KALLON KITSE. 15

1.4K 98 2
                                    

Assalamu alaikum sallama itace first kafin komai, a ciki ta amsa kana ta gyara tsayuwar ta, kansa ya sunkuyar tace Firdausi anawa tunanin ko albarkacin cewa MALAMIN kine ne yakamata ki gaisheni koda baki duba d'ayar alak'ara ba.
Kuma tunda kikaga nazo gidan ku kinsan wajan Ki nazo ba wajan wani ba, tunda ke nasani a gidan. Baki ta tunzuro tace nifa bangan kaba shiyasa ina kwana?
Saidana rok'a ban amsawa kuma kin ganni da wannan idon naki mai kama dana mage, batasan lokacin da tayi dariya ba tace Allah idona ko na Jabo da Auta albarka suda suke gani kamar sunada ido
Anya zan yadda kuwa. Allah kuwa idona yanada kyau, ok amma haka ake tarbon bak'o a barshi tsaye?, hannu tasaka ta rufe fuska tace I'm sorry tawo muje, tafiya tarafa yana bin ta abaya yana yaba yadda yaga take tafiya a nutse a hard'ewa ko wani abu da za'a kushe.

A haka suka k'arasa cikin sitting room bud'ewa tai sannan ta nunamasa kujera a hannu, tace 5 minutes zan shiga gida kaji?, da hannu yamata alama ba komai, murmushi tai tanajin k'aunar bawan Allah a zuciyar ta.
Da gudu ta shiga daidai nan Yaya KITO ya shigo shima, zama tai tana haki tace munci gari yammata
Bamu gane ba?, zayyanamusu komai tayi, waih murna harda tsalle, Yaya KITO ne yace bravo aikin mu yayi amma kinsan kada ki sakar masa fuska kad'an ja ajinki ki
Wah?, tab nakara sakiyar daba ruwa?, wallahi dariya zanyi na washe hakora, zakaban fake advice nakara jawa kaina

Au nid'in kuma?, eh kai fa, hhhhh yarinya zaki k'ara zuwa wallahi saina rama, habadai karame dai ance maka ni zan k'ara yadda musake fad'a?

Munji tashi ki je wajan sa, ko baku ce ba, Anee angama komai?, eh angama Besty Anker Ita sunada test so bazata zo ba, amma tamun transfer ta 10k tace a baki gift. Wow tnq bara nadawo nayimata godiya lallai Anker gaskiya mun more, sauri tai ta d'ebo cake da samosa ta d'ora gorar ruwa da juice ta tafi kaima sa
A kan d'an stool ta ajiye, cup ta d'auka lemon ta zuba masa sanann ta bud'e plate d'in tace bismillah?
Da kallo ya bita ganin yadda take komai a nutse, gashi sai yake gani kamar matar sa ma sukutum, hmm yace sannan yayi bismillah yafara ci.
Yana k'arewa tabashi tissue yana goge hannun ya fuskance ta, yace Firdausi nasan kina tuna abinda yafaru kwanaki, amma inason komai ya wuce muyafi juna ko ni keda laifi ko kece ayiwa juna afwaa kinji?
Kai ta kad'a, sannan yace Deedoh Wallahi kinji na rantse banda abinda nake so a hallita ta mutane na wanann k'arnin bayan iyayena sai ke. Najima ina Dakon son ki, nakasa gayawa kowa ina kishin ki shiyasa kika d'auka tsana ce ko wani abu, ina alfahari a yadda kika sami kyakyawar sheda a Makaranta da unguwar Ku, a kullum burina Allah yaban mace daidai ni, bangantaba banji taba sai akan ki, inafatan bazaki bulan k'asa a ido ba, Idan kuma bakida ra'ayina zanyi farin ciki kin gayan gaskiya
Idan kuma angama komai na bikin ki, fell free kifito ki gayan, amma zanyi bakin ciki Idan har kika furta cewa ankusa auren ki da wani, duk maganar dayake idonsa na kanta.
Kallon sa tai ta gefen ido kana ta juya kanta gefe, tace nifa banmaka komai ba rannan kayi zuciya katafi, kuma nakira wayar ka wajan 10× baka d'auka ba, nayi maka magana a chat ba reply to ya zanyi?
Sakkowa yayi ya tsuguna a gabanta yace, nace bartuna baya koh?, kai ta kad'a yauwa to yanzu sauran magana d'aya ankusa bikin ki ko kuwa?, nifa banda saurayi Allah ma yasani, saurayina d'aya Malam Ahmad shi kuma yayi fushi bayan Ita masoyiyar tasa tana begen sa

Lah to ina d'ayan nan fa, kuma naji ance bikin ki za'ayi tunda har rabon card ake, ni ba wani biki sauka zanyi ta Dalailu fa, kuma Yaya KITO wana ne
Kenan banda rivals?, a kunyace ta kad'a kai, alhamdulillah inafatan yau za akaini wajan Baba mu gaisa gobe na turo iyaye na?
Haba dai yayi wuri, awajan ki ba, amma ni waje na ko Yau a d'aura aban ke, bakisan yadda nake son kiba, shiyasa zakice haka, nan ya zauna yana bayyana mata asirin zuciyar sa, tuntana jin wani iri saigata itama Tana gayamasa yadda take sonsa tunkafin tasan shine, da kuma wani iri datakeji Idan ta gansa
Kaf sun manta da wani nauyi na Malami da d'aliba, sai hira suke, harda tsokanarta yace tagayamasa meyasa Ita bata wankan janaba (, kunsan tamasa wannan tambayar abaya can)
Kanta ta sunkuyar tana dariya ciki ciki, basu Ankara ba, saijin wazifa sukai, basu tashi ba, ZAHRA da Anee sukai sallama
Waih hardasu akasha hira, saiga Malam Ahmad ya ware ya aje malunta gefe yana hira da kawayen budurwar sa, ashe d'an gari ne, KALLON KITSE akewa rogo, suna masa Kallon ustaz ashe kansa a waye yake
Da kyar sukai sallama ya tafi, da daddare kwana cur sukai ana hira, a washe gari yace mata zai koma kano yafara shiri, yana dawowa zaiyi bankwana da ISLAMIYYA da komai da kowa tunda yasami muradin sa
******** Bayan Sati d'aya
Magana ta zama babba, kowanne b'angare sunyi na'am da kowanne, kuma ba'a saka lokaci mai tsawo ba wata biyu kawai aka saka, lokacin ta had'a saukarta ta Al Qur'an.
Yan Makaranta sunsha mamaki lokacin da sukaji labarin soyayyar su, Malamai duk sunmasa murna, tunda Deedoh mai kyan hali ce.

@ut@r h@jiy@

KALLON KITSE. Donde viven las historias. Descúbrelo ahora