A parlour ta tarar da Maman su, Shiga tai tana haki ta fad'a kan kujerun da ke zagaje a manyan parlour nasu
Da Kulawa Maman tace Deedoh lafiya?
Mama kedai bari wallahi MALAMIN FIQH ashe d'an iskane kullum maganar sa ta janaba da haila da wasu abubuwa ko wanka ko tsarki, yanzuma wai wanka zan koyawa yan ajinmu nikam na gudo
Kika gudo ai abin alfaharinkine ace gaki kin Iya wad'annan abubuwan a wannan zamanin mata nawane wad'anda basu iya ba, kuma koyan ya gagare su
Ilimin Fiqhu ai bayan Al Qur'an babu kamar sa, dashi zaka koyi yadda zakajewa ubangijin ka a tsarkake, ya ko yamaka yadda zakayi bautar Allah, yadda zakayi alwala da adadin ta, yadda zaka cud'e ko ina najikinka yayin wanka
Deedoh wallahi kiyi alfahari da wannan ilimin naki, kudena cewa Malam Fiqhu wai basuda kunya
Idan ba'a koyamuku ba, a ina za'a koya muku, haka zakujewa Ubangiji Ku kunamasu daud'a?
Menene babbar Mara barmu da kafurai? Sallah to Idan ba'a koyamuku ba ya za'ayi ku iya kusan adadin ta da kalar karatun da akewa ko wacce da inda za'a bayyana da inda za'a sirrin ta da inda za'ayi ta mai tsawo da gajeriya da daidai misali
Kafurai duk inda suke suna wari, amma mu meyasa bamayi? Saboda muna wanka su kuma basayi, wanka bana kullum ba a'a wanka wanda addini ya halasta
Lallai Madallah ga Malamai nagari wad'anda zasu bayyana wa 'ya'yayen mu karatu da bayani na gaskiya
Jikin Feedoh sanyi yayi, tace Mama kenan duk abinda yake fad'a akan gaskiya yake?
Tabbas kuwa Deedoh na, yanzu nasan bazaki koma ba, amma gobe tabbas saikinje tashi kiyi maza kije kicire uniform ashiga kitchen Iya Kwaiseh tana ciki kije kiga mai takeyi
Tom tace, sannan ta haura sama, bakin gadonta pink colour ta zauna wayarta ta janyo, nan tashiga Dandalin Auta, readers ke hira ba writers ba shiyasa tafita sai gidan albarka wato NAGARTA nan taga Aunty Lubie ma tafara programme nata
Gidan hira ta gudu, nan taga su Auta da Munay ga Sahaf ahaf bajewa tai ta d'ora akan hiran su
Lokacin data fita bayan angama dariyar, cak naga kowa ya tsaya na juya sainaga Malam Ahmad ne ya d'aure fuska
Xahra Bukar ya nuna yace mik'e, cikin sanyin jiki ta mik'e yauwa
Malama ZAHRA bani adadin kwanakin damai Haila da mai janaba suke d'auka kafin sunyi wanka
Ido ta bud'e tace Malam lokaci yayi ma, Malam Nasmal garemu dana fad'a
A'a aiyau double na keda, fad'i munaji
Qunquni tafara, tanacewa kai wannan bakwai d'an iska ba, daga ya tambayi wannan sai wanccen
ZAHRA yadai? Oh ai Yanzu dama zan fad'a
Shi jinin haila kwanaki ne dashi.. wata tana kwana 3, wata 6 har zuwa kwana 15 a wata ruwayar akace har kwana 40 ana yinsa
Hallita ne, kowa da yadda takeyi
Janaba kuma shi ai baya d'aukan lokaci, kana Iya wankan ka alokacin dakasamu kanka, kuma ba'ajinkirta shi
Alhamdulillah ZAHRA, to ya akeyin niyyarsu ko duk dayace?
Eh niyya kusan d'aya ce saidai zaka banbace wajan fadar Haila ko janaba ne
Takhbeer nan akayimata kabbara
Haka yacigaba da tambayar yan ajin d'aya bayan d'aya
Baisami mishkila da kowa ba, amma fa Deedoh tasa is d best
Ta gidan su ZAHRA ta biya nan tafara gayamata yadda sukai dashi, Dariya sukayi nan Feedoh tace Wallahi sainayimasa tambayar da zai kasa gayan amsa d'an rainin hankali
Yana magana kamar dole aka masa, ke gayen ya had'ufa black ne amma daga gani hutu ya zauna masa
Hhhhh ZAHRA a ina hutu ya zauna yana koyarwar ai ni Wallahi banga abinda zanyi da MALAMIN Islamiyya ba, me suka Iya banda qala rasulu ko afara maganar lahira
Me sukaci bare suba ka, kedai hala son Malam Fiqhu kike?
Haba dai Allah ya kiyaye, amma wayar dayake rik'ewa kaf unguwar nan albarka nandai suka shan take rabin hiran duk ta Malam Fiqhu ne
A chat databawa Auta labari ai nan tafara d'orata Wallahi kiyi masa tambaya wadda zai gigita, yama rai naki, nan ta d'orata akan wanda Zahar ta gayamata.Autar Hajiya

ESTÁS LEYENDO
KALLON KITSE.
Ficción históricaStory ne akan Feedoh da Malamin ta wanda aganin ta tunda yana koyarwa a Islamiyya bayada wani class ba shida kud'i...saboda shid'in Malamin islamiyya ne. uwa uba daya kasance mai d'aukan karatun FIQH wanda dashi mutum zaisan kansa sai suke d'aukan...