KALLON KITSE 2

2.4K 128 3
                                    

Adaidaita yana ajiye ta jakarta ta bud'e 1k tabashi ta juya, Hajya canjin ki? ko juyowa batayi ba ta bud'e gate d'in gidan ta shige
  Amaa taci karo da ita, da sallama ta shiga oyoyo Aunty Beeboh ashe kinzo?
Eh ke kuma fa daga ina?, hhhh makaranta mana nan tagayamsu yadda akayi dariya suka saka nan ta shan take saidataga lokacin tashi yayi sannan tayi musu sallama ta ware
   Batajima da shiga gida ba, tajiyo wayarta ZAHRA Bukar ce
"Hello qawas yah?
  Malam Fiqh yace mun wai bakida lafiya?
Eh hhhh wallahi nasan qarya kike nan take taga yamata yadda akai suma dariyar sukai
   Maman Feedoh na sama, bataji shigowar taba, saidata sakko taganta tana sana'ar tata wato chat ta jona wayar tana charge ita kuma tana aiki akanta
  Oh ni Asma'u Allah ka shiryamun Firdausi, Mama Firdausi..nidai Wallahi banaso haba saikace wata mai tallan zogale, nidai Feedoh zakinacewa dan Allah, ko su Aunty suma haka suke cewa
  To naji Feedoh, Yauwa mumcy na Yanzu naji bayani, nashigo kina sama? Eh maza a tashi ai Sallah
  Haka ta mik'e tai sallah ko Addu'a ma batayi wani dogon lokaci tana yiba, tashafa aka fara chat, 2go tahau Zahra itace online, anan aka fara hira, kafin wani lokaci saiga Auta aifa nan aka baje dagacan aka hau WhatsApp sai NAGARTA official
  Sun fara surutu kenan, saiga Aunty Lubie da gudu suka koma gidan hira
  Anan akafara zancen jumping da hiran su dai, basu suka saukaba sai 12:30 alokacin kowacce taje Sallah
   Washe gari, anan azahar Feedoh aka tafi makaranta, yau tayi abin kai,
Ta gaida kowa, amma wani rashin M ko kallon Malam Ahmad baitai ba, tashiga aji
  Shine first period kowa ya d'akko Fiqh, an bud'e Yau Babun fil janabati za'ayi, Anma yi bayani zaiyi akan yadda ake wankan janaba da wanda ya tabbata akansa da kuma abubuwan da zaiyi da wanda bazaiyi ba
   Wanka ya wajaba ga wanda janaba takama, Firdausi tashi Ki fad'an wanka kashi nawa ne?
   Ido ta zaro tace Malam nashiga uku, ni fa Wallahi bansan janaba ba, ko mai Ita bantab'a gani ba, ka tambayi Zahra ko inda take bamazuwa koh?
  Dariya ce ta kwacemasa sosai aka dara, yace niban tambayeki ba, gayan wanka nawa ya kasu, kuma ki gayan wad'anda yakama?
   Mutsikka ido tafara tana yarfe hannu, a hankali tace wanka yakasu kashi 11, 4 ya wajaba dole tilas ne akan wanda Yakama
7 shima wajibine amma bawai dole bane, Idan kayi fani'ima Idan bakayi ba babu laifi amma yin yanada fa'ida
1 wankan janaba
2wankan Haila
3 wankan Matacce(jana'iza)
4 wankan juma'a.
5 wankan sallahr Kisfewar wata
6 wankan sallahr kisfewar rana
7wankan dan Sallahr EDI
8 wankan Shiga Makkah
9wankan jinin istikhaba
10wankan Shiga musulunci
11 wankan Haihuwa(nifa'si)
Sannan kuma wankan Haila wajibine. sannan Idan kayi tarayya da matar ka shima zakayi wanka, ko mafarki kai ko kaida kanka ka tsikanowa kanka to wanka ya wajaba a kanka
   Gawa anamata wanka, sai ranar juma'a shima ana wanka, da kuma Idan za'ashiga Makkah....idan akai haila wanka dole ne idan aka gama gasu nan dai.
  Tunda tafara magana gaba d'aya bakinta yake kalla, yana yaba tsarin hallitar ta, mamaki yake dama duk karatun da yake tana d'auka taburgeshi matuk'a
   Jin tayi shiru, yasa yaqara kallon ta khabbara akamata, zata zauna yace to zo gayamun tsarki nawa ya kasu?
  Bakinta ta zub'aro tace Malam ni.....bata k'arasa ba yace maza ina jira
   Ba yadda tai tace 2 na Hadasi dana kabar, shikenan ai
  Yauwa to nawane ka'idojin musulunci?
   Hararsa tai tace Malam wannan ko jinjiri yayisu a ciki, bare ni
  Naji gayan dai , biyar ne5
Bravo alaiki ya Firdausi, sauran ki abu d'aya, gayan farillan sallah da sunnuni da mutahabai
  15 ne farillai, sunnoni goma sha takwas 18, mustahabi kuma laya'alamu  adaduhum illallah tana fad'a tana mugud'a baki
   Duk abinda take yana kallon ta, zama tai
  A'a aibance ki zauna ba, fito kowa yana kallon ki kiyi mana bayani ki kuma gwada yadda ake  alwala da wanka wanda kikayi rannan baiyi ba
  Malam ni wai zanyi, bala'i, wai nizany?
Eh, aiba qarasa ba ta kwashi takalmin ta ta d'iba a guje
  Kiranta yake amma ina takai, aji me za'ayi inba dariya ba
  Shima kansa saida ya dara, shifa gaskiya yanason Feedoh yadda take so a kira ta da shi
Haki take tana duqawa harta shiga gida

@ut@r h@jiy@

KALLON KITSE. Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora