9:30am agogon Nigeria da Niger ya buga, a wannan lokacin ne kuma motar Yaya KITO ta danno kan kwanar da zata sadaka da gidan su Deedoh.
"Yaya KITO saurayi ne matashi kyakyawan gaske wane a wajan Deedoh da Mamansa da Abban ta wa da qanwa ne, suna zumunci daidai gwargwado, bakajin kansu, suma yaran suna k'aunar junan su, wannan kenan.
Horn yayi maigadi yazo ya bud'e, shiga yayi yasamu waje ya ajiye motarsa sannan ya shiga ainihin cikin gidan, sallama yayi, Deedoh dama taji tsayuwar mota jin sallamar sa yasaka ta fito da gudu oyoyo d'an uwa lallai kacika alqawari waih basa banba sannu kasha hanya?
Nasha kam, dan da wuri na fito ko breakfast banyi ba, saboda d'okin zuwa wajan ki..... inaa!! badai niba, kace dai zamu taimaki juna nabaka ZAHRA kawai amma maganar kazo ganina bata taso baDariya yai yace hoo Deedoh kin d'ago jirgi na ashe, to ya kuke yasu Mama banji taba tana ina?, au Mama ta tafi Daura amma yau zasu dawo itada Abba ne ma, saidai Aunty Sady jegal Ita tazo muka kwana tana sama kasanta da bacci, hhhh Wallahi kam to nidai bani abinci kafin afara maganar.
Acici kai kullum cikin abinci Allah yasa nayi da yawa plantain ce sai yamballs, na had'o ko namaka wani?, haba dai had'o su duka da tea d'in nan mai dad'i, zubo maza nafara bawa cikina hakkinsa
Tray ta d'akko komai ta had'a masa ta kawo, suna hira yanaci harya gama, bakinsa ya wanke ya dawo yace yuafa zamu fara planing d'in mu, tunda yau Saturday kuma akwai makarantar kinga sai afara koh? Dole kije school maganar kindena zuwa bata taso ba akwai dai yau makarantar?,
Eh, akwai amma fa wannan plan din naka.....anyway dama yanzu zan saka Adamu jumping ya amsomin d'inki na, yauwa yar gari. Haka ya zauna hira suke harkawo lokacin da akayi Sallah ta Azahar sannan ta tashi tai shirin Makarantar tai kyau sosai ansha make up da takalmi da jaka komai ras haka tafito suka kama hanya.
15 minutes shine ya kaisu makarantar suna dosa kwanar kuwa akayi sa'a yana tsaye yana kuma fuskan tar hanyar, haba wa wani irin d'aci da firgici ya shiga lokacin dayaga ta tsaya da tafiyar ta juya suna fuskantar juna hira suke akan ZAHRA da yadda yace dan Allah Deedoh ta gayamata yana sonta dariya take tace shi ya fad'a shikuma yana rok'on ta.
Dariya take tana sane kamar basusan yana gun ba, su Malam Ahmad an shaqa dan kansa jiyayi kamar zai rabe. Lallai dama Deedoh tanada saurayi wahalar sa kawai take?, abin takaici harwani murmushi da bai tab'a gani a face nata ba, yau shi takewa wanccen. KITO ne yace Deedoh kitafi mutumin ki ya shaqa naga sai kallon mu yake kada yazo, tom kasan kuwa lokaci yafara tafiya, bara naje amma tawo mu tafi saikaje k'ofar wajan saika juya. Haka sukai kuwa gaisarshi tai batajira amsawarsa ba tai gaba.
Kwafa yayi kana yabi bayan KITO da kallo, dame yafi shi wannan amma take sonsa ta barshi, batasan kwana kin nan har rashin lafiya yayi ba?, kuma duk a dalilin ta.
Lokacin daya fito daga gidan su, a Mota har kusan kuka yayi, dama yayi zaton bazata soshi ba, Idan ta ganshi.Gashi kuwa magana ma ta arziqi bataimasa ba. Shi anasa tunanin fa, shiyasa kodata kira bai d'aga ba, kada tace zatagayamasa bata sonsa ko taimasa rashin kunya. Shiyasa yaji tsoran answer calling nata badan wani abu ba.
Jikinsa asanyaye ya shiga ajujuwa kafin ajinsu na k'arshe. Test ya raba musu tunda jarrabawa ta kusa, ba karatu saidai bayani Deedoh agaba ta zauna itada ZAHRA magana d'aya biyu ya kalleta amma Ita ko a jikinta, duk da tai missing nasa amma kuma ai ta kirasa bai d'aga ba.
Har aka tashi basu had'a Ido ba, saidai kallon juna qasa qasa ZAHRA dariya take Idan taga yadda MALAMIN FIQH yake kallon love, dama ya Iya tazata a MALAMIN sa ya tsaya ashe har MALAMIN LOVE ne.
Yaringa su fita, waih yana zuwa bakin gate yaga KITO acikin Mota bada kayan d'azu ba, ga earpiece a kunnan sa yana tsaye a jikin motar yana karkad'a mukulli murmushi yakeyi azuciyar sa yace Malam Ahmad saika dawo amma fa ya had'u over dole Deedoh ta rikice kallon juna suke babu wanda ya d'auke idon sa har saida Feedoh itada bestyn ta suka fito murmushi suka sakarwa juna kana ta bud'e gaban motar ta shiga ZAHRA a baya kumaIna wuta Malam Ahmad yasaka motar kawai, machine nasa yaja a fusace ya tafi gida, yanajin takaici lallai mata mayaudara ne KALLON KITSE yake mata yaganta mai hankali daidai kai dole ya koma tunda zuciyar sa na sonta amma kuma zata yarda?, ba amsa.
A Mota dariya suke ganin yau kad'ai yadda yayi kicin kicin yazama wani silent, KITO be yace ku wallahi wannan wataran zai Iya bigeni anya zanci gaba da zuwa?, Haba dai kada kabada maza mana a cigaba game yanzu aka fara, sauke ta yayi kana yatafi kai ZAHRA.
Lokaci nata tafiya Deedoh suna masa wasa da hankali, abin tausayi harta wa rama ya fara akan yaga ba wata mafaka dazai Iya qara gaya mata, amma yau yayi alqawarin tabbas saiya gaya mata yana sonta har yanzu, yaji maizatace Idan bata amince ba, a yau zaibar katsina ya koma Kano maybe yasamu acan@ut@r h@jiy@
ВЫ ЧИТАЕТЕ
KALLON KITSE.
Исторические романыStory ne akan Feedoh da Malamin ta wanda aganin ta tunda yana koyarwa a Islamiyya bayada wani class ba shida kud'i...saboda shid'in Malamin islamiyya ne. uwa uba daya kasance mai d'aukan karatun FIQH wanda dashi mutum zaisan kansa sai suke d'aukan...