CHAPTER TWO

699 47 8
                                    

  Hea guys!!!!! Hope you will enjoy it


   Wani makaranta neh mai d'an karan kyau nagani an rubuta THE LITTLE wanda ya tabbatar min da shine sunan makarantan. Makarantan yara k'anana neh daga Kg zuwa primary ba secondary. Bayan ta biya kud'in tricycle da suka sauk'a ta kama hannun Ayshe wanda koh hijabi bata saka mata ba a ganin ta yarinya k'arama ce is of no need. A bakin gate suka gaisa da wata malamar su, bayan sun gaisa ta karb'a Ayshe tana murmushi tace
  "Cutie yau kinyi late". Amma tayi murmushi tace
  "Wallahi duk laifi na neh na makara ban tashi da wuri yau ba"
  "Allah sarki ba komai".
   Kaf teachers na makarantan suna son Ayshe sosai sabida kyaun ta da ilimin ta, tunda take KG har yanzu da take primary 3 ita take dauk'an 1st position dan akwai ta da k'okari sosai. Bayan Amma ta mata bye-bye malamar ta shigar da Ayshe cikin school premises d'in Amma kuma ta juya.

   Wani gida ta shiga wanda bashida nesa da makarantan, gida neh ma daidai ci mai kyau ba laifi. Da sallama ta shiga cikin gidan, tana shiga ta cire hijabin ta tayi wulli dashi akan veranda ta shiga cikin wani d'aki. Wata mata ce dattijuwa wanda ak'alla bazata haura shekaru hamsin da biyar ba zaune a k'asan carpet tana cin biredi da kwai da shayi wanda yaji kayan had'i yayi k'auri. Zama tayi a gefen matar tare da cewa
  "Wash!!! Umma nagaji, wallahi nagaji. Yanzu nake dana sanin auren Abdulqadir, lokacin kina nuna mini hanya na rufe idonuwa na nayi kunnen uwar shegu, gashi banda bak'in cikin daya kulla min shekaru goma sha biyar da suka wuce ya auro babban k'awata sabida tsaban mugunta ga uwa uba kuma talauci, Umma wallahi yanzu nake dana sanin auren sa. Bazan tab'a barin 'yata Ayshe tasha wahala ba wai a sunan AUREN SO, Son banza son wufi, wallahi zata aura mai kud'i da tana son sa da bata sonsa, koda kuwa yana da muni kamar biri"

   Murmushi Umma tayi tace
  "Masu kud'i suna da muni neh? Sam basu dashi, kud'in ka kyaun ka ai. Kuma ma naga idan akwai kud'i komai munin mutum ba'a gani sabida kud'i ya wanke su"
  "Mts! Gaskia fa wallahi. Allah raya min Ayshe kawai Umma"
  "Ameen"
  "Umma Ayshe In Shaa Allah mai kud'i zata aura, bazata wahala yadda nasha wahala ba, bazata aura talaka ba"
  Umma tayi murmushi tace
"Tun yanzu zaki fara d'aura ta akan hanya, ki tuna mata talauci ba abun so baneh, ki cusa mata son duniya a ranta sabida gaba karki sha wahala, tun yanzu zaki fara nuna mata hanya. Allah mana tsari da talauci"
"Ameen fa Umma, Annabi ya nema tsari da talauci balle mu? Mu a nawa muke ma Umma? Ai talauci ba abun so baneh kuma Ayshe In Shaa Allah hmmm bari dai nayi shuru". Umma tayi dariya.

  Jawo ledan biredin tayi ta bud'e ta gusura kad'an, ta had'a da kwai tana ci tana kad'a kai tace
  "Umma ai gwara naci, rubuwa nah da biredi da kwai ai na manta, sai dai na siyowa Ayshe"
  Umma ta d'anyi murmushi tace
  "Sai dai kuta k'arata da koko da kusai kullum"
"Mtsw wallahi kuwa"
    Haka ta gama ci ta kwanta a wajen ba tare da tayi tunanin ta kwashe kwanukan koh wanke hannu ba. Nan da nan bacci ya d'auke ta. Ita bata tashi a baccin ba sai k'arfe d'aya da rabi, a lokacin har Ayshe almajirin Umma ya d'auko  ta a makaranta tana zaune tana cin dankalin hausawa da kwai. Murmushi tayi tazo daf kusa da Ayshe tana shafan dogon bak'in gashin ta tace
  "Habibty har kun taso"
D'aga kai tayi ba tareda ta amsa taba, tasowa Amma tayi tayi alwala tayi sallah. Bayan ta idar ta same Umma a kitchen tana tuk'a semo. Neman kujera tayi ta zauna tace
  "Umma dan Allah idan kin gama ki zuba min kinsan gidan mutumin naki baya siyo semovita sai garin masara"
   Dariya Umma tayi tace
  "Ina yaga kud'in siyan semovita idan banda ke, karki damu zan zuba miki a flask"
  "Yawwa Umma nagode wani miya kikayi?"
  "Miyar Egusi"
"Alhamdulillah, wallahi Umma kamar kinsan nagaji da cin miyar kuka, miyar kukan ma ba komai sai daddawa, koh d'an waken nan babu. Mtsw auren talaka sam baiyi ba"

   Haka nan bayan an gama abincin Umma ta zuba mata a foodflakes, shirin ta tsaf tayi harda wanka tayiwa Ayshe ma wanka, su tafi gida Ayshe ta fara kuka tace ita sam bazata gida ba. Umma tace
  "Mesa bakiso ki tafi gida Mamana?"
  Turo k'aramin bakin ta tayi tace
  "Gida ba wutan Nepa ba TV"
  Dariya Umma tayi tace
"Ayshe akwai ki da rigima, tam shikenan kiyi zaman ki anan kinji"
  Murmushi Amma tayi tace
  "Nima dai kin hutar dani" Sallama tayi da Umma ta d'au flask na abincin tayi tafiyar ta..

    Tana zuwa gida tayi shara da wanke - wanke, bayan ta gama ta hura wuta ta tuk'a tuwon masara da miyan bushashshiyar kub'ewa da babu koh daddawa bare kifi.  Bayan ta gama ta zubo su a wani old modern food flask, daga nan ta d'au abincin da Umma ta zuba ma ta zuba kad'an a plate tana ci tana santi ga nama baja baje, tace "Idan na gama ci na ajiye sauran da daddare ma na ci, idan ya rage gwara na baiwa  almajiri akan na bawa Abdulqadir. Haka ta gama ci tayi sallah'n asr ta kwanta...

    Da misalin k'arfe biyar  Mallam Abdulqadir ya shigo cikin gidan sa, kwance ya tarar da ita a sakar gida tana bacci
  "Amma! Amma!!" Nan tayi firgit ta tashi tana murza ido tace
  "Mallam lafiya kuwa ina cikin bacci nah mai dad'i zaka tashe ni?"
  "Ina kuwa lafiya? Kinzo ki kwanta a tsakar gida da yamma likis bakisan babu kyau ba, gashi kuwa namiji zai iya shigowa ya sameki haka"
  Dogon tsaki taja tace
"Kaga Mallam dan Allah banson masifa da yamman nan, ka barni naji da abunda yake damu nah dan Allah"
  Girgiza kansa yayi yace
"Allah shirye ki"
"Ameen! Allah shirye mu gaba d'aya"
 
   Shiga d'akin sa yayi ya barta a inda take kwancen, sai kusan bayan minti goma kan ta tashi ta d'auko masa abincin sa a kitchen ta kai masa d'aki, already har ya watsa ruwa a jikin sa ya saka farar jallabiya, zama yayi ya bud'e abincin tareda bismillah ya fara ci, sai can yace
  "Nikam ina Jannah? (Sunan da yake kiran Ayshe dashi dan sunan mahaifiyarsa ce) dan tunda na shigo gidan banji taba kuma yau alhamis balle nayi tunanin ta tafi islamiya"
  "Tana wajen Umma" Ta basa amsa a takaice, tura abincin yayi gefe yace
  "Kamar ya?"
"Tambaya na kake kamar ya? Kamar ya kake nufi? Tana wajen Umma nace koh baka ganeh Umma baneh?"
  "Mesa toh?"
"Yanzu shikenan 'yata bata isa ta zauna a wajen 'yan uwa nah ba, naga gidan kusa yake da makarantan su zata d'an hutar dani na kwana biyu da kud'in mota dan kai ba bani kake ba. Yanzu fisabillah mu tashi tun daga wannan k'auyen anguwar gwange zuwa old g.r.a ace bazaka iya cire kud'in mota ka bamu ba? Haba Mallam! Haba!  Wannan wace irin bak'in hali neh eh? Ai gwara da tayi zaman ta acan"
" Ai Amma ke kika raina arzikin da Allah ya bani, yanzu meye laifin Kashim? Kashim ba'a makarantan gomnati yake ba amma yana da k'okari sosai, kinsan komai sa kaine bawai lalle lalle makarantan da kake shi zaiyi determining ilimin kaba"
  "Wannan kuma k'arya kake Mallam"
"Yanzu kiga tsaban ido nah kice ina k'arya? A haka 'yarki zata tashi ta zama 'ya tagari bayan uwar ba tagari bace?"
"Kul! Karka kuskura kayiwa 'yata baki. Dama tun ba yau ba nagane kafison 'ya'yan ka na waccen matar, kuma wallahi gaba zaka sha mamaki, Ayshe da kake gani zata kaika hajj bi'iznillah, zata maka abunda sauran 'ya'yanka basu isa su maka ba, kai dai Allah kaimu gaba"
  Girgiza kansa yayi yace "Ameen! Nidai gobe kizo mini da 'yata"
Ya wanke hannun sa ya fice a gidan..

    Washegari da daddare  aka kawo Ayshe, tana zuwa taga gidan duhu ta fashe da wani irin kuka, nan take Amma ta d'auke ta tana girgiza ta tace
  "Habibty lafiya?"
"Amma duhu ba wuta"
"Yi shuru Habibty akwai lantern ai"
"Um Um bashi ba"
  "Ayshe yi shuru idan Abban ki yazo zaije ya biya kud'in wutan a gyara kinji"
  Haka da k'yar ta lallashe ta tayi shuru, bayan tayi shuru ta tura bakin ta tace
  "Amma ina jin yunwa"
"Toh me kike so kici?"
"Chips"
"Ikon Allah ina zan samu miki dankalin turawa a daren nan Jannah, koh na dafa miki spaghetti?"
  Girgiza kanta tayi, Amma tace
  "Indomie fa"
Ta d'aga kai, "OK bara naje na dafa miki kinji?"
  Ba tareda ta amsa ba ta k'ara d'aga kanta. Haka Amma ta shige d'aki ta d'auko naira tamanin ta zura hijabin ta tafita ta siya, tana zuwa ta kunna mukubur ta d'aura Indomie, cikin 5mins ta girka ta zuba a plate. Tana shiga d'akin ta taga already har tayi bacci, guntun tsaki taja tana d'an bubbugata tana "Habibty ga Indomie'n ki tashi kici"
  Haka da k'yar ta tashi ta jogwalgwala Indomie'n da fock ta k'ara koma wa bacci.

   How do you see it?

Should I continue? ???? Or a new story???

Your Votes and Comments is so important please don't forget to!!!!

DUNIYA~Ina Zaki Damu!!!!Where stories live. Discover now