CHAPTER FOUR

222 20 0
                                    

        Rungume 'yar ta tayi tana shafa bayan ta tace "Jannah yi hak'uri kinji kinsan kalan bak'in halin Kashim koh? Toh uwar sa ya biyo" Jannah kuwa sai tura bakin ta tayi tace
"Ammah nifa kullum idan naje wajen Mama sai ta siya min biscuit"
Had'a rai Ammah tayi tace "Karki kuskura k'ara zuwa gidan su, wata rana ai sai ta saka miki poison a biscuit d'in kinci kin mutu, kina so ki mutu?"
Take Jannah ta girgiza kanta tace "A'a"
"Yawwa toh idan ta k'ara  baki abu karki kuskura kici kinji?". Jannah d'aga kanta tayi kawai alaman toh, Ammah tace
"Wai ni bana hanaki zuwa gidan su Kashim ba, uban meye ya kaiki?"
Cikin shagwab'a tace "Nifa Abba neh mu kaje tare dashi", sosai ta harzuk'a tace
"Kai Abdulqadir sam baya kyauta min wallahi, idan ya dawo wallahi sai munyi dashi, idan ya k'ara d'aukan min 'ya yakai ta wani gidan Allah ya isa nah" (Duniya ina zaki damu??? Wallahi wallahi akwai matar da nasani tace wa yaran ta idan suka kuskura suka je gidan kishiyar ta bata yafe musu ba kuma baza ta tab'a yafewa ba. Haba Mata kishin nan har ina??? Duniya ce fa!)

   Bayan Kashim ya kai wayar Abban sa wajen sana'ar sa Abba yayi dashi su d'an zauna amma yace shi gida zashi sabida wani irin ciwon kai dake addabar sa a dalilin ja masa kunnen da tayi da k'arfin da Allah ya bata.
  Da k'yar ya iya takawa yaje gida, shima gida neh d'an k'arami har gwara gidan su Ammah, yana shiga ya tarar da mahaifiyar sa zaune tana gyara zogale. Waje ya nema ya zauna yana mai rik'e kansa sabida rad'ad'in da yake ji. Kallon sa take cikin kulawa tace
"Baba nah lafiya na ganka haka?"
"Mama wallahi lafiya kawai kai na neh yake ciwo amma idan nasha paracetamol ma In Shaa Allah zai daina"
"Allah sarki Allah baka lafiya"
"Ameen Mama"
Duban sa ta sake yi tace "Ya Ammah tana nan lafiya koh?"
"Lafiyan ta kalau"
"Baba nah meye sa baka zuwa kana gaishe ta kullum neh baka san itama mahaifiyar ka bace?"
Had'a rai sosai yayi  yace "Mama kinsan dai Ammah bata son mu koh? Kullum idan muka je sai ta kora mu"
Murmushi tayi tace "Ai duk da haka mahaifiyar ku ce"
Gyara zama Kashim yayi yace "Mama wai meye sa Ammah kullum sai tace mana wai ke kika jawo mana dan ita ta d'auke ki babbar k'awarta amma kika ci amanar ta?"
Ajiye zogalen hannun ta tayi da guntun murmushi a fuskan ta tace
"Har yanzu tana nan a matsayin aminiya ta, karka damu babana idan ka girma zan fad'a maka meye sa take fad'an haka"
"Toh shikenan Mama"
"Yanzu shiga ciki kasha magani kaji?"
Tasowa yayi yace "Toh Mama"
Bayan ya shiga cikin d'akin Mama tayi ajiyan zuciya, ita har yau har gobe tana jin son k'awar ta a ranta....


*After Nine Years* _(Bayan Shekara Tara)_

   Shekaru sun shud'e abubuwa dayawa sun canza ciki kuwa Abba ya had'a matan sa biyu gida d'aya, Ammah ta samu rabo ta haifa d'anta Hashim wanda yanzu yake da shekara takwas. Duk da yadda Meenah taso suyi shiri da babbar kawarta kuma aminiyar ta har yau amma sam Ammah taki bata fuska.

  Kashim a halin yanzu yana da shekaru ashirin da uku ya gama degree inda ya karance Mechanical Engineering a University of Maiduguri  yana jiran service, yayi wani irin girma na ban mamaki sai ka rantse yafi haka gashi sam baya sake wa kannen sa fuska balle su raina sa, a halin yanzu kaf kannen sa suna shakkan sa harta Jannah, dan idan tayi laifi har d'aki yake binta ya zaneta son ransa Ammah ma bata iya masa magana sai dai idan ya fita a d'akin tayi ta zage zage. K'anin sa Faisal kuma yana part 3 a Maths and Stat, Ibrahim da Jannah wato Ayshe sun zana waec da jamb, sai kuma autan su Hashim yana primary 3. Jannah ta k'ara girma tayi wani irin kyau sosai.


    Kwalliya sosai tasha ta saka wando da crop top bak'i ta d'aura kimono red da touches bak'i tayi rolling kanta da gyale bak'i ta saka wani dogon high heel vinci shima bak'i, bakintan nan yasha jan baki red, sosai tayi kyau abu da farin mutum ya had'a da red and black. Tafiya take kamar hawainiyya dan yanzu ya riga ya zame mata jiki tana chewing gum, idan ka ganta sai ka rantse 'yar gidan masu shi neh. Bud'e k'ofan su zatayi wanda duk ya k'ormashe duk tsatsa taji an datse k'ofan, d'aga manyon eyes nata tayi wanda yaji eye liner ta sauke su akan Kashim, wani kallo yake watsa mata yace
"Inaa zuwa?"
Ranta idan yayi dubu ya b'aci dan ita a duniya ta tsana ta bud'e ido taga Yayan ta Kashim dan a ganin ta sosai yake kawo mata cikas a rayuwa. Tura bakin ta tayi hawaye fal ya cika mata ido tace
  "Birthday party'n friend nah"
"Shineh da riga da wando?"
  Kallon kanta tayi daga sama har k'asa tace
"Yaya Kashim ga kimono akai I don't see anything wrong with that"
Buga bakin ta yayi wanda yasa ta d'an yi k'ara yace
"Yanzu yanzun nan kije ki canza kayan nan, kina 'yar musulma ki saka wando da top and you opened that your filthy mouth kina cewa you don't see anything wrong with it!  Very stupid girl kawai"

Haka ta koma cikin gida tana bubbuga kafanta. D'akin ta tashiga wanda ba komai a ciki sai wani katifa da duk a cinye da d'an guntun dadduman ta a k'asa, sai kuma akwati wanda zasu kai kusan dozen biyu duk a cike fal da kaya wasun ma har basa rufuwa. Cire Kimonon jikin ta tayi ta saka doguwar riga habbaya bak'i  a kai ta k'ara rolling da same gyalen ta na d'azu, Kimonon ta n'inka ta cusa a cikin chain bag nata mai uban tsada ta fice a gidan...

   Tana fita ta tsaida  tricycle sai Fushams Hotel inda suka yi booking hall na birthday d'in. Tana zuwa ta same k'awarta Rukayya, Rukayya yarinya ce sa'ar Jannah black beauty kuma halin su zat yazo iri d'aya da Jannah. Wani bumshort neh a jikin ta da wani riga armless ta zuba gashin ta a baya sosai tayi kyau, kallon Jannah tayi daga sama har k'asa tace
"Beb ya na ganki haka neh?"
Guntun tsaki taja tace "Kibari kawai nida Yaya Kashim neh, d'an rainin sense kimono ce fa ajiki nah ya saka ni dan dole na canza"
Dariya sosai Rukayya tayi tace
"Kaiii wallahi Yayan kin nan mugun d'an wahala neh baisan you'll never ever gonna change ba"
Rolling eyes nata tayi tareda jan guntun tsaki tace
"Change to what? Mtsssww"
Ba tareda da tayi tunani ba ta cire habbayan dake jikin ta ya rage daga ita sai top  na jikin ta tace
"Muje koh? Wani hall neh?" Tana kad'a eyes nata, Sosai Ruky tayi dariya tace
"Muje ina? Ke da wa? Like this???" Pathetic!"
Tana mai nuna ta da yatsa, Jannah sosai take mamaki ta bud'e baki tana mai k' are wa jikin ta kallo, b'ata rai tayi tace
"Please don't tell me dressing na baiyi ba"
Girgiza kanta Ruky tayi tana wani irin dariya tace
  "Kinyi kyau, but you look like a gurl with no class. You look cl-a-s-s-le-s-s" tayi emphasising word d'in, sosai abun ya k'ona wa Jannah rai tace
  "Kin san daga ina aka kawo mun wannan rigan" Tana mai jujjuyawa"
Rukayya tana mai dariya harda rik'e cikin ta tace
  "Hold it to yourself dan I don't wanna know"
Ta toshe kunnen ta, Jannah da k'arfe tace
"Gaga GH kuma kinsan Zayd baya kawo mun abu idan ba designers ba kuma latest"
Rukayya ta d'aga kanta tareda zaro eyes nata tace
"Ohhhh ummmm haka neh, ke banza kina wani jijji da Zayd yana karatu a Ghana banza kawai, idan kika shiga nan zaki raina kanki, kinsan friends na Zee-Zee 'yan university neh, daga masu saurayi a UK sai masu saurayi a Russia ke banza wani Zayd naki yana nan nan Ghana kibi ki ishe mutaneh, nifa bance rigan ki batayi ba, a'a wannan wandon neh nake so ki canza"
Jannah cusa hannun ta tayi cikin dogon sumar kanta wanda ya kwanta har gadon bayan ta tace
  "Toh yanzu ya zamuyi Ruky kinsan I hate people to look down on me? Idan nace zan shiga kasuwa na siyo ai har za'a gama party'n kuma ni gaba da baya 5k neh a account d'ina kuma gaskia perfumes na sun k'are so nake na siyo wasu"
Guntun tsaki Ruky taja tace
"Allah zai kawo kud'in perfumes kedai yanzu mu hau tricycle muje mu siyo miki wani trouser"
"Ohk toh"
Jannah Kimonon ta tasaka akan wandon, Ruky kuma ta saka doguwar rigan da Jannah tazo ta dashi


Comment


Share


And must importantly don't forget to vote!!!!!!!!

DUNIYA~Ina Zaki Damu!!!!Where stories live. Discover now