Bata sauka a chat ba saiga Kwaiseh da STYLICH nan akafara hiran ana cewa lallai shima tayimasa gyad'a tayimasa irin tambayar da yakeyi
Aunty Jegal ce tace kunganku baran Auta kinfi kowa d'orata menene aibun sa, akan yanagayamuku gaskiya Feedoh kada kice masa komai kinji
Dariya akasaka, Kwaiseh tace haba big Yaya ai kamar tayi tagama
Haka ta manta da wani kitchen saida Maman ta shigo kana ta mik'e da sauri
Malam Ahmad yana kwance ad'aki ya saka hannunsa ya bayan yayi matashi da shi, idonsa yana kallon fankar dake wulwulawa, idonsa k'ur tunani yake shifa Wallahi yaga type nasa, dama yanajin wani abu gameda Deedoh amma na yau ya zarce komai nata yayi masa
Gata da addini ga Iya speach shifa ya more, bazai tsaya b'ata lokaci ba ko Jan aji ayi bashi kamar yadda yayi akan budurwar sa ta farko *Ashnur* saijin aurenta yayi
Best solution is to go nd tell her ina sonta, to Idan tace bata sonka ya zakayi?
Waye Malam AhmadAhmad d'ane ga Alhaji Isah Kadara wanda yake attajirine yanada matan aure biyu inda kowacce cikin su Allah baibata Haihuwa ba, sai daga baya uwar gidan ta haihu akasami Ahmad
Murna d'oki babu wanda basuyi ba, Ahmad wajan amaryar Abban sa yatashi tayimasa rik'o na gaskiya da amana ta tarbiyantar dashi
Yayi makaranta sa a Musa Ilyasu daga nan yatafi ABU inda ya karanci Medicine zallah yanada kokari, Allah yabashi sa'a arayuwa shiyasa har ya k'are karatun sa baisami matsala ba
Ahmad yanada farin jini sosai, kuma ga sakin fuska dangi kowa nason shi, yammata ma haka
Ahmad yanada kwarjini yanada burin taimakon mata shiyasa yakaranci aikin likita, Yanzu haka yana aiki a AKTH bayan wanda Abban sa ya bud'e masa a unguwar tasu ta Janbulo
Mata da yawa nasonsa amma kowacce badan Allah take sonsa ba, wata dan kyau nasa wata dan kud'in su, gashi nan dai, shiyasa yace zaije inda ba'asanshi ba, yanemi matar aure kuma zainemi islamiyya yayi koyarwa aciki, ya lura mata sunada k'arancin Ilimin Fiqhu, sau dayawa zaiga wasu cikkakar alwala basayi daidai bare akai ga batun yadda zasu tsare dokokin wanka
Wanka shine gaba, tunda Idan har yarinya ta kai minzalin da zatayi al'ada wanka ya wajaba akanta, to Idan bata Iya bafa?, ko ta Iya amma bata cikakken sani akan yadda zata cud'e can tasawa nan ruwa ai anyi ba'ayi ba kenan
Haka zaka jewa Allah kanamai najasa, kayi masa bauta bacikin tsarki ba, (dan Allah mata adaure Wllh akwai wadda ko yanda akeyi bata sani ba, even niyya ta wankan wata bata iyaba, amma tafito tana gwalli)
Kana iyayi kana turancin banza kana kashe kud'i kuna zuwa cinema ko malls ko yaukaine nan qasa Kaine can, Ka daure ka Iya wannan abubuwa badan komai ba, saidan Ibadarka ta cika kuma ka kasance cikin tsafta
Yazo garin katsina badan komai ba, saidan kara dayaga mutanen suna dashi, kuma katsina tayi kusa da Kano zai iya zuwa gida lokacin da yaso
Abokinsa shine yayimasa hanyar da aka d'aukeshi amatsayin MALAMIN FIQH
Shekaransa d'aya da wata uku cikinta, yana jin dad'in yadda kowa ke yabon sa akeson period nasa, Illa FEEDOH dayaga bata so
Yayi tunanin irin ajebo ce, amma jiya tabashi mamaki yadda tasan sharuddan komai, yanason mace mai shagwaba da ilimi Feedoh duka ta had'a
Gata ba laifi kyakyawa black beauty, ga hanci bakinta maikyau hak'oranta farare k'al garaigarai
Siffarta ke masa gizo, yana hango yadda take cuno baki gata da tsokana sai tsoro
Idonta namasa kyau, haka yazauna yana sunbatun son Deedoh
Wayarsa ya janyo, a zuciyarsa yace aji irin na Deedoh nasan dole tana insta bara naga
Searching sunan ta yafara, yasaka Feedoh nan ya laluba ba Ita, yasaka Deedoh nan ma no, Firdausi zaisaka anan dariya takamashi yadda ta tsani sunan aiba zatayi using dashi ba
Haushi ne yacika shi, har zai fita saiyace bara yaga yaji ZAHRA nacemata Yar ficika nan yasa shima no, OK bara na raba naga
Yar_ficika yes
Nan yai following nata, Pics nata yashiga nan yafara cikin karo da ita aisaiya rud'e yaga yadda take real zuba gayu wani photo ne yaja ra'ayinsa wanda tai kusa da bishiya ta bud'e garaigarain hak'oranta ta dafa kugu tayimasifar tafiya dashi
Komai ya tuna naga yayisauri yayi unfollow nata, wayar sa d'ayan k'iran Motorola new Yar yayi, Ita yaimaza yai download na insta ya bud'e shi
Posting pics nasa yai guda 2 nasa amma duk irin yakare fuskar sa, sai ragowan kuma duk irin me love d'in nan ne
Sunanta yasaka, sallama yayimata
Batajimaba ta amsa anan yace mata nice short, tnx tace
Yar ficika sunan yamun sweet abaki
"Koh tace masa, eh shima wajan posting nasa tai, pics sunmata kyau baran wani mai kalamai sanyayyu
Basu qara magana ba, kowa yacigaba da sabgarsa
Nan fa akafara saving pics, yanayi yana qara jaddadda sonta cikin zuciyar sa@ut@r h@jiy@

KAMU SEDANG MEMBACA
KALLON KITSE.
Fiksi SejarahStory ne akan Feedoh da Malamin ta wanda aganin ta tunda yana koyarwa a Islamiyya bayada wani class ba shida kud'i...saboda shid'in Malamin islamiyya ne. uwa uba daya kasance mai d'aukan karatun FIQH wanda dashi mutum zaisan kansa sai suke d'aukan...