Gama tunanin sa keda wuya, ya janyo wayar sa WhatsApp ya shiga yad'an yi hira har zai sauka saiya tafi wajan sunan ta, dp ya gani yayi mutuqar kyau ka kad'an ba, amma abin takaici itada wannan saurayin ne daya ke ganin su tare, kuma har gidan su yaga yana shiga tunda yana binsu a baya yagani.
Haushi ne ya kamashi, ganin yadda kafad'arta ta kusa gogar jikin sa, gashi ba mayafi kishi ne ya motsa, status kuwa shine yasaka yayi cilli da wayar gefeKalaman k'auna zalla ta rubuta abin takaici wai da shidai saurayin na kan dp take, leb'ensa ya lashe yana furzar da iska mai zafi, tsam ya mik'e ruwan swan gora guda ya juye a cikin sa, saboda bushewar mak'ogaran ta.
Cire kayan sa yayi, towel ya d aura sannan ya shiga toilet, wanka ya calla, kafin nan ya shirya cikin wani d'anyen boyel sky blue Ga glass yasaka turarensa ya fesa kansa yasha mayuka masu K'amshi, takalmi d hula iri guda yayi kyau .matuqa key nasa ya d'akko ya shiga mota ya zauna kafin lokaci yaja yatafi
Su kuma can dariya suke akan yadda suke ganin sa kullum kamar abin tausayi, duk Ita yanzu Deedoh tafara sarewa batason ya wahala tana sonsa itama.
Saukar makarantar Dala'ilul khairat zasuyi shiyasa hankalin ta duk yanzu ba'a kwance ba, ana ta sabga, gefe guda kuma soyayyar MALAMIN FIQH tana mata katutu a zuciya.
4:00 ya kama hanya zuwa unguwar su Deedoh hankalin sa a tashe yana jin tsoran yadda zai tunkareta tabbas yayi wauta data kirashi dama ya d'auka, haka yayita zancen zuci har ya k'arasa.
A waje ya ajiye motar sa ya taka da k'afa zuwa bakin gate d'in, sallama yayiwa maigadin amsawa yai sannan yace masa yana neman Feedoh kotana ciki?, anya kuwa naga kamar sun fita amma ka kirata kaji ko sun dawo. Tom yace, kafin yayi wata magana yaji a bayan sa ana hira dubawa yayi ZAHRA ce da Anee Allah yasa basu ganshi ba, Ji yayi suna hira akan yadda bikin zai kasance ZAHRA ce tace Wallahi MK za'a kirawo taiwa Deedoh kwalliya gaskiya zatayi kyau zamusha bidiri, Anee tace ke nifa nagaji da rabon card d'in nan haba, ko gidan masu kayan snacks zuwana biyu yau fa, gashi Ita sunfita da KITO tabarmu da wahala, Huum aike dai ayi shaani kawai a haka suka shige shi.
Gumi ne ya jikamasa kayan sa innalillah! kardai bikin ta za'ayi?, no bashi bane Deedoh dama mayaudariya ce?, amma kin cuceni duniya da lahira, bakisan nafi wannan gayen son ki ba, nashiga dad'i ni Ahmad haka kuma rayuwa zata juyani?
Gaba d'aya jikin sa a sanyaye yake haka ya zauna zaman jiran dawowar ta, Insta ya shiga yana duba hotunan ta masusashi cikin nutsuwa.
K'arar bud'ewar gate dayaji yasashi juyawa itace cikin wata red doguwan Riga ta yane kanta da yellow mayafi tai kyau, da alama ya ajiyeta ne ya tafi, tunda yaji tashin Mota.
A gajiye take a hankali tafara tafiya tana d'an wulla jaka sama, shikuma tashi yayi daga inda yake ya nufota, bata kallon gaban ta shiyasa bata ganshi ba illa tashin turaren sa data Ji
Ido hud'u sukai dashi, dam zuciyar ta ta buga anya shine kuwa?, kara kallon sa tayi, really shine, shima kallon ta yakeyi idonsa akan fuskar ta yana karantar yanayin ta ba k'aramar murna ce ta kamata ba, amma a fuska waskewa tai tazaga ya ta bayansa zata wuce
"Cak ta tsaya sakamakon kiranta sunan ta da My Sugar da yayi, bata motsa ba har ya juyo saitin ta, Kallon ta yayi sosai sannan yaja numfashi ya d'ogo.
YOU ARE READING
KALLON KITSE.
Historical FictionStory ne akan Feedoh da Malamin ta wanda aganin ta tunda yana koyarwa a Islamiyya bayada wani class ba shida kud'i...saboda shid'in Malamin islamiyya ne. uwa uba daya kasance mai d'aukan karatun FIQH wanda dashi mutum zaisan kansa sai suke d'aukan...