Dan Allah mu koma ciki". Girgiza kanta Ruky tayi tace
"Tun k'arfe hud'u fa ina gidan ku gaskia yanzu magrib tayi"
Jan ta ciki Jannah tayi game da cewa "Karki damu zan raka ki har gida"
Alwala sukayi suka shiga sukayi sallah, bayan sun idar Ruky tace
"Jannah bamu tab'a had'uwa a school ba fa?"
Hararan ta Jannah tayi tace "Tayaya ma zamu had'u, bayan ke kina science complex ni ina can cikin medical college"
D'an gutun tsaki Ruky taja tace "But ai part one science duk gaba d'aya neh"
Dariya sosai Jannah tayi tace "No ku da 'yan paramedics neh d'aya banda mu da 'yan BDS. And afterall ai ba'a fara lecture sosai ba, they just resumes"
"Eh fa haka neh", gyara zama tayi tazo kusa da Jannah tace
" 'yar uwa kinga friends da nayi? Big girls na k'arshe. Duk inda akaca miki big girls toh fa sun kai"
Tab'e bakin ta Jannah tayi tace "Ruky ni tunda na fara zuwa school naji komai ya fice min a ka, dan wallahi idan ka biyewa su k'arya k'aryan nan kai zaka wahala wallahi. Ni Zee-Zee ce ta had'a ni da cousin sister'n k'awar ta, yarinyan she is also a big girl ba k'arya. Tana jan mota tana saka kaya masu tsada, she told me motan ma wani neh ya bata, ni gaskia bazan biye mata ba kawai karatu na zan saka a gaba In Shaa Allah with my own sweat wata rana sai labari"
Dariya sosai Ruky tayi har tana hawaye tace "Ayshah a yadda na sanki d'in da son k'arya? Tohm Allah ya sa"
Hararan ta Jannah tayi tace "Ai Allah na shiriyan mutum a rana d'aya" Dariya sosai Ruky tayi suka cigaba da hiran su. Jin ana kiran sallah'n isha'i yasa Ruky tayi sauri tasowa gameda gyara mayafin ta tace
"Jannah kinga har isha'i tayi, gashi number na a kashe nasan yanzu Umma tana nema na. Yau zan sha masifa, that woman can nag ehn"
Jannah murmushi tayi tace "Karki damu, zan buga mata waya na sanar da ita muna tare tun da yamma"
Hararan ta Ruky tayi tace " 'Yar iska ain't you the one that said zaki rakani har gida"
Rufe bakin ta tayi tace "Opps i said that? Kiyi hak'uri dare yayi but gobe idan na tashi a school zan tsaya miki"
Ruky rolling eyes nata tayi tace "Whatever! Muje na hau napep"
Bayan tayi sallama da Ammah suka fice a gidan, tafiya suke suna hira Ruky tace "Jannah Yaya Kashim yana mun kyau, i have a very huge crush on him"
Baki bud'e Jannah take kallon Ruky tace "Uhm. Wani Yaya Kashim d'in?"
Dariya Ruky tayi tace "Kinada wani Yaya Kashim neh banda wanda na sani? Yaya Kashim na d'akin Mama, a duk lokacin da na ganshi baki san yadda nakeji ba, kibar gani nah ina da samari but wallahi inason Kashim, da a yau Yaya Kashim zaizo yace yana so nah ina tabbatar miki da cewa zan rabu da duk saurayin da nake tare dashi, my feelings for him is unexplainable"
Jannah tattaru hankalin ta tayi tana jin maganganun Ruky, tana son k'awar ta sosai, kuma tana son duk abunda k'awar ta ke so, tasan bata shiri da Yaya Kashim sabida bataji, but har a ranta tana son Yayan ta, watarana da gangan take wasu abubuwan sabida ya tanka mata. Jannah ta numfasa tace
"A gaskia Ruky kina da k'yau'n da duk wani d'a namiji zai so ki". Hararan ta Ruky tayi tace "See who is talking, na kaiki kyau?"
Girgiza kanta tayi tace "Ki bar wasa Ruky, let's be serious. Ni haske kawai nasan na fiki, but kina da kyau. Yaya Kashim bashida ra'ayin auren mace irin mu kinsan meyesa?"
Girgiza kanta Ruky tayi zuciyan ta yana mai bugawa, Jannah taciga "Sabida gani yake muna da yawo, bamujin magana. Idan har kina so Yaya Kashim ya so ki fa saidai kin canza hali Ruky. Ki zama mai yawan saka hijabi, ki daina zuwa gidan mu da yamma har kikai dare" Bugu Ruky ta kai mata tana hararan ta tace
"You're talking as if ke bakya zuwa gidan mu da daddare"
Dariya Jannah tayi tace "Ai abun da yayiki shi yayini, duk hali d'aya ai muke da ke. I am just advising you if you really wanna win his heart, so you've to prepare for it"
Wani miyau mai kaifi ta had'eye tace "Jannah i can do anything to have his attention In Shaa Allah, but how i am gonna do it Jannah? He will never notice me. Koh zan fito fili neh na fad'a masa sirrin dake raina?"
Jannah tayi murmushi tace "Gashi gobe zai kama hanyan kano,ganin sa zaiyi wuya daga gobe har zuwa wane shakara. Zan baki number'n sa, try your luck kinji? Kuma zan na miki campaign a wajen Mama"
Rungume ta Ruky tayi tace "I love you soo much Jannah"
Raba jikin ta Jannah tayi tare da hararan ta tace "Mtws.... Ke dallah muna kan titi kan wasu su fara tunanin wani abu daban"
Murmushi Ruky tayi tace "Let them Dear, i am just sooo fucking excited"
Jannah tace "Kingani koh? Another reason that he won't love you. The fucking word, you can't make a complete sentence without the F word"
Tushe bakin ta tayi da yatsun ta tace "Zan gyara In Shaa Allah"
Rolling eyes nata Jannah tayi tace "Whatever"
Sallama sukayi Ruky ta hau napep ta wuce gida, a lokacin Jannah ta tuna Zayd zaizo wajen ta gashi wayan ta babu charge ya mutu, sauri tafarayi dan tana tunanin koh yanzu yazo yana k'ofan gidan su. Tana cikin tafiya taji wani husky voice ta gefen ta yace "Assalamu Alaykum"
Manyan idanuwan ta d'aura akan saurayin da ya mata sallama, dogo neh sosai mai faffad'an k'irji, chocolate colour yana da ido daidai tsaka tsakiya wanda ya dace da fuskan shi da hanci sa dogon gaske. Murmushi yayi mata yace " 'Yan mata ina yini, dan Allah tambaya nake"
Zuciyan ta ya d'an buga ganin uniform na soja ajikin shi, tafiya take batare da ta kulashi ba dan tasan sojoji da son matan gaske. Ganin bata tsaya ba ya cigaba da bin ta yace
"Dan Allah tambaya nake, nan gwange2 neh koh 1?"
Cigaba da tafiyan ta tayi ba tareda da ta kulasa ba, a zuciyan ta cewa take idan ba rainin hankali da k'arya ba ita kad'ai ya gani a layin, ganin taki ta kulasa yace
"Wallahi zan biki har gida if you didn't answer me, na rantse da Allah"
Cak ta tsaya, ta tattaru hankalin ta gareshi tana masa wani irin kallo tace
"Mallam ni kad'ai kagani a fad'in anguwan nan da zaka tambaya, ga mutaneh dayawa why do you choose to ask me?"
D'an murmushi yayi yace "Ba haka baneh, it's just that my heart chooses to ask you. Ke kad'ai ce zuciyata ta aminta da na tambaye ki"
Murmushi tayi had'e da girgiza kanta tace "Toh Mallam ba nan baneh"
Ta juya ta cigaba da tafiyan ta, shi kansa murmushi yayi had'e da girgiza kansa ya koma. Ganin ya koma yasa tayi ajiyan zuciya tace Yaa Allah nagode, yanzu haka ma nasan 'yan sa'idawan arean nan sun fara gulma...A can gefen gidan su taga motan Zayd inda yake tsayawa kullum idan yazo, cikin takun ta na k'asaita ta tako inda yake. Bud'e motan tayi ta shiga had'e da sallama, tsadadden murmushin ta tayi masa tace "Habibi kayi hak'uri nasan kayi ta kiran number na a kashe kuma ka aika gida bana nan. I know an sanar da kai nayi rakiya"
Girgiza kansa yayi had'e da watsa mata wani mugun kallo yace "Idan kin raina wa mutanen gidan ku hankali ni baza ki raina min hankali ba Aysha, wato kin musu k'arya kinyi rakiya bayan ina shigowa layin ku nagan ki da wani akan titi, soja ma for that matter"
Idan zuciyan Jannah yayi dubu toh ya b'aci, ta rasa ganeh wani irin kishi neh da Zayd, kwantar da muryan ta tayi ta langwab'e kanta tareda kashe muryan ta tace "Wallahi Soulmate tambaya na yayi, Allah ban san shi ba, I don't know him. Allah ka yarda dani"
Ajiyan zuciya ya sauke yace "Shikenan. Nan gaba please idan wani ya tsaidake kar ki tsaya kinji? Ba darajan mace baneh a ganta a bakin titi tsaye da na miji kuma da daddare haka. Next time sai ki kiyaye, kinsan halin mutaneh da gulma da sa'ido"
A zuciyan ta cewa take kaci darajan gobe zakayi tafiya, banso mu rabu da fad'a da wallahi sai ka ganeh kuran ka na rashin yarda da ni. Cikin sanyin muryan ta tace
"Ba komai zan kiyaye In Shaa Allah".... Daga nan suka d'an tab'a hira yayi mata sallama, k'in fita tayi a motan sabida ji tayi zuciyan ta yana tsinkewa, Zayd ya saba tafiye-tafiye amma wannan tafiyan taji shi daman. Zayd yace
"Ayshah kar a neme ki a gida kinga mun jima a waje ki shiga ciki kinji" shima yana maganan jiki a sanye. Wasu guntun hawaye neh suka sauk'a akan kuncin ta tace
"Zayd I don't know why zuciya na yana tsinkewa, Zayd ina sonka. Ina matuk'ar sonka.. Dan Allah never turn your back on me no matter what"
Murmushi yayi, shi kansa yasan Jannah tana son shi, kuma ya san da cewa duk son da Jannah take masa nashi son da yake mata ya ninka nata. Muryan sa yana cracking yace
"Jannah ina sonki, ina son ki fiyeda yadda ke kike so na. I love you more than words can say. Dan Allah ki kula min da kanki kinji. I beg you take care of yourself for me"
Murmushi tayi tace "In Shaa Allah... You also should take care of yourself for me. Ance duk wanda ya shiga camp sai yayi girlfriend"
Baisan lokacin da dariya ta sub'uce masa ba yace "Shin a ganin ki har akwai wata 'ya macen da zata burge ni neh a cikin camp?"
Turu bakin ta tayi cikin shagwab'a ta d'aga kanta tace "Uhm, ai koh ba a camp ba abu zakaje kayi kayi shekara d'aya a can, nasan halin 'yan matan abuja. Su suke neman maza ma ba maza ke neman su ba. Gashi kuma a yanda ka had'un nan, ga kyau ga kud'i.. Hmm lalle ma wallahi dole masu suce suna son ka"
Dariya yayi sosai yace "Toh nikam Jannah meye zanyi da irin matan can? Karki damu Habibty ni nake neh kema tawa ce In Shaa Allah.. Yanzu ki shiga gida kinji.... I will miss you badly....."
Rufe fuskan ta tayi da dogayen yatsunan ta cikin sanyin muryan ta tace "I will miss you more"....
"Iyyehh... Yaushe kika fara jin kunya na?"
Nan take ta bud'e fuskan ta ta harare shi tace "Kaga irin ta ba? Allah kiyaye hanya"... Barin sa tayi tashige cikin gida, girgiza kansa yayi yana murmushi yaja motan sa ya tafi.......D'akin Mama ta shiga ta zauna, Mama murmushi tayi tace "Ya dai? Yau tun safe ban ganki ba. D'azu naji muryan ki dake da k'awar ki Rukayya, ai kafin ki dawo daga makaranta yarinyan nan tazo ta same ni ina shara haka ta karb'a tayi min shara tas ta wanke min kwanuka"
Murmushi Jannah tayi ta gyara zaman ta tace "Ai kuwa Ruky tanada kirki Mama" Mama ta zuba rid'i a bakin ta tace "Umm tabbas"
Matsowa kusa da Mama tayi wanda kamar zata shige jikin ta tace "Kinsan wani abu Mama?"
Girgiza kanta Mama tayi tace "A'a"
"Hmmm ai inaga kamar Yaya Kashim da Rukayya zasu dace". Kallon mamaki Mama tayi mata tace
"Kamar ya ban ganeh ba"
Sosa suman kanta tayi tace "Umm emm ina ganin kamar they will make a good couple... Gani nayi kamar idan sukayi aure zasu zauna lafiya, kinga Yaya Kashim ba ruwan sa haka ma Rukayya itama ba ruwanta.. Baiwar Allah ga hankali, ga ilimi, ga tarbiya, ga uwa uba kyau"
Mama tasowa tsaye tayi tace "Jannah banson magana shirme, kije ki kwanta dare yayi kinga kuma gobe zakije makaranta"
Jannah tasowa tayi taje kusa da Mama ta kama hannayen ta tace "Mama halan bakyason Yaya Kashim da Rukayya neh?"
Girgiza kanta tayi tace "Bawai bana son ta dashi baneh, idan ita Rukayya tana son shi ba lalle baneh shi ya so ta. Kuma kinga bazan tilasta mishi akan abinda bayaso ba"
Rungume ta Jannah tayi tace "Mama ai bance ki tilasta masa ba, kuma I didn't say you should tell him. Tunda ke kina son ta ai shikenan, yanzu it's left for Ruky tasan yadda zatayi dan jawo hankalin sa"
Murmushi Mama tayi tace "Tabbas idan hakan ya faru zanfi kowa farin ciki"
"Uhum uhum". Nan take suka juya dan ganin wanda ke gyaran muryan, sosai duk suka sha jinin jikin su ganin Kashim tsaye a bakin k'ofan......Don't forget to VOTE
COMMENT
AND SHARE
YOU ARE READING
DUNIYA~Ina Zaki Damu!!!!
غموض / إثارةNow every gurl's dream is to marry a rich Man. money! money! money!!!! is what all gurls crave for now... Duniya is a story of a young spoiled girl born in a poor family. All she ever wanted is to marry a billionaire! Find out if she's gonna end up...