CHAPTER SEVEN

187 19 2
                                    

   Wani kayataccen parlour neh wanda yasha kayan alatu, tsaya misalta had'uwan parlour'n b'ata lokaci neh, Jay na hango yana saka agogo a hannun sa k'irar Armani sai wani irin murmushi yake yi yace
"Ya Babs zamu je neh ko ya?"
Yayi wa wani guy magana wanda yake ta danne-danne da wayarsa, dariya wanda ya kira da Babs yayi yace
"Kai Baaba ka bari kawai abu gobe da safe zamu wuce sai dai next time idan Allah yasa mun sake zuwa"
"Akwai wata k'awar ta fa wallahi idan ka ganta zaka falling mata dan itama ta had'u"
Tunani ya d'an tsaya yayi yace "Kai inaa ka bari kawai aboki na sai next time ni yanzu kaina ma ciwo yake but ka tafi da AMG mana ka saka shi a hanya, ka nuna masa life"
  Wani yaro neh sa'an Jay wanda shima ak'alla bazai haura ashirin da shida ba ya fito a wani d'aki rik'e da cup a hannun sa, dogo neh sosai wankan tarwad'a, yana da broad chest da packs, jikin sa irin na mazan da suka sha gym, ga saje kwance luf akan fuskan sa, tsaya describing kamannin sa inaga waste of time neh dan ya had'u na k'arshe, duk inda aka ce namiji toh yakai har ya wuce.
  Wani kallo ya watsa musu ya zauna a kujera tareda d'aukan remote dake center table, Jay da Babs neh suka fashe da dariya Jay yace
"Kai Babs ya zakayi wa mutumina haka neh kasan ba ruwan shi da harkan mata"
Babs yayi dariya yace "Ai mata su DUNIYA neh"
Wanda suka kira da AMG girgiza kansa yayi yace
"Kuma su zasu kaiku lahira idan baku tuba ba"
Babs dariya yayi yace "Please dan Allah ka barmu muyi enjoying life koh da kad'an neh"
Ajiye cup na hannun sa yayi yace "You will never gonna change"
Dafe kafad'an sa Jay yayi yace
"Change to what Dude? What those a man need  apart from money and woman?" 
Girgiza kansa AMG yayi yace "Allah shirya"
Duk suka had'a baki suka ce "Allah shirye mu gaba d'aya"
D'aukan key na motar sa Jay yayi ya fice a gidan sai hanyan gidan su Ruky....

    Wani sabon make-up tasha, Ruky musamman ta hura charcoal ta saka turaren wuta Jannah ta cire kayanta ta aza akan khabbasan da yaji turaren wuta, sanda kayan yayi wani irin k'amshi kan ta saka a jikin ta, body spray masu k'amshin gaske ta k'ara fesawa a jikin ta, ta k'ara d'au humra ta shafa a fatan jikin ta. Wani irin rikitaccen k'amshi ke tashiwa a jikin ta ga wani irin kyau'n da tayi. Ruky ce take washe hak'ora tace
"Mashaa Allah K'awata wallahi kin had'u, son kuwa k'in wanda ya rasa"
Jannah sai jin kanta take a sama tana wani irin murmushi dan ita kanta tasan tabbas ta had'u, wani rolling eyes nata tayi tace
"Ki fad'a da babban murya Ruky"
  Wani irin dariya Ruky tayi tace "'Yar iska toh bakiyi ba"
Wayar ta neh ya fara ringing, ganin Jay baro-baro akan screen yasa Ruky tayi saurin d'aga wayan ta mik'a wa Jannah, bayan ya mata magana tace "Ohk toh gani nan fitowa"
  Kallon Ruky tayi tace "Ruky yazo shi fa"
"Ohk ki bari sai irin after 10mins sai ki fita ki d'an ja masa aji"
"Ohk toh"

  Haka suka zauna suna kallon wani Indian film Kick wanda suka share kusan 20mins ba tareda sun sani ba, ringing na wayarta neh yasa tayi firgit daga kallon da take taga Jay, tab'a Ruky tayi wanda all her attention yake kan film d'in tace "Ke fa he is calling again"
Duba agogo Ruky tayi taga ashe fa har kusan twenty five minutes suka share, bud'e baki tayi tace
"Yanzu kusan twenty five minutes da yazo fa, yi sauri ki tashi ki tafi please kar yayi fushi"
Da sauri Jannah ta tashi ta k'ara shafa powder da turare. ..

    Wani irin cat walking take wanda is now part of her baza ta iya daina wa ba, wani mota Benz tagani ash colour glass d'in super tint ba'a iya hango wanda yake ciki. Latsa number'n sa tayi ringing d'aya yayi receiving yace
"Baby na tun d'azu nake jiran ki fa"
"So sorry Dear kaine a cikin wata ash mota?"
"Eh ki k'araso please na hangoki"
"Ohk" Ta katse wayan.

    Tana isa wajen motan ta bud'e k'ofa tashiga, wani irin k'amshi neh ya dake hancin sa wanda ya nema nutsuwar sa ya rasa, ji yake kamar ya rungume ta ('yan mata turare fitina neh a kiyaye fesawa irin over). Murmushi ta masa wanda kyakkyawan hak'oran ta fari tas suka baiyana da kuma dimples nata suka lutsa wanda ya k'ara fidda asalin kyaun ta.
Wani lumshe idanuwan sa yayi yace
"Mashaa Allah Jannah wallahi Allah ya zuba miki kyau"
D'an dariya tayi tace "I know"
Zaro idanuwan sa yayi yace "Haba? Ki fad'a min maza nawa suka ce miki kina da kyau"
Murmushi tayi tace "Madubi ai baya k'arya"
Dariya yayi yace "Wow I love that, but ai wani madubin...."
Katse shi tayi tace "Shhhh mu bar maganan, ya kake?"
"Lafiya kalau Baby nah wallahi tun jiya dana ganki na kasa samun nutsuwa"
Kallon cikin idon sa take tace "Same here Durlin"
Wani irin murmushi yayi yace
"Allah?"
D'aga kanta tayi tace "Ga gaskia ga rantsuwa baka ganin abun zaiyi yawa?"
"Hahah haka neh fa Baby, yanzu bari muje city star muci abinci dan yunwa nake ji"
"Ohk toh ba matsala"

    Jan motar sa yayi sai City star, ordering na Burger, Pizza da Ice cream sukayi. A wajen suka zauna suna ci suna hira yake bata labarin sunan shi Jafar asalin d'an Kano neh  amma yana zama a Abuja and yazo wani program shida friends nashi neh kuma gobe zasu koma. Sosai taji ba dad'i da yace mata gobe zasu koma kenan arzikin da take tunanin zata samu da k'yar ya yiwa.
Kamar zatayi kuka tace "Yanzu Durlin gobe zaka koma?"
Shafa fuskan ta yayi yace
"Don't worry baby zan tura miki kud'in flight kije ki same ni a can"
  Wani irin dad'i taji anyi maganan jirgi da abuja, amma data tuna Abban ta da Yaya Kashim taji zuciyan ta ba dad'i, ganin ta yak'une fuska Jay yace
"Koh baza ki zo waje na ba Baby?"
"Ba haka baneh Jay wallahi akwai wani Yaya nah mugun d'an wahala neh bazai barni nayi tafiya ba"
"Koh da wajen 'yan uwan ki zakije?"
Har tana so tace masa basu da 'yan uwa a Abuja amma gani take idan ta fad'a aji down neh yanxu zaiyi looking down on her tace
"Wallahi fa, Uncle namu dake Abuja yanzu suna Moscow da family'n shi kan su dawo gaskia zai jima"
"Ohk ba matsala zan na zuwa ina duba ki Baby don't worry kinji" tareda shafa fuskan ta.

   Bayan sun bar city star ya kaita wani babban plaza inda ya siya mata kaya masu kyau'n gaske da sabuwar waya Samsung note7, sosai tayi murna dan daman tsana ta bud'e ido ta ganta da hegiyar wayar ta k'irar Infinix. .

  Bayan sun shige mota tace
"Yanzu sai gida koh dan har an idar da sallah'n magrib"
"Baby gida kuma? Muje gida na mana ki gani". Yana mai murza hannun ta. Yak'une fuska tayi zuciyan ta na mai bugawa tace
"Wallahi zamun fad'a a gida some other time Dear"
Murmushi yayi yace
  "Ba komai lemme drop you at home ai ana tare"
Hankalin ta neh taji ya kwanta tayi murmushi tace
"Thanks lurv"

  Har k'ofan gida ya kawota, sai wani murza hannun ta yake yana lumshe ido tareda lashe leb'en sa yace
"Yanzu mai zaki min ina tunawa dake"
Kallon kissa take masa tace
"Me kake so Lurv?"
Matsowa kusa da ita yayi yana kallon lips nata, ji tayi zuciyan ta ya buga dan tunda take da Zayd bai tab'a taba koh da hannun ta ba.
Had'a lips nata da nashi yayi sanda ya tsotsa bakin ta  tas iya son ransa (wa'iyazubillah) ita kuwa ta tsaya kamar gunki, bataso ta hanasa ganin ya kashe mata kud'i sosai, sanda ya tsotsa iya son ransa ya sake ta yana mai sauke numfashi, ita kuwa sai wasa take da ring na hannun ta ta k'asa had'a ido dashi. Wani rungume ta yayi yana shinshinata kamar kare yace
  "I love your smell Baby, is really driving me crazy"
Cusa kanta tayi a k'irjin sa zuciyan ta na mai bugawa amma haka ta dake tace
  "I will miss you Lurv"
"I'm gonna miss you more Baby"

Cire kud'i yayi a aljihun sa dubu d'ad'd'aya bugun abuja ya mik'a mata yace
"Ki siyawa wa Hashim Biscuit". Dan zaman da suka d'an yi har yasan Hashim dan bata da wani magana sai k'anin ta Hashim. Murmushi tayi tace
"Thank you Lurv" Ta amsa ta cusa a cikin jakarta, ji yayi kamar kar ya rabu da ita dan zaman da sukayi ta shiga ransa sosai, murmushi tayi tace
"Zan shiga gida Lurv yanzu fa isha ake kira koh magrib banyi ba ka min wayo kai kayi magrib"
Rungume ta ya sake yi yace
"Baby ji nake kamar kar mu rabu"
Shafa fuskan sa tayi dan ita Allah Allah take ya tafi tagaji dashi tace
"Don't worry Durlin ai ba rabuwa na har abada zamuyi ba, even bamu tare but zuciyan mu yana tare"
"Take care of yourself for me"
"I will Durlin"

   Must  Vote

Comment! !!!!

Share!!!!!

DUNIYA~Ina Zaki Damu!!!!Where stories live. Discover now