KALLON KITSE. 5

1.7K 117 2
                                    

Yau   ba Islamiyya shiyasa Feedoh bata da wata fargaba, akan MALAMIN FIQH, tasan bamakawa saiya doketa wannan gudun datayi, gashi  ZAHRA tace ansiyo Manyan bulale da aka tashi
    Amma ganin ba Islamiyya yasaka ta bararraje tafara chat, brush tai da wanka, tasaka yar vest haka da wani milk skirt ta janyo pillow ta d'ora kan cinyarta ta aka soma sana'a  sa'a
    Tana hawa da Maganar Lubie tafara cin karo, nan sukai hiran su irin ta amintattun k'awaye, sannan ta shiga group nata, yau rashin Mutunci zatayi shiyasa ko d'an abokin mu jumping bata saka ba, tafara duba wad'anda basa comment removed tai na wajan 10 peoples kafin aka shiga gidan hira dandalin karya tattalin Data
    Hira suke sosai ana Shafa, saiganin abun Insta tai ya shigo, da sauri ta duba, Mohd Ahmad ne na jiya, yayi liking pic d'inta ga comment da yayi mai dad'i, tnz tace masa
   Magana yayi mata, zai iya samun contact nata, ko WhatsApp suyi, yaga tanada hankali
  Later tace masa kawai, bata fita ba, taga yayi posting photon sa, wow he look so nice da kayan NYNC yayi amma yasaka fulan ya rife idonsa
Huum, amma kai mai yasa baka fidda ainihin fuskan ka?, naga yawan cin pics naka kana cover na face why?
   Ba komai, kawai inason photo a haka, ok
  Am nace naga kinsaka author kina rubutu ne?
  Eh inayi, but social not publishe one
  Ashe ina tare da marubuciyane, wanne book kika rubuta?
  Ba yawa, amma dai Kunya Adon Mace dashi nayi popular
  Kai zanso na karanta, Kunya tabbas Adon Mace ce, amma sainaga kamar wasu matan basuda kunya, baran na wannan zamanin Kuma kunya tanacikin musulunci
  Da alama littafin ya fadakar, ya za'ayi nasame shi?
  Kai maza dama suna karatu?, eh to wasu sunayi, inacikin jerin wad'anda basu yi, amma tunda kece zan iya karantawa
  Huum, ni kuma yaushe kasanni da zakace haka?
   Ai kinsan ana iya sabo na one hour ma, bare mu harmun kwana ma
  Haka!, harnafara d'okin nakaranra nasan anyi aiki da ilimi wajan yinsa daga gani kinada ilimi daidai gwargwado
  Hhhhh, saikace munzauna ko katab'a ganina?, kufa kanawa kunfiya Iyayi komai karatu, da alama kunason karatun addini sosai
  Wallahi kuwa bare na Qur'an da FIQHU dan sune ja gaba, rashin sanin ilimin FIQHU ai babbar asara ce ga d'an adam Wallahi
   Na farko kinga shi Qur'an yagayamana zamuyi alwala muyi Sallah muyi wanka, mu bautawa Allah, amma baifad'i yadda zamuyi komai ba.. bai fad'i adadi ba kuma.
  Amma FIQHU shiya fad'a kuma ya tantance ya ware Sunna da Farilla da Mustahabi, ya ware Sunnah mu'akadda wadda sunnah ce amma maik'arfi
  Ya.....a'a Malam afwaan, wannan zuba haka, da alama kagama typing d'in abin kafin kafara
  Waih wa'azi amma kana fama, Kuma shine kake Insta da WhatsApp?
  Da alama malami ne kai?
  Kwarai kuwa MALAMIN FIQHU Kuma na Islamiyya ba
   Tab, kaga sai anjima da kafara hira mai dad'i amma zakasako wani zance, muma munada irinku a garin mu
   To kai inbaka shawara, Idan kana magana da mace kama dena cewa kai MALAMIN ISLAMIYYA ne, dan ba wadda zata soka, ahaka dai kamar wice kai amma ina ashe ....tab a hakan zanbaka number na?
  Dama FB kaje Ka bud'e page akan haka, amma daga had'uwa zaka fara zuba
   Ku zancen ku d'aya, wanka tsarki haba, ninama fara ganoku, duk iskanci ne a fakaice kukeyi
  Bye
   Tana gama fad'a, ta sauka tana tsaki, kut da harna fara zurmawa kalarsa tamun, duk da banga face nasaba, ashe tsami  ne
  Amma Idan hakane Malaman Islamiyya suna da kyau, saidai ba Money a hannu, gasu wayewarsu kad'an ce
   Amma suna da kyau, kaya kuwa kala 5 ko 6, kai a tafe su a tafe
   Waya ta d'auka ta bugawa ZAHRA, tace ke qawa nahad'u da Malam a Insta, haryafara maganar tasu ta wanka tsarki saikace ba'a iyaba
   Hhhh lallai ke Malamai 2 kika had'a, yimun shiru, amma fa gayen ya had'u duk da banga fuskarsa ba.

    Love u all my fans ana tare ❤❤

KALLON KITSE. Where stories live. Discover now