Bayan Jannah ta idar da sallah ta zauna kusa da Ruky wanda hankalin ta sam baya jikin ta tana replying comments na mutane a twitter, wartan wayan Jannah tayi tace
"Dan Allah ke baki rabuwa da twitter, ni meye dad'in shi?"
D'an guntun tsaki tayi tace "Ina zaki sani kullum daga watsapp sai IG"
"Toh ni gani nake bai had'u ba"
"Cab! Wallahi twitter duniya neh, a social app banga app da ya kai twitter dad'i ba. Ki d'au china phone naki na miki downloading"
Jannah mik'ewa tayi ta d'au sabuwar wayan da Jay ya siya mata, tace "Ungo"
Ruky tana ganin wayan take ta amsa tayi wani irin ihu, tace
"Babes kin fara pasowa gari fa"
Wani d'an dariya Jannah tayi tace
"Dan Allah?"
"Wallahi, amma shi d'an duniya neh mesa bai siya miki iphone ba ya siya miki samsung, ai iphone shineh class, idan kinyi tweeting abu a twitter ma aga twitter for iphone"
Zare manyan idanuwan ta Jannah tayi tace "Wato idan kayi tweet ma zai nuna kalan wayan?"
"Yes"
"Yanzu idan nayi tweet da Samsung zai nuna twitter for Samsung?"
D'an guntun tsaki Ruky taja tace
"Inaaaa. Ai samsung android ce, sai dai ya nuna twitter for android"
Jannah ta kwashe da dariya tace "Su infinix da techno ma halan android neh?"
"Sosai ma"
"Toh ni da bud'e account a twitter sai ranar da na siya iphone"
Wani kalan dariya Ruky ta fashe dashi tace
"Allah kaimu ranar"
Daga nan Jannah ta nuna mata sauran kayan da ya siya mata, ta cire abaya d'aya a ciki ta bata.....
Can suna cikin hira sai Jannah tace
"Ruky Jay baya so na tsakani da Allah"
Ruky gyara zaman ta tayi tace
"Ta yaya kika sani? Kuma ya so ki koh ma dan meye shi ya sani. Dan kema ba tsakani da Allah kike son sa ba. Sabida kud'in sa kike kula sa"
"Eh haka neh... But ina tsoron gaba Ruky, I want to keep myself for Zayd. I can't lie to you Ruky, ina masifa da bala'in son kud'i but wallahi I love Zayd more"
Nauyayyan ajiyan zuciya Ruky ta sauke tace
"Jannah nima bazan baki shawara ki bada jikin ki ba, protect yourself... But kinsan duniyan yanzu an girma kuma jiki da jini sai ahankali, I ain't saying you should have sex with someone, but atleast romance. Kiss da hug ba abunda zai rage miki"
D'an zare manyan eyes nata Jannah tayi tace
"Idan akayi loosing control aka wuce fa?"
Gyara zaman ta Ruky tayi tace
"Jannah idan kinga kinyi having sex da wani toh ke kika so, duk wani maganan loosing control k'arya neh. I've been with guys, we deeply romance but bana loosing control, duk abunda yake tafiya ina sane dashi, bana tab'a bari a wuce wajen, ke har ta fingering kar ki tab'a yadda a miki"
Jannah zuciyan ta na mai bugawa tace "Ruky baki tsoro? What if watarana an miki dole, anyi rapping naki?"
"Kash Ayshe! Ai baza ki tab'a yin hakan da wanda baki yarda dashi ba"
"Ruky baki san maza ba, ba a yarda da namiji"
"Eh haka neh, amma ni ma nasan kalan mutanen da nake haka da su, idan zasu wuce wajen nace bana so. Kuma ya zauna"
"Hmmm Ruky kenan..... Allah shirye mu"
"Ameen Ya Rabbi"Sai dai tun daga lokacin nan Jannah bata k'ara receiving call na Jay ba, ya kira har ya gaji.... Ita ba kowa a ranta sai Zayd, kuma a halin da take jin kanta baza ta iya bawa kowa kanta ba idan ba Zayd nata ba..........
Bayan Wata Biyu
Jannah da gudu ta shigo gidan tana ihu, ganin Ammah tayi a tsakar gida tana shanya kayan ta da gudu ta rungume ta, tace
"Ammah na samu admission"
Ajiye kayan Ammah tayi tana washe hak'ora tace
"Dan Allah?"
"Wallahi Ammah" Take ta cire wayan ta a jakan ta tace
"Ammah na kigani, na samu Medicine and Surgery"
"Kice Habibty zata zama likita"
Rumgume Ammah tayi tace
"In Shaa Allah Ammah nah, Bi'iznillah"
Mama fitowa tayi daga d'aki tace "Jannah wani labari mai dad'i kika zo mana dashi?"
Da gudu Jannah taje ta rungume ta tace
"Mama na samu admission, na samu medicine and surgery, Ibrahim kuma ya samu Law"
"Dan Allah" Mama ta fad'a tana murna, sosai duk 'yan gidan suka taya su murna. Abba na dawo wa gida suka fad'a masa. Shima sosai ya taya yaran sa murna.......After some few days
A yau Jannah zata fara shiga cikin makaranta, tun k'arfe shida tayi wanka amman ta share kusan awa biyu tana neman kayan da zata saka. Akwatin ta dozen gudu biyu sanda ta zubar da kayayyakin cikin duka, duk kayan da ta saka sai ta cire tace sam bai mata ba. Atlast wani abayan da Jay ya siya mata shi ta saka, simple makeup tayi ta d'au jakan ta Versace da takalmin ta Vinci ta saka. Idan kaga dressing na Jannah sai ka rantse gida mai maik'o ta fito. Shiga d'akin Mama tayi tace "Mama zan wuce"
"Nikam Jannah tun asuba kikayi wanka sai yanzu kika gama shiri? Dube agogo fa k'arfe goma, tun k'arfe takwas Ibrahim ke jiran ki yaga bazai iya ba yayi wucewar sa. A hakan zakiyi karatun likitanci?"
D'an turo bakin ta tayi tace "Maaamaa this is my first day I really must have to look good"
Salati mama tayi tace "Ngla! Toh 'yar nan Allah bada sa'a kinji. Banda k'awayen banza, ki rike mutunci ki, kisan abun da ya kaiki kinji? Allah miki albarka"
"Ameen Mama nagode, bara nashiga na gaishe da Ammah"
"Toh toh madallah nagode"Tasowa tayi ta shiga wajen Ammah, zaune Ammah take tana kallo a laptop na Jannah, wanda Zayd last hutun da yazo ya kawo mata tsaraba. Murmushi tayi tace
"Habibty zaki wuce?"
"Eh Ammah, I am already late wlh. Ya kamata naje sabida layin clearance"
D'an gyara zaman ta Ammah tayi tace
"Tohm Habibty, a kula da kyau. Banda k'awaye talakoki, sam karki kula su. Ki samu k'awa wanda gidan su da maik'o ba wanda kina fama itama na fama ba. Idan har Allah yasa kin samu wani mai sonki sai ki amince, dan Abban ki bashida k'arfin da zai kula da suturan ki dasu takardun makarantan ki"
D'an dariya Jannah tayi tace "Ammah halan kina manta da Zayd neh? Kallo fa yanzu kike a laptop nasa"
Hararan ta tayi tace "Toh ai ni banga uban abun da Zayd yake tsinana miki, emm emm idan banda wannan laptop d'in da da wayar da kika bani ita ba banga komai ba"
Dariya sosai Jannah tayi ta rungume mahaifiyarta ta tace
"Ammah na Allah bar min ke"
D'an murmushi Ammah tayi tace
"Ameen Habibty, Allah kaini ranar auren ki. Allah sa ki aura gomna"
Dariya Jannah tayi sosai tace "Ameen, na d'au Ammah nah na kaita saudiya"
Ammah tayi dariya tace "Da madina da Dubai"
Jannah sosai tayi dariya tace "In Shaa Allah"
Daga nan ta mata sallama ta fice a gidan, tana fita ta toshe fuskan ta da wani uban su sunshade brand na Versace, napep ta d'au ka wanda ya kai ta har gaban university of maiduguri.Bayan ta shiga cikin makarantan ta d'au wayan ta kira zee, zee tana d'agawa tace
"Yake nashiga cikin school fa, kuma kamata ace na tsaya ina tambaye tambaye ai aji down neh"
Sosai zee tayi dariya tace "Kuma fa haka neh, kina ina?
"Ina park"
"Park na acada koh complex?"
D'an guntun tsaki taja tace
"Nikam Zee ina zan sani neh? Ni dai ana sauk'e ni a makarantan na shiga ciki"
"Okay kina park na acada kenan, bara mu zo mu d'auke ki"
"Okay dan Allah kiyi sauri" ta katse wayan.
Cikin 10mins sai ga wata perfection bak'a tayi parking a gaban ta, Zee ce ta fito a cikin motan, wani wando crazy neh a jikin sai wani top da yake bayyanar da ilahirin bayan ta, dogon attachment da ta zuba a kanta shi ya taimaka ya rufe bare skin nata, rungume Jannah tayi tace
"Ayshe irin wannan kyau d'in haka?"
D'an zaro da manyan eyes nata tayi tace
"A hakan wai?"
"Sosai ma kuwa" D'an peck ta mata tace
"Awwwnn! Thank you"
Murmushi Zee tayi tace "You're welcome.... Shall we?"
Tana mai nuna mata motan, murmushi sosai tayi wanda ya bayyanar da fararen hak'oran tace tace
"Yes please" Bud'e mata motan zee tayi ta shigaDon't forget to Vote
Share
And comment
Love you all
YOU ARE READING
DUNIYA~Ina Zaki Damu!!!!
Mystery / ThrillerNow every gurl's dream is to marry a rich Man. money! money! money!!!! is what all gurls crave for now... Duniya is a story of a young spoiled girl born in a poor family. All she ever wanted is to marry a billionaire! Find out if she's gonna end up...