Washegari da safe wanda ya kama ranar asabar ba makaranta sai Islamiya, Jannah ce a tsakar gida take wani irin kuka tana bubbuga k'afanta tana cewa "Ammah nifa bazan je Islamiyan nan ba, ana duka na ni gaskia bazani ba"
Amma ce tazo da d'an gudu gudunta ta d'auke ta cak tana jijjigata tace
"Haba Habibty me yayi zafi har da kuka haka eh? Yi shuru ki daina kuka karki damu bazaki ba"
Turo bakin ta tayi tace "Toh ai Abba zai dake ni kuma ya mun tsawa idan yaga banje ba"
"Kar ki damu bazai dake ki ba muddun ina gidan nan, kuma anjima zanje na samu Malamin ku naja masa kunne kar ya kuskura ya k'ara tab'a min ke kinji? Ya ma sunan Malamin mai dukan ki in?"
Da d'an guntun hawayen ta tana mai turo bakin ta tace
"Mallam Ali gaja amma yana duka idan kace masa Ali gaja wai sai dai Mallam Ali"
Murmushi Ammah tayi tace "In Shaa Allah zan masa kashedi bazai sake dukan ki ba kinji Habibty?"
D'aga kanta tayi tana murmushi, ajiye ta Ammah tayi tace "Habibty bara na d'aura sob'o kan anjima azo nema babu"
Ba tareda ta amsa taba ta shige d'akin Abba da gudu, Ammah kuma ta shiga Kitchen dan d'aura sob'o a kan wuta dan shineh sana'ar ta.Tana sab'o akwai wani almajirin ta mai kai mata waje dayawa yana siyar mata kuma Alhamdulillah tana ciniki dan mutaneh dayawa suna k'aunar sob'on ta.
Bayan ta d'aura akan wuta ya tafasa ta sauke, shiga d'akin ta tayi dan ta kimtsa kan sob'on ya huce ta had'a. Speaker ta had'a da wayarta ta saka wak'an M.Sheriff ta kura volume d'in gaba d'aya. Miming wak'an take sai kace tare da M sheriff d'in suka rera wak'an tana yi tana taka rawa tana kimtsa d'akin.
Kashim neh ya shigo cikin gidan yana ta sallama amma shuru ba amsa ba sai dukan sautin da yakeji dake tashi, ganin zai b'ata lokaci kawai yayi hanyan d'akin Abban sa ya cusa kai tareda sallama. Ganin Jannah yayi tana game da wayar Abba wanda shineh dalilin da yashigo da Kashim cikin gidan, Jannah wanda bata san ya shigo cikin d'akin ba sai game take da wayar tana bin wak'an da Ammah ta saka. Matsowa kusa da ita Kashim yayi ya warta wayan nan take ta d'aga manyan idanuwan ta sauke su a kansa, ganin Yayan ta Kashim take ta fara hararar sa, ce mata yayi
"Abba neh ya aiko ni na d'auko masa wayar sa ya manta kuma wallahi zan tattakaki idan kika k'ara harara ta "
Wani irin ihu tayi da gudu ta bar d'akin ta shige d'akin Ammah ta rungume kafanta tana kuka tana yarfa hannayen ta, Ammah hankalin ta take ya tashi nan ta kashe speaker'n tace
"Habibty lafiya?" Tana mai shafa fuskan ta
"Habibty waya tab'a min ke?"
Cikin kuka had'e da shagwab'a Jannah tace
"Ammah Yaya Kashim neh ina game da wayar Abba ya karb'a kuma ya dake ni"
"Meye!!!?". Take ta ajiye tsumman dake hannun ta tace
"Yana ina shi Kashim d'in? Koh uwar data haife sa bata isa ta tab'a min ke ba bare shi"
Take ta fita a d'akin, tana fita taci karo da Kashim d'in, shiko har k'asa ya durk'usa yace
"Ammah ina kwana"
Dunkule ta masa tace "Da ban kwana ba zaka ganni haka eh dan uwar ka"
Kansa a k'asa yayi shiru, zuwa tayi ta wanke sa da mari taja kunnen sa da k'arfi wanda yasa yaji zafi kar kwakwalwansa tana huci tace
"Uban waye ya aiko ka gida nah da har zaka tab'a min 'yata"
Cikin rad'ad'in rik'e masa kunnen da tayi muryan sa na rawa yace
"Ammah wallahi ban tab'a Jannah ba, Abba neh ya aiko ni na d'auko masa wayar sa ya manta kuma bazai iya komawa ya d'auka ba sabida wasu suna jiran sa a kasuwa"
"Shineh dan tsaban mugunta da bak'in hali irin na uwar ka zaka dake min 'ya"
"Ki yarda dani wallahi ban tab'a taba"
"K'arya kake shege munafiki kawai"
Sanda taja kunnen sa son ranta kan ta sake shi da sharad'in kar ya k'ara tako kafan sa gidan*ASALIN LABARIN SU*
Mallam Hamisu shuwa neh usul, babban malami neh a maiduguri yana da mata d'aya Habiba wanda Allah ya azurta su da yara maza gudu biyu Kashim da Ibrahim. Tun Kashim nada shekaru goma sha biyu Ibrahim nada goma Allah yayi wa Mallam Hamisu rasuwa. Haka matar sa Habiba ta kula da yaran ta tabbata sun samu illimin addini sosai basuyi boko har Allah yasa suma sukayi aure a rana d'aya. Kashim ya aura 'yar yola bafulatana kyakkyawan gaske mai suna Aysha, Ibrahim kuma ya aura yaren sa shuwa kuma 'yar k'auyen su Kalabalge ita kuma sunan ta Ramlah.
Bayan shekara d'aya Aisha ta haifa 'yarta kyakkyawan gaske son kowa kin wanda ya rasa aka saka wa Inna wato mahaifiyar su (Habiba) takwara, a cikin watan kuma matar Ibrahim Ramlah ta haifa d'a namiji suka sa sunan mahaifin su wato Hamisu. Murna a family'n ba magana, sai kuma cikin ikon Allah duk basu k'ara samun haihuwa ba har sai kusan shekaru biyar Aisha ta haifa d'an ta Kyakkyawa shima suka rad'a masa suna Abdulqadir(Abba). Ita kuwa Matar Ibrahim daga kan Hamisu wanda suke kiran sa da (Abi) haihuwa shiru sai can har ma ta fidda rai dan yanzu Hamisu yana da shekaru goma sha d'aya Allah ya bata wani cikin, murna a wajen su ba magana cikin ikon Allah ta haifa 'yarta Amina suna kiran ta da Meenah.
Mallam Kashim yaran sa biyu Habiba da Abdulqadir Mallam Ibrahim shima yaran sa biyu Hamisu da Amina, murna a wajen su ba magana suna bala'in son Meenah sabida itace 'yar auta kuma mace.
Bayan shekaru uku Mallam Kashim ya tattara kayan sa zai koma lagos sabida kasuwan cin sa ya bunkasa, sosai sukayi kukan rabuwa dan an saba da juna sosai a lokacin Meenah na da shekaru had'u Abdulqadir kuma shekarun sa goma.
YOU ARE READING
DUNIYA~Ina Zaki Damu!!!!
Mystery / ThrillerNow every gurl's dream is to marry a rich Man. money! money! money!!!! is what all gurls crave for now... Duniya is a story of a young spoiled girl born in a poor family. All she ever wanted is to marry a billionaire! Find out if she's gonna end up...