CHAPTER 14

122 10 1
                                    

   Murmushi tayi wanda ya bayyanar da fararen hak'oran ta had'e da gyara zaman ta, typing ta farayi a wayan ta kamar haka 'I am soo happy for you Mine, Yanzu yaushe zaka tafi?" Ta tura masa, kurawa wayan ta tayi dan jiran reply nasa, ganin call nashi tayi nan take ta d'au wayan tace "Mutanen abuja kenan", dariya yayi yace
"Hmm ni a su wa? Ai zan na zuwa gida idan anyi hutu"
Jannah take ta tura bakin ta tace "But you told me you'll relocate"
"A'a Ayshah nace miki i'll only relocate idan sun tura ni south, kuma Alhamdulillah Abuja suka tura ni kinga ba wahalan booking na flight"
Kukan shagwab'a ta fara masa tace "Um um ni gaskia ban yarda ba, yaushe kazo gari koh kwana uku mai kyau bakayi ba, yanzu kuma zakaje kayi shekara d'aya complete a wani gari"
"Haba Tawan ai na fad'a miki zan na zuwa hutu koh? Kiyi hak'uri kinji, ina gama service ma sai auren mu In Shaa Allah"
Turo bakin ta tayi tace "But ai kace sai nan da two years zamuyi aure"
Dariya yayi sosai yace "Kar ki damu, Allah kaimu lokacin" da kyar ya lallashe ta akan anjima zaizo da daddare suyi hira..
Bayan ta gama wayan ta shiga ban d'aki tayi wanka, daga nan ta shirya zuwa makaranta. A zaure ta had'u da Abba shima lokacin yana shirin fita, durkusawa tayi har k'asa ta gaishe shi. Kallon mamaki yake mata yace
"Ina zakije da safen nan Mamana?"
"Umm Abba makaranta zanje"
"Makaranta kuma? Naga ban biya miki kud'in makarantan ba"
"Ai Abba koh mutum bai biya ba zai iya zuwa lecture"
Abba ya girgiza kansa yace "Mamana ban yarda ba, ki kira mun Kashim"
K'ofan d'akin su Kashim taje ta kirasa, bayan Kashim ya fito Abba yace
"Babana ni kam koh mutum bai biya kud'in makaranta ba za'a barshi ya d'au karatu?"
Murmushi Kashim yayi yace "Eh Abba ai ba wani abu baneh, ana hakan sabida kar a barka a baya"
Abba yayi salati yace "Ikon Allah, hakan ai yana da kyau, Mamana In Shaa Allah zuwa wani sati zan baki kud'in makaranta kinji? Karki damu"
Murmushi Jannah tayi tace "Ba komai Abba, yanzu kud'in mota zaka bani dan lecture d'in k'arfe takwas neh gashi har k'arfe bakwai da rabi tayi"
Laluma aljihun sa ya fara wanda da k'yar ya samu naira d'ari da talatin, mik'a mata naira d'ari yayi yace "Ga wannan ni kuma sai na rike naira talatin ya shigar dani bakin kasuwa, kiyi hak'uri ina fatan zai ishe ki?"
Har ga Allah Jannah koh tasi bata dashi a jikin ta, dan naira dubu hamsin cib Zayd ya bata, ta biya kud'in registration dubu arba'in da biyar, saura dubu biyar d'in ta biya k'ananan due fees dashi, sauran d'an canjin da ya rage mata ta siya rabin kwalin indomie dashi. Jannah tace
  "Abba daga nan zuwa university hamsin neh, idan na shiga makaranta dole sai na hau tricycle daga acada zuwa complex shi kuma fourty naira neh, kagani duka duka eighty naira, eighty naira sau biyu kuma d'ari da sittin neh"
Abba yace "Ikon Allah, ki tambaye maman ki idan tana da naira d'ari ta baki idan na dawo zan bata In Shaa Allah"
Cikin sanyin murya tace "Toh shikenan nagode Abba"
Abba ya juya wajen Kashim yace "Ni Kashim wani gari kace aka tura ka"
Cikin husky voice nasa yace "Kano Abba"
"Ahh Toh Alhamdulillah, ai kano gida neh. Yaushe zaka yafi?"
"Gobe In Shaa Allah"
"Toh madallah Allah kaimu, zan karb'a bashi ka samu kud'in mota yau In Shaa Allah"
Girgiza kansa Kashim yayi yace
  "Abba karka da mu, inada kud'in mota"
Abba ya gyara tsayuwan sa yace "Baba ma baza'ayi haka ba, koh kud'in siyan abinci zan baka In Shaa Allah kaji?"
Godiya ya masa sosai ya masa Allah kiyaye, bayan ya koma d'akin sa Abba ya dube Jannah yace
  "Mamana nasan kin makara, kije ki tambaye Ammah kud'in sai mu fita tare"
"Toh" ta amsa masa a sanyaye ta shige ciki, d'akin Ammah ta shiga had'e da sallama. Bayan sun gaisa Ammah tace
"Sai makaranta koh?"
"Eh, daman zan wuce ma dan nasan idan  ba ranar girkin ki  ba  bakya tashiwa a barci da wuri"
Hamma Ammah tayi had'e da cewa "Wallahi fa, yau ma dan zanje gidan Yaya Yaseer neh auren 'yarsa asabar mai zuwa"
"Wallahi hakane kinga har na manta ban kai anko na d'inki ba". Daga can zaure taji Abba ya kwala mata kira, nan take ta amsa tace gani nan zuwa, canza zancen tayi tace
"Ammah inji Abba wai idan kina da naira d'ari ki bani idan ya dawo zai baki"
Ammah ta harare ta had'e da jan dogon tsaki tace
  "Ai ni na gama nawa, tun daga nursery, primary har secondary school ni na maki, yanzu university d'in neh shima sai na taimaka? Wallahi koh tasi, ke gwara ma ki tafi dan bazan bada ba.. Haba Habibty ki tausaya min mana, tun kina k'arama nifa nake miki makaranta, Abban ki koh sau d'aya bai tab'a ce min ungu ga kud'i ki biya kud'in makarantan Jannah dashi ba"
Ganin Ammah zata b'ata mata lokaci ta rungume Ammah tace "Ammah na bansan da mai zan saka miki ba, karki damu kud'in da ya bani ma zai ishe ni.. Don't worry kinji?" Had'e da mata peg...
  Da sauri taje zaure ta samu Abba tace "Abba wallahi kud'in neh da k'yar aka samu"
Murmushi yayi yace "Tunda an samu ai shikenan, nawa aka samu?"
"Naira d'ari"
"Ahh yayi kyau toh, k'arfe nawa zaku gama na yau d'in?"
"Umm muna da 8-10, last class namu yau 4-6"
Salati Abba yayi yace "Yanzu har yamma zaki kai? Naira arba'in meye zai miki?" Ki dawo gida k'arfe d'aya kici abinci zan aiko miki da kud'in makaranta sai ki sake komawa kinji?"
Murmushi tayi tace "Toh shikenan Abba", a haka suna hira har suka hau kan titi ta hau tricycle da zai kaita makaranta shima ya hau na kasuwa. Tana shiga cikin napep d'in ta latsa number'n Amat, Amat na d'auka wa tace
"Yane ina hanya kina ina?"
Amat cikin sanyin muryan ta tace "Nifa ina gida"
"Gida kuma? Lecture d'in fa, bayan munga time table dake jiya"
Dogon tsaki Amat taja tace "Halan baki hau watsapp kin gani ba? Har na bada number'n ki a saka ki a group"
"Mtsw Amat wallahi banda data ban hau watsapp ba, wai what happened?"  A daidai lokacin har sun iso makaranta
  "Umm Allah sarki, toh dai lecturer d'in bata gari so babu lecture da safen nan sai k'arfe goma sha d'aya"
  Hannun ta ta rufe fuskan ta dashi bak'in ciki kamar ya kashe ta, dogon tsaki taja tace
   "Gashi wallahi har na iso school" Sauk'a akan napep d'in tayi ta mik'awa mai napep kud'in sa waya bisa kunnen ta tace
  "Kina nufin na koma gida kenan, na sake fitowa anjima eleven? A uban ranan garin nan? Ana August amma kamar wanda ake April koh March? Mtsw"
Dariya Amat tayi tace "Calm down kinji, bari na kira cousin sister na tana 202 sai kuje d'akin ta"
Girgiza kanta Jannah tayi kamar wanda Amat d'in na kallon ta tace
  "A'a bazan shiga 202 ba"
Guntun tsaki Amar taja tace "It's not like zaki shiga hotel koh club Babes, calm the fuck down! 202 gida neh, akwai wanda family house suna zaune neh, akwai students maza da mata. So calm the fuck down, bari na kirata yanzu zanzo nima na same ki kinji?"
  Ba dan ranta yaso ba tace "Toh"
Bayan minti goma sai ga kiran new number, picking tayi, can b'angaren taji muryan wata yarinya tace "Umm da Ayshah nake magana?"
Nan take Jannah tace "Eh wacece?"
Daman Amat ce ta bani number'n ki akan na dauk'e ki kina bakin gate, gashi har na fito bakin gate d'in"
Juye-juye Jannah ta fara tace "Ki d'an fito na sanya riga da skirt light purple"
"Ohh okay na ganki gani a cikin EOD maroon ki d'anyi gaba"
  Ganin EOD maroon tayi nan take taje ta bud'e motan ta shiga, Yarinya ce wanda ak'alla baza ta haura shekaru ashirin da biyu ba, fara ce amma ba wata kyakkyawa can ba. Murmushi Jannah tayi tace "Nagode sosai"
Murmushi yarinyan tayi itama tace "Haba dai ai ba komai, Amat 'yar uwata ce fa"
Suna d'an tab'a hira har suka kai bakin gate na wani gida, yarinyan tace "Yawwa mun iso"
D'aga kanta tayi ta kurawa gidan ido, sake-sake take a ranta sai can tace
"Umm nagode" ta sauk'o a motan. A cikin gidan kaf mata neh a ciki, inda hankalin ta ya d'an kwanta. Bayan sun shiga d'akin ta tace "Mata neh kawai a gidan?"
Yarinyan dariya tayi tace "Ai naga tunda muka shiga hankalin ki bai kwanta ba, toh ni da friends na neh muka kama gidan nan, kuma dukkan mu mata neh, so ki kwantar da hankalin ki kinji"
Ajiyan zuciya ta sauk'e tace "Umm ba komai, gashi har yanzu ban san sunan ki ba"
Dariya yarinyan tayi tace "Sunana Suhaila"
Daga nan suka d'an tab'a hira kad'an yarinyan tace zata shiga school, daga nan ta bar Jannah ita kad'ai a d'aki. Jannah kunna tv tayi ta kwanta akan gado tana kallo, daga nan bacci ya kwashe ta.........

     Da misalin k'arfe sha biyu da rabi na rana Amat ta shigo d'akin taga Jannah kwance tana ta kwasan bacci. Bugun ta da k'afa tafarayi tace "Ke banza ni da na shagala ina jiran call naki ashe ke bacci kike"
Cikin muryan bacci Jannah tace "K'arfe sha d'aya har yayi neh?"
Amat dirshin ta zauna akan gadon had'e da marin ta a bayan ta tace "Ai saidai sha d'ayan dare ba dai na ranan yau ba"
A firgice Jannah ta taso had'e da janyo wayan ta ta duba time, ganin sha biyu da minti talatin da biyar tayi salati ta d'aura hannu a kai. Ta juya tana kallon Amat tace
  "Kefa nake jira har bacci ya kwashe ni"
Dogon tsaki Amat taja tace "Tohm ni d'in ma bacci nayi, ai sai mu jira lecture na k'arfe biyu cox we already missed this one"
Cusa hannun ta tayi cikin suman gashin ta tace "Amat wallahi zan iya mutuwa, rabo na da abinci tun jiya da daddare"
Bud'e baki Amat tayi tana kallon ta tace "Wai mesa?"
Kwanciya ta sake yi akan gado ta d'aura hannu a bisa cikin ta tace "Wallahi sauri nake na samu lecture ga uwa uba ina gandan dafa abinci"
Dariya Amat tayi tace "Wallahi gashi ni kam nagaji, ga car key na kije nearest restaurant kici abinci. Nima please kizo min da take away"
  Guntun tsaki Jannah taja tace "Ni ina naga kud'i Amat? Gaba da baya naira hamsin ce a jakata"
  Baki bud'e Amat take kallon ta tace "Ahh haba ki bar wasa"
  "Na rantse da Allah"
Dariya Amat ta kwashe har kasa, tace "Haba Ayshah, wallahi wani ya ganki sai yace dubu hamsin zuwa d'ari a jikin ki.  Ga holland babba kin sanya, ga jakar ki nasan ta kai 12k, ga takalman ki Vinci wanda zai kai 7k. Haba dai 'yan mata"
Jannah tsaki taja tace "Shikenan tunda baki yarda dani ba, ke kayan nan duk samari na ke siya min. First idan sukazo sai kiga suna kashe min kud'in bala'i, daga baya idan sun nema suyi sex dani idan naki sai su gudu"
Amat ta tab'e bakin ta tace "Ahhh lallai kam, sannu mrs sun jiki. Aka gaya miki zakiyi wa namiji wayo neh? Wanda kikaga maza suna sake musu kud'i kuma basu amfani dasu toh ba'a banza suke ba. Sun had'a su da malamai neh. Ke zamanin yanzu nothing it's free, you've to risk your life before you get what you want. Ke Ayshah idan zaki zage kici rayuwar ki, ki zage ki ci. Yanzu mazan yanzu dake virgin da ba virgin ba idan suna son ki zasu aure ki. Kuma ai akwai magani da zai maida ke virgin tsab"
Dariya Jannah tayi tace "Maganan nan bazai tab'a shiga kaina ba, once idan akayi disvirgining naki  toh koh sama da kasa zai had'u baza ki tab'a zama budurwa ba"
  Dogon tsaki Amat taje tace "Ke meye kika sani? Jannah baki san komai ba. Ni bazan tsaya musu dake ba akwai wata yarinya a nan d'akin k'awar Suhaila ita ba virgin ba , no mesa zan b'ata lokaci na ina baki labari? Mu shiga dak'in ta kije labari da kanki yarinya" Nan take Amat ta taso akan gadon tana mai gyara rigan jikin ta, Jannah tace
  "Meye haka? The labari can wait, ni yanzu yunwa nakeji ki bari randa na sake zuwa sai muje mu sameta.. Ki kaini naci abinci dan wallahi zan iya mutuwa"
Guntun tsaki Amat taja tace "Mayya! Amma wallahi a yau d'in nan zamu shiga wajen koh da mun gama lecture sai mun bi ta nan"
Rolling eyes nata tayi tace "Naji yanzu please muje naci abinci"

     Ganin Amat sai tafiya take da mota yasa Jannah ta k'asa yin shuru tace "Wai ni Amat ina zamuje haka? Cikin 202 ba restaurant neh? Idan babu ai da mun shiga cikin school mun ci"
D'an buga siterin motan tayi tace "Wallahi pizza nake so na ci"
"Ban ganeh ba, kamar ya pizza kike son ci? Bayan kinsan lectures namu k'arfe biyu neh, gashi yanzu past one"
Murmushi tayi tana mai mata calm down da hannun ta tace "Easy Easy girl, In Shaa Allah before 2pm muna cikin school kinji? Just calm down"
"Amat how the fuck do you want me to calm down? Tun safe na fita a gida sabida nayi attending lecture, gashi koh d'aya ban samu ba"
D'an guntun tsaki Amat taja tace "Toh laifin wa Ayshah?  Toh nama fasa kar muyi late kiyi blaming na. Daman city star nake so muje but kawai bari mu tsaya a down town mu siya shawarma da drinks kawai"
Girgiza kanta Jannah tayi tace "Yunwan cika na bana shawarma baneh, i want to eat a good good"
"Okay tohm ba matsala muje koh city star d'in su zuba miki a takeaway"
  "A'a mu koma school muje restaurant muci abinci, idan yaso idan mun gama lecture sai muje muci pizza d'in"
Hararan ta Amat tayi tace "Halan kina da kud'in pizza neh?" Jannah ta kashe mata ido d'aya had'e da murmushi wanda yasadimples nata suka lotsa tace
  "Ai nasan k'awata tana da kud'i"
D'an guntun dariya Amat tayi tace "Ngla"

DUNIYA~Ina Zaki Damu!!!!Where stories live. Discover now