CHAPTER EIGHT(B)

140 8 0
                                    

Hea Guys!!!!! I am so freaking happy to tell that I AM BACK!!!!

Y'all must be thinking zan cigaba da NIDA TAGWAYEN MAZA (Lol) But unfortunately it happens that zan cigaba da wannan 1st, idan na samu time will be posting both In Shaa Allah. Kuyi hak'uri da ni fa, I know I am not a straight forwarded! Person at all... Sha enjoy it!!!!

Jannah bata farka ba sai k'arfe bakwai na safe, da k'yar ta iya ta tashi dan duk jikin ta yayi tsami yana wani irin rad'ad'i. A daddafe ta tashi ta shiga toilet tayi alwala, ta fito daga ban d'aki kenan taga Hashim da uniform na makaranta yana rufe zib na jikin sa, murmushi ya sakar mata yana cewa "Anty Jannah jiya Abba ya zane ta" Wani uban harara ta sakar masa tayi shigewar ta d'aki dan ji take batada lokacin sa, tana shiga tayi sallah, bayan ta idar ta d'au ledojin da Jay ya siyo mata kayayyaki. Zub da kayan tayi kan gado tana binsu da kallo d'aya bayan d'aya. D'an banda wayan da ya siyo ga abayas had'add'u guda biyar da jaka k'anana masu kyau sai uban tsada. Kwalin wayan ta d'auko tana jujjuyawa, muryan Ammah taji a bakin k'ofa tana sallama, da d'an tsiririn muryan ta ta amsa tace "Ammah shigo mana", Bud'e k'ofan Ammah tayi ta shiga d'akin tace "Habibty ni jiya meye yafaru na dawo daga teaching hospital naga Abban ki a sakar gida yana ta k'ananan surutai wai na bi na b'ata ki, inaso na shiga d'akin ki na duba ki amma ya hana. Wani d'an guntun tsaki taja tace
"Ammah ki mantar da Abba, kawai dan wani saurayi na yazo ya sauke ni a gida shikenan ya mare ni wai zan b'ata masa suna a anguwa. Ni a duniyan nan idan kana bin ta mutane ai baza ka tab'a yin abun son ranka ba"
"Sub'hanaAllah, ya jikin naki yanzu?"
"Norms fa, karki damu Ammah" Dan Jannah ta san sarai idan ta fad'awa Ammah irin dukan da Abba ya mata baza'a kwana lafiya a gidan ba.
"But Hashim yace mun wai da belt da bulala aka zane ki"
"Mtsw ki daina jin maganan Hashim Ammah na"
Nuna mata kayakin kan gadon Jannah tayi tace
"Ammah na ki gani" Nan take Ammah tazo gaban kan gadon ta tsuguna tana kallon kayan d'aya bayan d'aya, ta d'au wayan tana jujjuyawa tace
"Habibty ina kika samu kaya masu mugun tsada haka? Gashi har da waya uban su"
Wani d'an shu'umin murmushi tayi tace
"Wani na samu mai uban kud'i, kinga yadda yake fitar da kud'i? Kamar bai san zafin su ba"
Gyara zama Ammah tayi tace
"Dan Allah? Shi kuma ina kuka had'u dashi?"
"Mtsw wallahi wajen birthday party'n wata k'awata neh"
"Wai wai wai, Mashaa Allah! Ya sunan shi? D'an garin nan neh?" Ta tambaya a rikice tana mai kallon wayan, d'an murmushi Jannah tayi tace
"Sunan shi Jay, kuma a garin Abuja yake"
Washe hak'oran ta Ammah tayi tana jin dad'i tace
"Haba dai, ikon Allah. Tun da ina fad'a miki idan kin samu wanda yafi wancan d'an kirtan saurayin naki ki rabu dashi, dan ni wallahi tun asali ba son sa nake ba"
Dariya Jannah tayi tace "Ammah kenan, Ammah baza ki ganeh ba, So ba ruwan shi da kud'i koh arziki, Zayd na sona tsakanin sa da Allah, nima haka"
Buga bakin ta Ammah tayi tace
"Kul! Kar na sake ji kin furta wannan mummunar kalma wai so, so na kai mutum ga halaka, ni nan ba auren so nayi ba? Meye ya tsinana min idan ba bak'in ciki ba? Habibty so baya d'aure wa koh a zamanin da balle yanzu, yanzu komai ya b'aci, kud'in ka mutuncin ka. Mata nawa suke k'in masu kudi su aura dan so, amma daga baya zakiga ana samun matsala. Zakiga wata ta aura miji bashi da koh sisi, amma da zaran yayi kud'i ba abunda zai fara zuwa masa ransa sai k'ara aure. Wasu kuma suga dan son yi kud'i su shiga neman matan waje. Wasu mazan kuma idan basuyi kud'i ba sai ki ga at times goes on halin su zai canza, zasu zama masu zuciya da bak'in hali, kinsan talaka zafin rai neh dashi. Toh a wannan lokacin idan kin aura mijin ki bashi da kud'i yazo yayi kud'i idan zai k'ara aure sai kiji b'acin rai, kina ganin bai kyauta miki ba, kina ganin yaci amanar ki, toh a wannan lokacin zaki nema son da kike masa ki rasa, idan kuma wanda bai samu yayi kud'i ba zaki same sa da zafin rai in which baza kiji dad'in auren ba. Ni bana so kisha wahala Habibty, idan zakiyi aure ki aura mutumin da eh ke kanki kin san kud'in sa kike so, ki aura mutumin da koh zai miki kishiya koh zai nema matan waje bazai dame ki ba as far as kina babban gida, kina ci mai kyau kina sha mai kyau, ina jan motan da kike so, kina kashe kud'i son ranki. Kina ganin idan kika samu jin dad'in rayuwa namiji ya isa ya cusa miki bak'in ciki?"
Nauyayyan ajiyan zuciya Jannah ta sauke tace "Ammah na kenan, waye baya son jin dad'i?"
Kama hannun 'yarta tayi tace "Banso ki wahala Habibty, banso ki wahala. Kiso duniya yadda zaki more shi kinji?"
Dariya tayi tace "Angama Ammah"

Bayan Ammah ta fita a d'akin ta d'au sabuwar wayan ta ta jona shi a charge, d'aukan wayan ta tayi taga 7 missed calls, d'aya na Jay, biyu na Ruky sai hud'u na Zayd. Zayd ta fara latsa wa kira, ringing d'aya yayi picking call d'in, da muryan sa mai dad'in sauraro wanda ni kaina inajin abunda yake fad'a yace
"My Soulmate ina kika shiga? Kin tada mun hankali nata kiran ki bakya d'auka wa, ni wlhy sam naji karatun ya fita a kaina kamar na dawo gida, tsoro nake kar wani ya kwace min ke"
Wani murmushi tayi tace "Ni taka ce, taka na har abada, ka daina damun kan ka. A DUNIYA kai nake so, kai na zab'a, idan har kaga bamu kasan ce tare ba toh sai dai ni koh kai d'ayan mu baya numfashi"
Ajiyan zuciya ya sauke yace "Kinsan ke kyakkyawa ce, you're so beautiful Ayshe, ba namijin da zai ganki bai sake juyawa a k'aro na biyu ya sake miki kallo ba"
Dariya sosai tayi tace "Kai ka san inada da kyau Zayd, kai kake mini kallon ni mai kyau ce amma ba hakan baneh"
"Ki yarda da ni Soulmate, wallahi a duniya samun irin ki zaiyi wahala. You're so beautiful and you've a good heart"
"Thank you My Love, nidai ka kwantar da hankalin ka, ni taka ce"
"Allah sa Soulmate"
"Ameen, Ya labarin ghana? Ance mun akwai mata masu kyau har su half cast. Ina tsoron kar wata ta kwace min kai"
Dariya yayi sosai yace "Ikon Allah, Mata masu kyau ghana? Ni duk kallon maza nake musu. Kuma mai zanyi da matan can? Thou akwai musulmai akai masu hankali abun wasun su sai addu'a Ayshe. Kai Ayshe, DUNIYA INA ZAKI DAMU? Ayshe idan kinga iskancin da wasu mata suke anan sai kin musu kuka, wallahi abun ba kyau. Gaba d'aya an maida tsab'on Allah ba komai ba, an maida zina kamar wani abin burge wa. Shiyasa nake alfahari dake Soulmate, na yarda dake, nasan a duniya baza ki tab'a bawa wani kanki idan ba mijin ki ba. Allah kaimu auren mu dake Ayshe, can't wait to kiss your virgin lips, can't wait na zama farkon namijin da zaki sani a rayuwa. Zan nuna miki so, zan nuna miki so Ayshe. Baza ki tab'a da na sanin aure na ba Ayshe. In Shaa Allah"
Wasu zafafan hawaye neh suka sauk'a akan kuncin ta tana mai shafa lips nata, take ta kashe wayan gaba d'aya ta fashe da wani irin kuka, sai yanzu take dana sanin abunda tayi, sai yanzu take jin haushin kissing nata da Jay yayi, ruf ta kwanta akan gado tana kuka zuciyan ta na me k'ona, a haka har bacci ya kwashe ta...

Da misalin k'arfe biyu na rana Ruky ce ta shigo gidan su Jannah, ganin Mama tayi a sakar gida tana shara, har k'asa ta tsuguna ta gaishe ta, tace "Haba Mama ke da kanki kike shara, ki bari zanyi". Kan Mama tace wani abu take Ruky ta karb'a tsintsiyan, Mama tayi murmushi tace
"Allah sarki 'yar nan kullum idan kika zo sai kin tayani aiki, nagode Allah saka da alkhairi"
Murmushi Ruky tayi tace
"Haba dai Mama ba komai wlh, ni kam ina Ayshe dan tun da safe nake trying number ta baya shiga"
"Ahh wlhy yau koh motsin ta banji ba, amma ina ganin tana ciki tana bacci, kin santa da son bacci" Dariya Ruky tayi tace
"Ai malalaciya ce, she is too lazy wlh"
Murmushi Mama tayi tace "Kunfi kusa" nan takr ta share tsakar gidan tsaf, bayan ta gama ta shiga d'akin Ammah ta gaishe ta, Ammah ta fad'a mata Jannah na d'akin ta...

Kwance ta tarar da ita tana bacci, a hankali tazo kusa da ita ta matso da kanta kusa da Jannah, Cizo ta kai mata a kunne take Jannah ta farka a firgice. Ganin Ruky da tayi taja wani dogon tsaki ta had'e rai kamar hadari, dariya sosai Ruky tasha tace
"Zuhr fa yayi yarinya "
A tsawace Jannah tace "Ke wace irin banza ce, what you did was wrong"
Dariya Ruky tayi tace "Kema kina min fiye da haka, malama tashi kiyi sallah please lokaci yana guduwa"
D'an guntun tsaki ta ja ta nufe toilet, bayan tayi alwala ta shigo d'akin lokacin Ruky na danne-danne da wayan ta tace
"Hmm ke Ruky you didn't ask me abunda yafaru jiya"
Dariya Ruky tayi tace
"Yi sallah'n ki first sai muyi hiran"

Like

Vote

Comment

Share

Much love❤❤❤

DUNIYA~Ina Zaki Damu!!!!Where stories live. Discover now