Ido ta bud'e sosai tace nashiga uku Malam mene haka, plx ka fita waya kawoka gidan mu?, tana magana tana ja da baya shikuma yana binta, Ido ta ware ganin ya kusa cimmata kafin yayi wani yunquri ta kwasa da gudu, zagaye parlour d'in suka fara, gajiya tai tace Malam nifa mene haka?
Tana magana tana murgud'a baki, a tsaye take Ita tamarasa wani tunani zatayi, meyakawoshi gidan su yazo yamata duka ne kome?, amma kuma ya akayi yayi shiga irin haka, saiyayimata kama da my sugar, amma shi ai ba MALAMIN ISLAMIYYA bane.
Huum my sugar mene na tunanin bayan gani a gaban ki, Feedoh nasan abin zaizo miki a bai bai, kuma zakiga kamar almara ko al'ajabi ta wani fannin zakiga kamar namiki k'arya ko something like that dai.
Kan kujera dayake ya tashi, kusa da ita ya dawo, yace believe me Feedoh Wallahi tun ranar danafara ganinki naji kin kwanta mun a rai, kuma nutsuwarki da hankalin ki yasani nacewa saimunzamo abu guda, babu wanda yasan ina sonki sai iyayena da mahallicina saini Kuma, sauda yawa inason bayyana miki kaina saina kasa badan komi ba, sai dan tsana da yammata kewa MALAMAIN ISLAMIYYA, baku d'auke mu abakin komai ba, kunazaton cewa bamuda aikin yi shiyasa naji tsoron gaya miki.
Lokaci yana tafiya naga kullum kara sonki nakeyi, ke kuma k'ara kyau kike nasan ba kowanne d'a Namiji bane zai ganki bai k'ara kallon Ki ba, kinada suffar da kowa zaiyi burin kizama tasa.
A ranar da natambayeki, Ki kamun cikakken bayani Wallahi aranar naqara tantance wa nasamu mata, ilimi babu kamar sa a yanzu, saigashi nasamu wadda ta had'a komai, a ranar na nemi number naki nafara miki magana.
Addu'a naitayi kan Allah yasa ki amsheni saigashi kinkarb'eni, harna furta miki Kalmar so kikayi accepting a ranar ba k'aramar murna nai ba, nagode Allah sosai
Washe gari naje gida wajan Abba na, nagayamasa nasamu mata, Mama na tai murna sosai, ranar tare da Abban mu, mukazo yayi bincike akanki da komai kinsamu kyakyawar sheda wajan jama'a iyayen ki ma, mutanen arzik'i ne, Feedoh kiyiwa Allah ki karb'i soyayyata badan ni ba, nasan namiki laifi kan b'oye miki kaina da nayi, amma Wallahi duk maganar dana gayamiki a waya akaina duk daidai ne, abu d'aya na b'oye miki shi, shine nuna miki ni waye, amma kimun afwaa, kada ki hukuntani da laifin da nasan bawani babba bane.
Nasan muna son juna ni dake, naji kuma ana fad'a ana son Ahmad Insta, kuma kinsan nima ina sonki, Idan har kin amince da gaskiya wallahi gobe iyayena zasu zo, biki watan maulud.
Kansa sunkuye duk yake wannan maganar, a hankali ya d'ago yana duban ta cikin shauqin so.
Ajiyar rai tayi, zuciyar ta na waswasi anya hakane?, to ya akayi bata gane saba?, huuum Malam Ahmad nidai banda magana a yanzu sainayi shawara saboda haka sai anjima, tanagama fad'a ta mik'e.
My Sugar tsaya dan Allah!, ko juyowa batayi ba, saboda Ita abin daure mata kai yayi, gashi kuma wata kunyar sa takeji, lallai ashe KALLON KITSE akewa MALAMAN ISLAMIYYA ji yadda MALAMIN FIQH yake magana yana tsarata tabbas ta yadda shine, amma Kuma ya shammaceta, itama kam saita rama, shiru tamasa.
Fiddausi kina nufin kice baki amince dani ba?, duk maganar dana gayamiki tazama abanza fine nagode sosai, ko lokacin ki da kika ban a waya ma nagode.
Ina miki fatan alkhairi, arayuwar ki My sugar inawa rayuwar ki kyakyawan zato, inaiwa duk wanda ya aureki fatan samun kamilar mace, Allah ya cigaba da yiwa rayuwar ki albarka.
Allah yabamu alkhairi, yana gama fad'a ya janyo Leda mai tambarin UAE guda uku ya ajiye mata sai envelop a cike shima ya ajiye mata ya bud'e ya fita ba waiwaye.
Sandarewa tai a wajan, takasa magana tanajin tashin motarsa tafita da gudu, ina ya fice sai bayan motar tagani Highlan, kiransa tafara amma ina ya fice.
Gida ta wuce da gudu, kukan ma baizo ba, saidata dangane da d'akin Mama sannan ta fasa kuka, da sauri mama tace Auta lafiya menene baizo ba?, ko wani abu ya miki?
Mama ya tafi yace wai nasamu wani mijin, Allah inasonsa Mama yazanyi nashiga uku, wayyo Allah na.@ut@r h@jiy@

ANDA SEDANG MEMBACA
KALLON KITSE.
Fiksyen SejarahStory ne akan Feedoh da Malamin ta wanda aganin ta tunda yana koyarwa a Islamiyya bayada wani class ba shida kud'i...saboda shid'in Malamin islamiyya ne. uwa uba daya kasance mai d'aukan karatun FIQH wanda dashi mutum zaisan kansa sai suke d'aukan...