CHAPTER FIVE

194 17 0
                                    

Tricycle suka shiga ya kaisu wani babban boutique dake hanyan lagos street, Ruky taso Jannah itama ta d'au bumshort amma Jannah tace sam ita she want something different. Wani crazy wando ta d'auka bak'i wanda tun daga saman har k'asan a yage kamar wanda aka yaga da razor blade, Ruky wani deadly look ta mata tace "Beb are you serious?"
Rolling eyes nata Jannah tayi murmushi kwance a fuskan ta tace "Damn Serious Shawdy"
Haka ta biya kud'in wandon 4k suka fita a cikin boutique d'in, Ruky tace
"Jannah kefa 'yar duniya ce irin wannan wandon haka?" Dariya sosai Jannah tayi tace
"Ke barni ni yanzu matsala ta mu samu napep kar before we know su gama party'n"
Bata gama rufe baki ba wata mota corolla-X yazo yayi parking a gaban su. Wani mutum wanda ak'alla zaikai shekaru arba'in bak'i ba laifi yana da kyau ya fito a motar cikin sakin fuska yace
" 'Yan mata ina zuwa haka?". Jannah d'auke kanta tayi Ruky kuma tace
"Nan Fushams zamu shiga"
"Ohk toh ku shigo na kai ku mana"
Ruky nan take tace "Toh shikenan"
Jan hannun Jannah tayi suka shiga cikin motar, Ruky ta zauna a gaba Jannah ta zauna a baya. Sai hira yake musu duk sun basar dashi koh ufn basa ce masa sai sunan ta da Ruky ta fad'a mishi, har k'ofan Fushams ya ajiye su ya cire kud'i d'ari biyar biyar ya mik'a wa Ruky yace su hau Tricycle idan zasu koma gida tareda mik'a mata compliment card nasa yace
"Dan Allah Rukayya idan kin samu time ki kirani please"
"Ohk ba matsala"
     Bayan sun shiga cikin Hotel d'in Ruky ta fashe da dariya tace
"Nifa mutumin nan baiyi min ba" Dogon tsaki Jannah taja tace
"Toh uban meye ya kaiki kulashi"
"Haba ni nagaji da yawo a cikin adai-daita tsaho haba kamata yayi ace muna yawo cikin manya manyan motoci wallahi"
Dariya Jannah tayi tace "Ni ai kin san dan Zayd baya gari neh"
"Mtsw kefa banza ce mata nawa suke tara samari daban-daban masu kud'in gaske, kinga kalan motoci kuwa wanda suke zuwa wajen su? Ni wata rana abun har mamaki yake bani ina suke had'u wa dasu haka"
Guntun tsaki Jannah taje tace "Wallahi koh nima I wonder ina suke samun maso kud'i haka, akwai wata yarinya a arean mu kin ganta kuwa? Wallahi sam bata yi ba amma kinga irin kalan latest rides da suke zuwa wajen ta kuwa? Motoci na gani na fad'a, amma ni sai d'an Zayd da nake dashi shima dai a Zenith bank muka had'u dashi"
  Haka suke ta hira har suka same d'aki suka canza kayan jikin su suka k'ara painting fuskan su da make-up. Sosai sukayi kyau dan duk kansu suna da kyau na gani na fad'a.

   Cikin irin takun su kamar basu son taka k'asa suka shiga cikin Hall d'in, gaba d'aya ido ya koma kansu all eyes on them, ganin haka suka k'ara canza salon tafiya suna wani feeling kansu. Wajen birthday gurl d'in suka je suka mik'a mata wani k'aton gift wanda akayi raping nashi sukayi hugging nata suka had'a baki suka ce "Happy Birthday Zee-Zee". Murmushi Zee-Zee tayi tace "Thank you"

   Sosai suka case suka ci suka sha, dan party'n ta had'a wa friends nata  mata neh kawai ba maza.  Sosai wasu k'awayen Zee-Zee suka fara shige musu suna d'au pics tare, Ruky ta d'au wayar ta Samsung S6 edge suna ta selfie Jannah kuma tayi k'arya ta manta wayar ta a gida sabida bata son cire d'an wayan da Zayd ya siyo mata Infinix Hot 4 karsu raina ta, Cikin kunnen Ruky tace
"Kinga yadda suke cire Apple da Samsung ai aji down neh na cire wannan hegiyar China Infinix"
Sosai Ruky tayi dariya tace "Ai wallahi waya idan ba Apple ba toh Samsung, amma sauran duk aji down neh, yanzu so nake Bukar ya shigo gari ya canza mun wannan Samsung d'in ni gaskia IPhone 7 ce a raina, company'n Apple ai shineh class"

Wani ajiyan zuciya Jannah ta sauke tace "Ba gwara keba kinji dad'i nida nake rik'e da wannan hegiyar Infinix ji nake kamar na bugu shi k'asa dan takaici mtsw"
   Bayan an gama party'n ko wacce tayi shirin tafiya gida, a wajen Fushams Hotel d'in motoci neh sunyi parking duk suna jiran budurwar su, ganin friends na Zee-Zee sai cewa suke bye-bye suna shiga motan samarin su, wata friend na Zee mai suna Khady wanda tabi ta mak'ale musu ta kama hannun Jannah tace  "Ga saurayi nah ku gaisa koh za rage muku hanya neh naga har yanzu bazo an d'auke ku ba?"
Murmushi Jannah tayi tace "Wallahi Khady yanzu Swt nah ya buga min waya yayi hatsari i am so worried"
"Sub'hanaAllah, Allah  sarki how was he now?"
Cikin fuskan damuwa tace
"Wallahi yace min dai ba wani ciwo yaji sosai ba"
"Ayyah toh muje a sauke ku a gida kinji Dear"
"Hope bazamu tak'ura muku ba"
Murmushi Khady tayi tace "Not at all muje kawai"

Cikin takun su na k'asaita har suka kai wajen motar k'irar Perfection maroon colour  glass na motar bak'i k'irin wato super tint kai da kake waje baza ka iya ganin wanda ke ciki ba, bud'e musu back door d'in tayi tace "Bismillah", murmushi suka mata duk suka shige ciki da "Thank you". Itama Khady ta shige gaba bayan ta zauna ta kalla saurayin ta wanda ke zaune yaro wanda ak'alla bazai haura ashirin sha shida ba tace "Durlin dan Allah kayi dropping nasu a gida mana"
Murmushi yayi yace "Ohk love anything for you" tareda matsowa kusa yayi kissing nata, Jannah nan take ta kalla Ruky wanda suka had'a ido harda muskulin juna. Ta mirror ya kalla su Jannah yace
"Umm 'yan mata wani anguwa kuke?"
Ruky nan take tace "Ni ina nan Mairi Jannah kuma na Gwange"
"Ohk toh ba matsala"
Sanda ya tsaya ya siya musu kaji da Icecream kan yayi dropping na Ruky a gida sannan ya kai Jannah yayi dropping nata ya mik'a mata ledan ta na kajin, godiya ta musu ta shige cikin gidan.

  Tana shiga cikin gida taji muryan Yaya Kashim yana waya,  ganin Hashim dake gefen ta tayi sauri ta mik'a masa ledan hannun ta tace "Yi gudu ka shigar min dashi d'aki na", da sauri Hashim ya amsa ledan yayi gudu ya shigar mata dashi d'akin ta, a lokacin dan har an idar da sallah'n magrib.
  Sauri sauri take ta shige d'akin ta kar ta had'u da Yaya Kashim ji tayi an mata wani irin tsawa wanda sanda yasa ta d'an firgita yace
"Sai yanzu kike dawowa?"
Jikin ta na rawa tace "Wallahi Yaya Kashim ban samu abun hawwa da wuri baneh"
"Toh uban waye yace karki bar gidan su yarinyan da wuri eh dan gidan ku"
Tura bakin ta tayi hawaye fal cike a idon ta dan ita masifa kad'an ka mata zata fara zubda kwalla
"Maza ki shiga ciki kuma wallahi nan gaba idan kika k'ara kai magrib a waje sai jikin ki ya fad'a miki"
Murkud'a masa baki tayi dan yana ta bayan ta, shiga cikin d'aki tayi ta cire kayan jikinta ta d'aura zani ta fad'a toilet tayi wanka, bayan ta fito ta shafa cream mai k'amshin gaske a jikin ta tareda fesa body spray. Zama tayi a kan d'an katifan ta  ta bud'e ledan kajin da saurayin Khady ya siya musu, ganin paper tayi a ciki, nan ta saka hannu ta d'auka ta bud'e, gani tayi an rubuta in bold "Words can't explain how beautiful you are, I've falling for you Gorgeous. Here are my digits please do call me" sai ya rubuta masa numbers nashi guda uku "From J-boy" wani irin murmushi tayi wanda ya baiyanar da dimples nata tace "YES!", nan take ta latsa number'n a wayar ta tayi saving da J-boy.
Kazan ta bud'e da Icecream, kaza biyu da Ice cream shima biyu, ci take tana lumshe idanuwan ta hankali kwance. Hashim neh yashigo d'akin kai tsaye yace "Anty Jannah d'azu ledan da kika ce na shigo dashi da gudu kar Yaya Kashim ya gani kamar naji k'amshin kaza"
Wani kallo ta watsa masa tace "Toh idan kaji k'amshin kaza sai na maka uban meye?"
K'aryar da wuyan sa yayi yace  "Anty Jannah zanci"
"Mtsw ni wallahi sam banson mutum mai shegen kwad'ayin tsiya, zo nan gashi kaci"
Da gudu yaje ya zauna shima akan katifan ta, yanka masa tayi ta basa sauran Ice cream da take sha
Kusan kaza d'aya yaci sukutum dan shegen ci neh dashi, bayan ya k'oshi nak yace "Ayyah Anty Jannah ki ban wannan Ice cream d'in gobe na tafi makaranta dashi mana"
Wani mugun kallo ta watsa masa tace "Bazan bayar ba maza fita min a d'aki"
"Dan Allah fa please"
A tsawa ce tace "Ka fita koh na wanke wannan ugly face naka da mari"
Tasowa yayi akan gado cike da rashin kunya yace "Toh wallahi sai na fad'awa Yaya Kashim kin shigo da ledan kaza saurayin ki ya siya miki"
Tasan sarai zai iya aikatawa yanxu tasha duka tace
"Kai toh ai zuwa gobe zai narke dan gidan ku babu fridge kuma idan ya narke babu dad'in sha"
"Eh na yarda ina so ki bani"
Hararan sa tayi ta mik'a masa tace "Maye kawai sai uban kwad'ayi, kuma kaza na daka ci Allah sa da daddare cikin ka ya b'aci yayi ciwo ka kasa bacci"
Shi koh a kwalan sa ya karb'a ice cream d'in yayi d'akin su dashi. Yana shiga Ibrahim ya gani yace
"Zo nan Hashim wa ya baka Ice cream d'in nan?"
"Anty Jannah ce"
"Akwai wani a wajen ta?"
Dan baison ya karb'a na hannun sa yace "Eh akwai har guda biyu ma"
Ajiye handout na hannun sa yayi ya shiga d'akin ta da sallama, kaf cikin gidan sunfi shiri kuma sunfi fad'a sabida shekara d'aya neh tsakanin su, wani kallo ta watsa masa tace
"Meye?"
Murmushi yayi yace "Ice cream nake so nima a bani koh na kai k'arar ki wajen Yaya Kashim"
Dogon tsaki taja tace "Idan ka fasa kaki Allah"
Zama yayi a wani kujeran dake gefen ta yace "Dan Allah kar muyi haka dake ki ban man, kamar ma ina jin k'amshin suya"
Girgiza kanta tayi tace "Kai da kwad'ayi sai dai Allah gyara hali", mik'a masa sauran kazan tayi tace
"Gashi Mallam", karb'a yayi yana wani irin murmushi yace
  "Ice cream d'in fa?"
Guntun tsaki taja tace "Kaga Mallam idan zaka ci kaci idan bazaka ci ba ka bar min abu nah"

  Zama yayi ya cinye kazan harda k'ashi k'ashin data bari suna hira bayan ya gama ya kar kad'a rigan sa ya fice a d'akin, yana fita ta d'au wayar ta ta kira Zayd dan tun da safe basu yi waya ba kuma taga kusan 10 missed calls nashi. Bayan sun gaisa sama sama tace masa bacci take ji bawai dan ya gaji da jin muryanta ba ya katse wayan. Alwala tayi ta had'a sallah'n Asr, magrib da Isha'i bayan ta idar ta shiga d'akin Ammah ganin tana bacci ta fita a d'akin ta koma d'akin ta tabi lafiyan gado...


Vote please

I love you all
      

DUNIYA~Ina Zaki Damu!!!!Where stories live. Discover now