KALLON KITSE 1

3.9K 199 3
                                    

Yarinya ce doguwa mai kyan fasali da kyan tsari, tafiya take cike da yanga da tak'ama kaikace d'iyar Sarki ce
Bayanta nagani, uniform na Islamiyya ne ajikinta Ash colour riga da wando da hijab, wanda kayan daga gani sabbine ko ince tsabar kyan guga ya maidasu sabbi
Takalmi ne a k'afarta irin peep toe d'in nan, shima Ash sai jakarta swaga itama Ash tafiya take d'ai d'ai zataje Madarasatul gwadabe Maitasa
Tanason makarantar amma matsalanta d'aya Malam Ahmad mai Fiqh ya fiya jida kai gashi da bayanin iskanci jiya ma haka yace ta mik'e ta koya wankan Haila saikace bata Iya ba
Mts wallahi sainasaka janbakin nan naga alama baison asaka Shege
Magana take harta qarasa bakin makarantar, malamai ne a zaune amma ko kallo basu ishetaba illa d'aga kai datayi ta shige
Firdausi sunan dataji ankirata dashi kenan, cak ta tsaya tasan ba kowa bane Illa Malam mai Fiqh ta tsani acemata Firdausi
Juyowa tai, ganinsa tai cikin jallabiya fara ga hularsa samarin Madina sai farin glass nasa, u look so muah tace a zuciyar ta
Firdausi bakida hankali kiga malamai ki wuce amma ko gaisuwa, kina tafiya saikace wadda zata gidan party ga takalmi mai tsini makaranta cefa ba gidan biki ba
Maza d'ebi k'asa ki goge wannan janbakin Yanzu
Kallon sa tai tace k'asa Malam?
Eh ita, had'e rai yayi yace kina b'atan lokaci inada aji, maza yi sauri kuma kin makara ga omo can wankin band'aki ya tabbata a kanki, wannan acuci mazan a kunceshi yanzu
Idonta ne yai raurau tace Malam Fiqh Plx I'm sorry don't give me dis hard work ooo I..... Bata qarasa ba yace ke! is not Modern school is Islamic so u better keep ur small broken a side
Ido ta bud'e jin wai broken, kut amma ya yanketa Ita datake degree na biyu shine zaice mata haka
Tukunnama a ina ya koyi turanci haka?
Huum a wajan ki na koya tunda ni banda iyayen dazasu sani makaranta
Kunya taji ta lullub'eta, amma haka ta maze tace dan Allah malam kayi hak'uri Wallahi bazan kuma ba dama Sis Lubie ce tasiyo new cosmetic shine nad'an shafa amma bada nufi naiba
Ganin yace a kamasa bulala yasa tasaki wata qara osh wayyo Allah tana magana tana dafe cikinta
Da kulawa ya dubeta yace ke lafiya?
Malam wata ne yakama dama naji alamar sa, inallillah Zahara Bukar kina ina kuka tafara wiwi tana dafe da ciki
Hannu yakai zai kamata da sauri ya d'auke yace bara akiramiki ZAHRA saita rakaki gida kinsan kina ciwo kika zo
A'a bansan fa zaizo yanzu ba, naji dai alama breast d'ina yafa...... Uskut yace mata jin zata b'aromasa magana
Tana sane ta gantsare tace Malam yana juyowa ai da sauri ya d'auke kansa, yace mik'e a hankali kitafi gida yana magana kansa a sunkuye
Gwalo tamasa ta fara tafiya tana cije baki, harta fita
Adaidaita sahu ta tara sai gidan Lubie aminiyar kwarai aje asha shafta
Tana cikin adaidaita tana tuna yadda taga Malam Fiqhu yayi, dayaga ta gantsare dariya tasaki tace kaikuma cemun Firdausi, saikace wata villager kai amma zan maka rashin m
Yana wani kanne ido kamar abokina jumping

Saina b'aromaka tambayar dazata gigitaka, tunda kai kullum cikin bayanin mata kake har kana wani banbance Maniyyi da maziyyi hhhh zaka banbance wani abu kuma
Muje zuwa

Auta ce

KALLON KITSE. Where stories live. Discover now